Sunday, 6 August 2017

Yazeed ko Yaseer

[2/17, 1:08 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer
           Nah
Ayshart Farouq
           NWA

    
                35

Kuka Afnan ta shiga yi tana nuna Yaseer din da ya shigo Wanda shima kanshi mutuwar tsaye yayi yana kallonta sai dai sanin abunda ya aikata ne yasanya yayi tamkar bai taba ganin halittarta a duniya ba, ganin haka ya sanya Afnan tayo kanshi tare da ciyo kwalar shi, "wlh Allah shi yamin fede wlh shine Yazid kaci amanta ka cuce ni"
Buge hannuwanta yasir din yayi, " ke kinada hankali kuwa waye ke? Meye hadina dake da zakimin sharri?" Alh ya dube Yasir din yace, " ya isa haka yasir zo ka zauna abunda ta gama cewa Yazid kenan "
Jin haka ne ya sanya Afnan tayi wata uwar Kara tare da fashewa da wani matsananci kuka, cikin ranta tambayar kanta take,  me ke shirin faruwa Dani ne? meyasa Yazeed zai min haka? taya Yazeed ya koma Yaseer ? Gigitaccen Marin da aka dauketa da shi  ne ya dawo da ita cikin hayyacinta, sake daga hannu yayi ya sake dauketa da wani Marin Wanda saida taga wuta cikin tsananin fushi yake magana,
"Kin cuce mu Afnan, kin cuce kanki,  kin kuma cuce kauna da tarbiyar da mahaifinmu ya baki".
momy kam tunda ta zauna banda hawaye ba abunda takeyi, duniyar baki daya ta Mata zafi, mikewa tayi tana dubin su Yazeed din da suka zuba ma ikon Allah ido suna kallo,  " Dan Allah bayin Allah kuyi hakuri da Abunda ya faru" ta fada dakyar tana maida nunfashi, jin yanda take maganar ne ya sanya Ibrahim yayi saurin dubota amma kafin kace me daga kafarta keda wuya ta sulale ta fadi kasa, Ibrahim yayi kanta da sauri yana jijjigata,
Afnan da ke tasaye baki daya kasa komai tayi dakin kanshi duhu yake Mata wata irin juwa take gani ga wani irin matsanancin ciyon marar da ya taso Mata wata irin Kara ta kwala ta zube kasa yayin da jini yaketa bin kafafuwanta,

Ibrahim kam ya rude iya rudewa yarasa kanwa zaiyi ga mahaifiyar shi ga kanwar shi, duk da tsanar Afnan din da yake kasan cewar ita  taja komai, yasan tana bukatar taimako Ruwan da Yaseer yayi saurin kawowa ne yazubama momy amma Ina ko motsi batayi ganin haka yasan ya,
Ibrahim din cewa "pls Yazeed  Ku taimaka min mu kaisu asibiti Dan Allah."
Yazeed kam har zuwa lokacin haushin Afnan yakeji saboda tamishi abunda ba'a taba yi mishi ba.  Yaseer kuwa wani irin tausayinta ne ya kamashi sai dai ba yanda zaiyi don yasan ba yanda za ayi yace shi yamata ciki a zauna lfy.

Cikin motar Ibrahim aka sanya momy yayin da aka sa Afnan cikin mota Yaseer suka nuface asibiti,

Direct emergency aka nufa dasu don ceto rayuwarsu  bama kaman Afnan da taketa bleeding.

Cikin ikon Allah momy ta farfado sai dai jininta ya hau sosai don harma  yafi na dady hawa.
[3/19, 12:54 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer
              Nah
   Ayshart Farouq
             NWA

           36
Afnan kuwa har kusan magrib bata San inda kanta yake ba, cikin jikinta ma ya zube saboda wahala da damuwar da ta shiga  saida ma aka Kara Mata jini.

Har zuwa wannan lokacin kuma Yazeed da Yaseer suna nan a asibitin, shi Yazeed yana zaune ne kawai don amincin da ke tsakanin shi da Ibrahim,  Yaseer kuwa  Abubuwa da yawa suka sa shi zama a asibitin.
  Ibrahim ne yafito dakin da momy take, hannu yabasu sukayi musabuha tare da ce musu, " nagode kwarai fah da dawainiya Allah ya saka muku da alkhairi" suka karba da ameen,
Yaseer yace, " mushiga daga ciki munganta don wucewa zamuyi lokacin sallah na gabatowa,
Harararshi Yazeed yayi don shi bai so haka ba son yayyi su wuce tunda ga Ibrahim nan yazo, ba yanda zaiyi dole yabi bayansu suka shiga dakin da Afnan din take ciki,

Kwance take har zuwa lokacin, kallo daya zaka Mata kagane tana cikin mawuyacin hali saboda yanda take jan nunfashi da yanda take maida shi.

"Har yanzu bata falkla ba?" Cewar  Ibrahim yana duban nurse din da ke daura Mata drip a hannu,
"Gaskiya yanada wuya ta falka yanzu saboda Injections din da aka Mata masu karfi ne, inaga sai zuwa dare ko tana falkawa"

Cikin damuwa Ibrahim ya bude baki zaiyi magna, wayar hannnushi tayi kara, cikin ladabi yake karba wayar, Wanda ya nuna alamar da mahaifin shi yake magana, kallo daya zaka mishi ka tabbatar da baya cikin nutsuwar shi saboda yanda yaketa bawa mahaifin shi hakuri, jikinshi mace ya ajiye wayar.

Yazeed da Yaseer kuwa zuba mishi idanuwa sukayi ganin yanda yaketa gumi,
"What happen friend?" Yazee ya fada yana kallon shi,

Shafe zufan da ke  karyo mishi yayi, "their is problem friend I need you helps"

"Ok inajin ka how can we help u?"

Cikin damuwa Ibrahim ya ce, " dady yace yanzu yanzun nan inzo yana nemana kuma bayq so kafata ta sake takowa wajjen Afnan ya yafeta bata cikin 'ya'yan shi idan kuma na sake nayi bai yafe min ba",

" subhanallah" Yazeed ya furta, yayin da Yaseer ya fadi jagwab zaune kan gado yana dafe Kai,

" yanzu to ya zamuyi mu" Yazeed ya tambaya yana maijin haushin iyaye irin na Ibrahim da basu San kaddara ba.
Ibrahim ya ce, " Ina so Dan Allah Ku taimaka min ku Dan kulamin da ita, har zuwa lokacin da za'a sallameta nasan mahaifinmu ya fada ne kawai saboda fushin zuciya m sure kafin lokacin ya sauko daga fushin da yake da ita, pls friend don't say no",
[3/19, 1:40 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer
            Nah
  Ayshart Farouq
            NWA

           
              37
    Yaseer yayi saurin cewa "kada ka damu zamu taimaketa insha allahu", yafada yana kallon fuskar Yazeed da ta chanja kala,

Ibrahim ya ce, " thank you very much guys am really appreciate, zamuyi waya idan Ana bukatar wani abu"  ya fada yana basu hannu, yafita da sauri,

Cikin bacin rai Yazeed ya juyo ya dube Yaseer "me yasa kayi haka? Ko Kai kanada maccen da zata zauna ma da ita ne?"

Shima Yaseer fuskar shi tamke yayi magana" ko babu ni Zan zauna da ita,"

Tsaki Yazeed din yaja "wayasani ma ko Kaine kayi aika aikan"

Murmushi Yaseer yayi, " nagode Allah dai da kowa yasan waye tace ya Mata na tabbatar da ko yanxu ta buda baki zatace Yazeed ne ya Mata fede so nasan ko miyema Kai ne zaka hada mata cox at the first place Kai............."
"Just shout up crazy boy" Yazeed ya katse Yaseer cikin tsawa, idanuwan nan nashi sunyi jajur kallo daya zaka mishi kasan yana cikin bacin rai,

Tsaki Yaseer din yayi tare da fita kasancewar anfara kiraye kirayen magrib,

Bayan sallahr isha'i duka su biyu suna dakin ba Wanda yace da wani ci kanka kowa dannar wayar shi kawai yakeyi.

Nurse ce ta shigo dakin da sallamarta tana ce musu " yakamata fah mace tazo tayi jinyarta don akwai Abubuwan  da ake bukatar mace ta mata,"

Yaseer ya ce, "dole sai mace zatayi?,"
"No ba dole ba tunda ita kadai take a daki amma idan da mace zaifi, anyway ko mijinta ma zai iya, tunda dole mutum daya zai rika kwana da ita, Kai Doctor Yazeee kasan dokar ai,"
Gyada Mata kai kawai yayi,
tayi yana abubuwan da zatayi ta wuce.

" duk tsun tsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, ka daiji abunda nurse ta fada yanxu" inji Yazeed,

Tsaki Yaseer yayi " mai uwa a gindin murhu ba ya kukan ban koshi ba," wayar shi ya dauko ya Kira mahaifiyar shi cikin shagwaba da sakuwa yake magna,
" pls mom wlh yarinyar tana cikin mawuyacin hali, hava mom ko fadeela ce ki turo Dan Allah, oh my god yaushe fadeela ta tafi? Banji me ake cewa bangaren can ba amma ga alama bai samu nasarar convincing mahaifiyar tashiba ko da ganin yanda ya ajiye wayar,

Hada idanuwa sukayi da Yazeed " yadai zata zo ne?" Yazeed ya fada yana yamutsar fuska saboda baki daya asibitin ta gundure shi.

" bazata bar mijinta shi kadai ba" Yaseer ya bashi amsa

No comments:

Post a Comment