Sunday, 6 August 2017

Yazeed ko Yaseer

[1/2, 10:42 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer
           Nah
   Ayshart Farouq

Nagarta Writers Association
   ©NWA©

           30
Kuka sosai Afnan keyi, yayin da Yazid yayi kwance reran yana maida nunfashi, ganin kukan nata bamai karewa ba ne yasanya yajawota jikinshi yana lallashinta,

" plz Afnan Dan Allah kiyi hakuri ki yafemin wlh bada son raina nayi miki haka ba,  i just don't know what to do, Ina cikin tsananin bukata ne shiyasa naga ke kadai ya dace ki taimaka min keda Zan aura believe me Afnan wlh ban taba aikata zina ba ya karashe maganar cikin kuka,

Tureshi tayi jikinta,
" bakada abunda zakace min in yarda da Kai Yazid, kuma kasani Alla yana ganin ka bazai taba barinka ba Allah ya isa tsakanina da Kai, ta fada tare da mikewa sai dai wani azbtacen ciyo taji Wanda yasanya ta sake komawa zaune tana fitarda hawaye.

Da sauri Yazid ya yunkuro don ya kamata sai dai cikin zafin nama ta bige mishi hannu,

" kada ka sake tabani macuci azzalumi, ka bude min kofa infita wlh ko inma abunda baka tsammani"
 
" Dan Allah Afnan kiyi hakuri ki gyara jikin ki sannan ki je plz Dan Allah ba Dan halina ba"

" Kai har kasan Allah ne? Ai ni bana tunanin kasan Allah don da kasan shi da bakayimun abunda kayimin ba, ka bude mun kofa infita nagaya maka," ta fada cikin tsawa,

Haka ya mike jikinshi duk a mace yaje ya bude Mata kofar,
Da kyar ta mike tana dingirshi hawaye nafita idanuwanta ta bar gidan tana jin dama ba a haifeta ba da ganin rana irin ta yau,

Keke napep ta samu tashiga ta isa gida, amma  kallo daya zaka Mata ka gane cewa ba lafiya ba,

Cikin faduwar gaba tana bin gini ta isa falon gidan, mahaifiyarta taci karo da ita zaune tana kallon sunnah tv,

" subhanallah Afnan lafiya kuwa? Me yake damunki ne?"

Kasa bata amsa Afnan din tayi sai kawai ta fashe da kuka,

Hankalin momy yayi matukar tashi   ta mike tsaye ta isa gurinta tana girgizata

"Ki fada min Afnan me yake damunki?, lahaula walakuwati illah billa, Afnan miye a zanenki haka?"

Jin wannan tambaryane ya sake jefa Afnan cikin rudani,
K'ank'ame momy tayi
" wayyo momy mutuwa zanyi marata ciyo takemin sosai "

Momy tayi ajiyar zuciya sannan ta ja diyar tata cikin tausayawa " kai wannan ciyon mara ya gwada miki bone Allah dai ya miki maganin shi, muje ciki ki wanke jikin ki kisha magani kinji"

Haka tajata takaita har daki tare da fitar Mata da magungunanta sannan ta fita tanata jimamen ciyon Mara irin na diyar tata,

Afnan kuwa ba abunda takeyi a toilet idan ba kuka ba,  rayuwarta ta Mata zafi ji take tamkar Allah ya dauki ranta ta mutu ta huta da wannan rayuwar duniyar,, ganin kuka bazai Mata magani ba yasanya ta daure ta gasa jikinta a ruwan zafi sannan tayi wanka ta fito,.
Pain relief ta samu ta Dan sha sannan ta kwanta cikin kankanen lokaci bacci ya dauketa Wanda ya kasance baccin bakin ciki mafi muni a rayuwarta.

Sai bayan la'asar ta falka, jikinta ba laifi taji sauki sosai sai abunda ba'a rasa ba, arwalla ta Doro  tayi sallah sannan ta sake kwantawa Sam bata damu da yunwar cikinta ba don tasan ko kadan bazata iya cin abinci ba,
Miss call din Yazid kan sunfi a kirga a wayarta tare da texts dinshi na ban hakuri amma ganin suma kara tunzarata yayi wata irin  tsanar shi takeji a cikin zuciiyarta, kashe wayar tayi baki daya sannan ta kwanta, sai gab da magrib ta tashi, momy ce ma ta matsa Mata tadan ci abinci,

           
              31

Saida Afnan ta share kwana da kwanakki tana ignoring call din Yazid duk da tasan ba karamin takura zuciyarta tayi ba, saida taga ta gasa shi da kyau sannan tafara daukan call dinshi, shima idan ta dauka duk  maganar da tazo bakinta gaya mishi takeyi sai daga baya   ya samu ya lallasheta da magangannu masu dadi har yasamu ya shawo kanta ta hakura  suka koma kaman yanda suke a da, amma  wani lokaci idan ta tuna abunda ya Mata takanji ta tsane shi da duk ma wani namiji a fadin duniyar nan ita dai fatan ta Allah ya tabbatar da auren su ko zata samu kwanciyar hankali.

Bayan sati uku da faruwar haka Afnan ta shiga tashin hankali na rashin ganin call din Yazid har na tsawon sati daya tun tana sharewa har abun yafara damunta kasancewar tun lokacin da ya Mata fyade tabar kiran shi sai dai shi ya kirata, ganin haka ne ya sanya ta yanke shawarar kiran shi taji ko lafiya sai dai yanzu kusan kwana biyu tana kiran wayar a kashe, hankalinta ba karamin tashi yayi ba gashi Abban ta yace,  iyayen yazid basu kirashi ba don haka ta gaya ma Yazid din jibi ya turo magabatan shi tunda ya dawo tun last week su kadai yake jira don yanada abunyi.

Kwance ta ke ta kudndunne cikin bargo kasancewar yau da zazzabi ta tashi da ciyon Kai ga wata irin kasala da takeji,

Momy ce ta turo dakin ta shigo da sallama,

" Afnan lafiyarki kuwa mahaifin ki na kiranki bakya dagawa,?"

"Rass rass! Gabanta ya fadi lafiya kalau momy kaina ne yake ciyo shiyasa nasanya  wayar silent  banji ba"

" eyya Allah ya sauwaka, tashi kije mahaifinki na neman ki sai kisha maganin" ta fada tare da wucewa

Haka Afnan ta mike jikinta duk ba dadi kanta tamkar ya cire saboda tsananin ciyo,

Falo ta same shi zaune kamar ko yaushe sallama tayi, tagaida shi tare da neman guri ta zauna,

Kallonta yayi cikin kulawa sannan yakira sunan ta da "Afnan"

"Na'am Abba" ta karba muryarta na rawa

Yaci gaba da cewa, "ina so ki san cewa duk abunda ya faru ga bawa daga Allah ne kuma Allah yana son bayinshi masu hakuri da tawakkali, Afnan yanzu Yaron da kike so ya kirani ya shaida min cewa ya fasa auren ki"

Wata irin Kara Afnan ta buga tare da faduwa kasa sumamma......

Har yanxu dai Ina Mai baku hakuri kan errors din da zaku gani manage ne kawai nake Ina typing din luv you all my fans

©Ayshart one©
[1/8, 9:53 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer
           Nah
Ayshart Farouq

Nagarta Writes Association
   ©NWA©

           32
   Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Abba ya shiga fadi tare da kwalawa momy Kira, itama momy da sauri tashigo dakin, ganin Afnan kwance ya sanya ta rude ta shiga tambayar Abba " me yafaru da ita ne alhaji?"

Cikin dakakkiyar murya ya kwashe abunda yafaru ya gayamata, kuka momy tashiga rusawa tana fadin, "toh me tayiwa wannan yaron ne da zai saka Mata da haka? Gashi yanzu yaje ya kaimu ya baro",

Ganin kukan momy ba Mai karewa ba ne saima kara daga mishi da hankali da takeyi ne ya sanya ya rarume ruwa ya shiga zuba mata yana kiran sunanta.

  A hankali ta bude idanuwanta tar kan mahaifinta kanta ne takeji wani irin gingirim da shi, yunkurawa tayi zata tashi momy tayi saurin tayar da ita tana mata sannu, kallon mahaifiyar tata tayi idanuwanta cike da hawaye,
" momy kinji wai Yazid yafasa aure na"
Momy ta shafe Mata kwallar da ta zubo fuskarta " kiyi hakuri Afnan komai mukaddari ne, ko yanzu ma ai ba'a cire rai da tsammani tunda baki mishi komai ba"
  Gyada kanta tayi " momy Yazid ya cuce ni ya cuce rayuwata ya........... Bata ida fada ba taji zuciyarta ta hautsine wani irin amai ya taso mata, da gudu tayi toilet tamkar zata amaye yan hanjinta gashi dama cikin ba komai a cikin sa,

  Momy da ke bayanta sai sannu take mata cikin ranta tana matukar tausayin diyar tata da ta fada tarkon soyayya,

Tana kare aman momy ta rikota jikinta duk ya gashe yayi zafi sosai ba wanni karfi a tattare da ita,
Momy tace, " alhaji inaga fah ya kamata aje da ita asibiti a dubata don naga jikinta yayi zafi sosai kar wani Abu yazo ya sameta daga baya,"
Abba yace, " nima abunda nake tunani kenan, yanzu dai abunda za'ayi kije kibata abinci taci nama Ibrahim waya tun dazu zaizo ya dubata.

Haka momy taja Afnan ta kaita daki ta tsareta saida taga taci abinci amma abincin ko minti biyu masu kyau bai samu ba ta amayar da shi, hankalin momy ya tashi sosai, nasifa ta shiga yiwa yar tata don ita ganinta duk damuwar da tasawa kanta ne yasanya ta shiga wannan halin, saida taga hankalinta ya Dan kwanta sannan ta tashi tabar dakin,

Tana fita Afnan ta dora daga inda ta tsaya kuka ta shiga yi tamkar ranta zai fita, wata irin tsanar Yazid da soyayyar shi suka bijiro Mata lokaci daya, cikin ranta kuwa sai fadin takeyi, " Yazid ka cuceni ka rabani da mutunci na dama ashe ba sona kakeyi ba?, dama jikina kake so kuma ka samu Allah ya isa tsakanina da kai" haka taci gaba da kuka da surutai Kala kala ita kadai tamkar mahaukaciya, haka Ibrahim yazo ya sameta, shi kanshi ba karamin tausayi ta bashi ba allura ya Mata tare da wasu magungunna.

   Abba da momy kuwa haka suka sata gaba sunata kwantar Mata da hankali da magangannu masu dadi har takanji ta Dan fara samun relief din damuwarta.  

(Iyaye kenan Allah Kara mana son iyayen mu baki daya. Ameen)

Bayan kwana biyu da faruwar haka, ba wani chanji da aka samu kan rashin lafiyar Afnan saima abunda yayi gaba, zazzabi da amaye amaye kam ba'a ma magana abun ba karamin tayarda hankalin iyayenta yayi ba, shi yasa yau Abba ya yanke shawarar kiran likitansu don ya dubata yaga abunda ke damunta, tashin hankalin su daya kar ace ciyon zuciya ya kamata kan damuwar da ta sanya kanta a ciki.
            
         
              33
Kasancewar yau asabar dukan su suna falo Afnan da ba wani karfi a jikinta tana kwance ta dora kanta kan cinyar mahaifiyarta kallo daya zaka Mata ka gane tana cikin matsala saboda yanda ta Kara haske ta rame tayi fau da ita, yanzu haka ma aman tayi ga ciyon kan da yazame Mata tamkar kadangaren bakin tulu idanuwanta ma bata iya bude su sosai saboda azabar da takeji,

Doctor ne ya shigo da sallamar shi, bayan sun yi  'yan gaishe gaishe Abba ya bashi damar duba Afnan ba tare da bata lokaci ba yafara aikin shi.

Bayan ya kare yi Mata tambayoyi ne ya karbe fitsarinta,
Ya dube Abba " just give me five to ten minute I will be right back"  doctor ya fada tare da mikewa.

Batare ko da bata lokaci ba ya dawo duk suna nan zaune suna firar su,

Result din ya mikawa Abba, gwajin farko ya tabbatar da Afnan tana dauke da ciki na tsawon wata daya da kwana biyu.
Abunda idanuwan shi suka gani kenan mikewa tsaye yayi yana nuna likiti,
" amma dai likita wannan ba gaskiya ba ne ko?"
Doctor yace, "gaskiya alhaji abunda ka gani shine gaskiya 'yarka tana dauke da ciki"

" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Afnan kin cuce ne" Abba ya fada yana dafe zuciya saboda wani irin zafi da take mishi, ita kanta momy bata San lokacin da ta mike tsaye ba tana kalima, itama Afnan din mikewa tayi tana wani irin kuka Mai ban tausayi , yayin da Ibrahim da ke kokarin shigowa dakin yayi tsaye chak tamkar Wanda ruwa suka cinye,

Cikin tsananin tashin hanmali Abba yayo kan Afnan din yana "fadin kin cuce ni Afnan kin wargaza min tsari kin tuddamin mutunci na kin............" Bai ida fadi ba ya fadi kasa warwas saboda bugawar da zuciyar shi tayi lokaci daya,

Momy dake tsaye sai lokacin hawaye suka zubo mata, da gudu tayi kan Abba tana girgiza shi su Kansu su Ibrahim din kanshi sukayo suna salati,
Afnan ma cikin tashin hankali ta matsa kusa dashi tana fadin,  " wlh ba laifina ba ne fyade ya min wlh fyad........."

Marin da Ibrahim ya watsa  Mata ne ya sanya ta katse maganar,
" kika kashe mana uba wlh kema sai na kashe ki" ya fada cikin tashin hankali,

Doctor ya dube su "yanzu dai duk ba wannan ba mu dauki
Alhaji mu kaishi asibiti tunda nan ba kayan aiki"
Haka ko akayi aka kama shi akayi dashi asibiti cikin ikon Allah aka samu kanshi sai dai yana tashi ba abunda ya ce face " na yafeki Afnan har abada" wannan furucin ba karamin tayarwa momy da hankali yayi ba,

Afnan kuwa daga waje ta tsaya kasancewar an hanamata shiga dakin, sai rusar kuka takeyi tana cewa ba laifinta ba ne fyade ya Mata,

Sai da aka samu aka mawa Abba allurar bacci sannan Ibrahim ya dube momy yace,
" momy miye mafita yanzu akan Afnan don nasan Abba bazai taba barinta ta zauna mishi gida ba"

Momy ta dubeshi cikin damuwa tace,
" inaga tunda tace fyade ya mata kaman abun zaizo da sauki, yanzu kamata yayi aje a same yaron a gaya mishi idan ma ta Kama a shiga kotu shiga za'ayi don a fitar Mata da hakkinta"
Shawarar tama  Ibrahim dadi  shima,
waje ya sameta zaune rakube tana kuka
"Ke" ya Kira sunanta fuskar shi tamke,  "waye yamiki ciki? Kuma kikamin karya wlh yanka ki zanyi"
Saida ta fyace majina sannan tace,
"Yazid ne kuma wlh fyade ya min"
" kin san gidan su Yazid din?"
Gyada mishi Kai tayi,
" eh nasani"
"Ok tashi muje ki kaini ingan shi"

Batare da gaddama ba ta mike, momy tace,
Itama zata bisu sai Sagir ya tsaya gurin Abba don tafi son ayi komai a idonta, ba yanda Ibrahim baiyi ba don ta tsaya tace ita alan balan sai taje, ba yanda ya iya dole suka tasa Afnan gaba har gidan su Yazid din.
        
     
                  34
  A yanda Afnan keji ko daga bacci aka tadata zata iya zuwa gidan su don gidan bazai taba bace Mata ba har abada,

Hon sukayi maigadi ya bude musu suka shiga Ibrahim yayi parking duk suka fito,
Dai dai kofar da zata sada su da gidan suka bi wani mutum sukaci karo dashi, Wanda yanayin shigar shi ma zai tabbatar ma da shine mamallakin gidan,

Dakatar dasu yayi da  cewa, Ina zaku  masu gidan fah duk basa nan, hala bakuyi waya da hajiyar ba ne?"

Hannu Ibrahim ya bashi suka gaisa, yayin da momy ta gaidashi, ita kuwa Afnan kallo kawai tabishi da shi,
   Ibrahim ya dube shi yace, " Dan Allah ko Ina zamuga Yazid?"

" Yazid kuma? Ku kuwa me koke nema da Yazid?" Alhajin ya fada cikin mamaki,

Momy ta dube shi tace, "ko Kai ne mahaifin shi?"

Gyada musu Kai yayi " tabbas kuwa nine mahaifin shi wani Abu ne ya faru?"

Ibrahim yace, "kwarai kuwa wani Abu ya faru don kanwata tana dauke da cikin shi na tsawon wata daya"

" what?" Ya fada da karfi, cikin tashin hanakali " u most b mistaken, Yazid dina bazai taba ai kata wannan aikin ba, tun wurima kuje Ku nemo wanda yama yarku ciki amma ba Yazid ba"

Afnan ta fashe da koka " wallhi Allah shi yamin fyade Allah shine"

Jin maganar fyade da Afnan tayi ba karamin tashin hankali alhaji ya Kara shiga ciki ba,
Cikin mamaki ya sake kallon su " fyade fa ki kace?"

Afnana ta gyada Kai tana fyarce majina,

Saida yadan yi Jim na lokaci kadan sannan yace, " wannan magana bata yiyuwa anan Ku shigo daga ciki"  ya juya suka bi bayan shi,

Falon shi suka shiga suka zazzauna ya sake dubin Afnan " kin dai tabbatar da abunda kika fadi gskiya ne ko"

Sake gyada Kai tayi "eh"

Wayar shi ya dauko ya Kira Dan nashi, " kazo yanzu ina falo ina nemanka"

Cikin minti biyu yaron ya sauko daga sama cikin tafiyar shi ta kasaita hannuwanshi duka biyu suna cikin aljihun shi, sallama yayi ba tare da ya kalle mutanen da ke zaune ba, gurin mahaifin shi ya nufa " Abba gani kana nemana"

Cikin nutsuwa mahaifin nashi ya dube shi tare da nuna mishi Afnan "me yarinyar can ta maka ka Mata fyade?"

Yanda ya dube Afnan d'ai zai tabbatar maka da cewa Kalmar mahaifin nashi ba k'aramin ruda shi tayi ba,

Ita kanta Afnan din tana hada ido dashi taji wata irin mumunar faduwar gaba don ita bata taba gani  shi ba ma,

Haka Ibrahim ma da  yakasa b'oye mamakin shi ganin abokin aikin shi da yayi,

Cikin tashin hankali yace,
"Dad fyade fa kace? Ni fah ban ma taba ganin wannan yarinyar ba" ya fada yana kallon mahaifin nashi,

Ran Ibrahim da ya gama baci bai San lokacin da ya cakume wuyan shi ba yana cewa,
"Karya kake yi macuci, Yazid ka cuceni ka cuce zaman tare"

Shi kanshi Yazid din rayuwar shi ta gama baci, cikin tsananin fushi ya ture hannuwan Ibrahim daga wuyan shi, "dakata Ibrahim kada kayi da nasani daga baya wallahi tallahi ban taba ganin wannan yarinyar ba" ya fada yana nuna Afnan,

Afnan kuwa kuka ne yaci karfinta ita kanta tasan bata taba ganin shi ba toh amma me ke shirin faruwa da ita,
Cikin kuka tace, " ya Ibrahim ba shine yamin  fyade ba"

Baki daya kallonta sukeyi Ibrahim kuwa kanta yayi yafara jibgarta tamkar Wanda Allah ya aiko " don uban ki yau sai kin gayamin Wanda ya miki cikin nan"

Momy kam kuka kawai takeyi tana kiran " ku Kama min shi kada ya illata ta"

Baki dayansu kasa tare shi sukayi,
Afnan naganin zai kasheta ya sanya tace,
" wlh shi ne yamin yace idan nace shi yamin kashe ni zaiyi "
Jin abunda ta fada ne ya sanya Ibrahim ya saketa ya koma kan kujera yana dafe Kai saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki,

Yazid kanshi cikin tashin hankali yace, " ni mukayi haka da ke?"

Gyada Kai tayi alamar eh.

Kafin kace, me tuni mahaifin shi ya kwashe shi da wani irin wawan Mari, " irin wannan tarbiya na baka? Wallahi Yazid ka cuce ni"

Afnan kuwa tsanani tausayin yaron ne ya kamata saboda tasan taci amanar shi ba kadan ba, sai dai dole ne yasanya tayi haka don ta ceci kanta,

Muryar da bazata taba mantawa a rayuwarta ba taji "wai dad hayaniyar me akeyi ne?"

Mikewa Afnan tayi tana nuna Mai maganar "wallahi wannan Yazid din ne yamin fyade"

Baki dayan su kallon shi sukayi, 

Cikin mamaki mahaifin nasu yace, " ikon Allah YASEER din ne kuma yanzu ya miki fyade? Toh me kike nufi? Su fah ba yan biyu ba ne kuma basa Kama da juna, Kai wannan yarinyar Sam bakida  gaskiya kawai ki fadi tsakani da Allah Wa ya miki fyade  a cikin su yazeed ko Yaseer?,?

Ni dai marubuciyar nace daya daga cikin su ne ya Mata fyade, toh waye daga ciki YAZEED KO YASEER?

Masu karatu Ku biyoni next post don jin waye yazeed da Yaseer kuma Wa yamata fyade a cikin su

©Ayshart one©

No comments:

Post a Comment