[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko
Yaseer
Nah
Ayshart Farouq
NWA
10-15
Aisha Afnan 'ya ce gun Alh Umar Adam, Wanda
ainihin shi mutumin kano ne, yanada diya uku
Ibrahim, Sagir da Aisha Afnan, matar shi daya
wato Hjy Zainab,
akwai tazarar haihuwa sosai tsakanin yaran su
kuma tun bayan haihuwar Afnan basu sake
samun haihuwa ba shiyasa suka dauke son
duniya suka daura Mata,
tun Afnan tana karama burin mahaifinta tazamo
lawyer, shiyasa kwata kwata bata kula samari
har ta gama secondary school batada wani
saurayi ko wani Wanda take so ba kuma don
babu masoyanba sai dai don wannan ne ra'ayin
ta da na mahaifinta,
Ibrahim kuma ya qare karatun shi na medicine a
jami'ar england yayin da sagir yake karatun
business admin a malesia yayin da Afnan take UG
one a jami'ar bayaro da ke jahar kano tana
karatun law.
Tunda take karatun ta Kawai tasama gaba bata
damu da harakar kowa ba sai ta karatunta,
Tun lokacin da wani guy ya kyalla ido yaganta
yake bibiyar ta amma Ina yayi duk yanda zaiyi
don yaga ya mallaketa amma ya kasa saboda ita
ba irin matannan ne ba da zaka samu lokaci daya
kasanar dasu bukatar ka ba,
Wata Rana ta fita shopping tare da driver sai
motar su tasamu matsala ta tsaya musu kan
hanya ganin lokaci zai kuremata kafin a gyara
yasanya ta yanke shawarar shiga a dai daita,
bayan tashiga shop rite din ne tafara diban kayan
da take so, takai hannunta gurin wani turare
kenan sai aka dauka da sauri ta juya don ganin
KO waye, sai dai kallo daya ta mishi ta sauke
idanuwanta kasa saboda kwarjinin shi da tsabar
haduwar shi, murmushi yayi tare da cewa,
" wannan turaren nawa ne nariga ki ganin shi ki
zabi wani, ko in zabar miki ne? don Sam wannan
ma bai dace dake ba,"
Karo na farko a rayuwata da taji wani namiji ya
burgeta, gyada mishi Kai kawai tayi tana kallon
shi, wani Kala ya dauko Mata ya mika mata ,
karba tayi tare da yi mishi godiya ta wuce abunta
taci gaba da dibar abunda take so,
saida takare kaf sannan taje gurin biyan kuddin,
card dinta ta cire ta mika, ba zato taji ance Ai
anbiya Mata mamaki ne ya kamata ganin kusan
kayan 25k
"toh waye ya biyamin?" ta tambaya nuna Mata
shi akayi yana tsaye sai murmushi yake mata,
daure fuska tayi ta isa kusa dashi,
" malam miye na biyamin kuddi alhalin kuwa ban
saka ba?"
Murmushi yayi tare da cewa,
"Afnan kenan"
Zare idanuwa tayi tana kallon shi jin ya ambaci
sunan ta mika hannu yayi tare da karbar kayan
hannunta " banan ya dace muyi mqgana ba kinga
mutane sunata wucewa a gurin,
Yanda yayi maganar sai taji ya sake burgeta
saboda yasan mutuncin kanshi da darajar diya
macce, sake mishi kayan tayi tare da bin
bayanshi har bakin motar shi,
sanya kayan yayi a motar tare da cewa, "oya
shiga muje "
Girgiza mishi Kai tayi
"a'a bazan shiga motar ka ba tare nake da driver,"
Murmushi yayi
"ai har yanxun bai gyra motar ba"
ya fada yana kallonta,
" Anya kuwa wannan mutum ba aljani ne ba" ta
fada a ranta,
Ganin ba sarki sai allah ne yasanya ta shiga
motar tashi tare da jero mishi tambayoyi " Kai
waye? Kuma a Ina kasanni?"
Murmushi yayi am yazid kuma nasanki da
dadewa ya bata amesa batatare da ya kalleta ba,
" so why did u do all this to me ?" Ta sake
tambayar shi,
Kai tsaye yabata amsa da saboda Ina kaunar ki,
wlh Afnan soyayyar ki ta Dade a cikin raina ban
San ta yanda Zan gaya miki ba saboda naga baki
damu da kowa ba,
Ni sunana Yazid Ahmad Abdulrahman mutane
suna kirana da Ahmad Y Abdulrahman Ina
masters ne a bayaro university anana na sanki
faculty dinmu daya dake I hope wannan ya
gamsar da ke,?"
Ita dai Afnan kasa cewa komai ta yi saboda
mamakin shi da yakamata ganin har saida
yakawota bakin motarsu da ake gyara,
" idan baxaki damuba Ina son ki bani number ki
ko don murika zumunci,"
Ba musu sukayi musayar number, toh tun daga
ranar suka fara waya kuma suna haduwa a
school tun dai Afnan tana dari dari fashi har ta
daina ta saki jikinta dashi soyayya mai tsanani
tashiga tsakanin su,
Nan ta fayyace mai ra'ayin mahaifinta akanta
inda Shima akayi sa'a iyayen shi sunada wannan
ra'ayin duk da bai Kai irin na mahaifinta ba, haka
yasa Yazid ya daukarma alkawarin aure duk wuya
duk rintsi..
[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko
Yaseer
Nah
Ayshart Farouq
NWA
15-20
Da sauri ta Afnan ta is a gida gabanta sai
faduwa yake ganin motar mahaifinta, Mai aikinsu
taxi Karo da ita a falo cikin faduwar gaba tace, "
momy fah?"
Salah Mai aiki tace," tana sama gurin Alhaji,"
Dakinta ta wuce jikinta duk ya mutu tayi zaune
tare da rafka uban tagumi Allah Allah take tana
addu'a Allah yasa baima momynta fada ba, tana
cikin hakane taji wayar mimynta ta sake shigowa,
da Sauri ta dauka " momy na dawo tun dazu Ina
daki"
Can bangaren aka amsa da cewa, " Afnan kizo
dadyn Ku na neman ki,"
Batare da bata lokaci ba ta nufi part din
mahaifinta cikin faduwar gaba don har ga Allah
ta tsane kiran mahaifin nata duk da tasan baima
fiye yimata tsanani ba akan sauran yayunta.
Da sallama ta shiga dakin tare da gaida iyayenta,
cikin fari'a Abba ya ce, " zo nan uwata" murmushi
Afnan ta Saki ganin ba wata matsala,
Can ta matsa kusa da abbanta yayin da wayarta
tayi Kara, da sauri mahaifinta ya kalleta tare da
mika hannu ya karbi wayan don ganin ko waye
yake kiranta,
Cikin tashin hanakali Afnan ta mika mishi wayar
ganin sunan dake rubuce wato maryam2 ,
Ganin sunan ne yasanya yamika Mata wayar tare
da cewa, " dauki wayar tukun,
Hannunta har rawa yake gurin karbar wayar,
kafin tayi wani abu har Call din ya tsinke, ajiyar
zuciya tayi har saida abban Nata ya kalleta,
Kafin suce komai wayar ta sake daukan ruri, a
hanakali ta Kara wayar a kunne " assalamu
alaikum" can bangaren aka amsa da "my princess
da fatar kin isa gida lfy", marar gaskiya Ko a
ruwa sai yayi jibi duk a.c dake dakin bai Hana
Afnan yin zufa ba don ganin take tamkar
mahaifinta najin abunda Yazid ke fadi ,
A sanyaye tace, " eh wlh maryam nazo ban
sameki ba , ok to sai mun hadu islamiyar gobe,"
tayi saurin datse wayar tare da mikawa Abbanta
wayar,
Cikin murmushi ya karba, sai da ya duba
contacts dinta kaf duk tana zaune tana kallon
shi, wata kwalla Ce ta zubo Mata wadda batasan
lokacin da ta zubo ba.
Momy dai zaune kawai take tana Lura da halin da
diyar tata take ciki, nan take duk tausayin ta ya
kamata yayin da cikin ranta take tir da hali irin na
mijinta da ya kasa gane halin da rayuwa take ciki
a wannan zamani,
Kasa hakura tayi saida tayi magana
" amma dai fisailillahi alhaji abunda kakewa Afnan
Sam bai dace ba kaine ka haifeta amma ace ka
kasa yadda da ita wannan wace irin rayuwa ce,
Dagowa yayi ya kalleta fuskarshi tamke,
" bana son irin abunda kike mun zainab ni Ina
hango abunda baki hango ba, kun matsa abata
waya na bata waya don haka dole ne a gareni
matsayina na mahaifinta in Lura da abunda take
da wayar don bana so Allah ya kamani da wani
laifi akan tarbiyar Afnan gobe kiyama, don haka
idan kinji kina iya taimaka min mu tarbiyantar da
ita walillahil hamdu idan kuma kinji baki iyawa
kuwa kada ki sake min magana akan abunda
nake ganin shine dai dai."
Cikin bacin rai momy tace, "ai wannan abun da
kake ba shine tarbiya ba, tarbiya duk bai wuce ka
aurar da ita ba "
Daga Mata hannu yayi " kinfi kowa sanin cewa ni
mutum ne wanda yake so yaga Dan Adam ya
dogara da kanshi don haka maganar aure ba
matsala bace, idan lokaci yayi ni da kaina Zan
zabo Mata mijin da ya dace da rayuwarta,"
Afnan najin wannan maganar Bata San lokacin da
ta fashe da kuka ba Wanda saida yabaiwa iyayen
nata mamaki dukan su ,
Da sauri Abba ya dubeta " miye haka Afnan? Mi
kekewa kuka ne?
Cikin bacin rai momy tace, " ai dole tayi kuka
tunda taji kana nema ka tauye Mata hakki,
wallahi alhaji kaji tsoron Allah kasani yanda
mukeda hakki akan yaranmu haka suma suke da
hakki a kan mu,"
Jikin Abba yayi matukar sanyi baice komai ba ya
mikawa Afnan wayarta tare da cewa ,
" tashi kije daki Afnan yi hakuri share hawayen ki,
jeki Zan sake nemanki ,"
Jikin Afnan sanyi kalau ta tashi taje daki da
tunani da yawa a zuciyarta ,
Number maryam2 ta lalubo wato Yazeed dinta,
fira suka shigayi sosai tamkar za su cinye junan
so saboda so da kauna, basu sukayi sallama ba
saida aka fara kiran sallahr magriba..
Ayshart one
[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko
Yaseer
Nah
Ayshart Farouq
NWA
20-25
Bayan sati biyu da faruwar haka Afnan suka
koma makaranta wannan karon komawa hutun ya
Mata dadi don kusan kullun tana tare da Yazeed
dinta karatun ma yanzu tafara ja baya dashi don
wani lokaci ko attending lectures batayi tana can
gurin yazeed suna soyewa haka kuma idan
tadawo gida matukar tana daki to kuwa suna
manne a waya,
Afnan! Afnan!" Taji muryar yayanta sagir yana
kwala mata kira,
Harararsa tayi , " miye ne" tana kwance kan gado
rungume da wayarta tana waya da Yazeed,
hankalinta kwance saboda ba kowa zai fahimce
waya takeyi ba amma duniya taki jinin tana waya
dashi a katseta ,
Ganin hararar da take ta zuba mishi ne yasanya
sagir din karasowa cikin dakin,
" ni kike harara?, Allah Zan buge idanuwan nan"
Turo baki tayi " to miye ne na kwalamin Kira
haka kaman kaban ajiya ne"
Tsaki yaja " to Abba ne ya aikoni in kiraki, idan
kuma bazakije ba sai inje in fada masa kina waya
bakida lokacin amsa kiransa",
Zaro idanuwa tayi "Allah gaya sagir ba waya
nakeyi ba waka ce nake sha kada kamin sharri
wlh bazan sake hararanka ba kayi hakuri Dan
Allah kace, Ina zuwa"
"Kyat" yayi kyafci tare da banka Mata harara, "
yace, " kinyi sa'a wlh da kinga sharri,"
Nan ya fice ita kuma ta mike da sauri,
Ta bangaren Yazeed kuwa sai tsokanarta yakeyi
da yake headphone ne a kunnen ta,
" kicewa Abba kina biyayya Wa miji ne kina
faranta masa rai kina masa fira Mai dadi yana jin
muryarki Mai dadi tana ratsa jikinsa kina samun
lada,"
Dariya Afnan din tayi tare da cewa,
"Yazeed kenan!, kwarai kuwa Zan gaya mishi idan
yazo min fada har Kai sai a tattara a hada"
Shima dariya yayi "ba komai ai kin San dama
dadi da wuya munyi alkawarin rabashi nida ke,"
Murmushi tayi tamkar yana ganinta, " Zan dauki
wuyar ka dauki dadin"
"_a'a ni Zan dauki wuya ke ki dauki dadin"
" ni dai a'a" ta fada cikin muryar shagwaba,
A kasalance yace, "kin ganki ko? kin Fara kashe
min jiki da shagwabar nan taki ko? Yanzun
tunanin ki sai ya fitine ni ya hanani sakat,"
Dariya tayi " ai haka nake so tunanina kadai
yafitine zuciyarka "
"Afnan" ta sake jin muryar mahaifiyarta, da sauri
ta katse wayar ta fita da gudu, tace,
" gani nan zuwa momy ina toilet ne "
" toh maza kiyi sauri Abban Ku na son magana
dake tun dazu"
Ta karba da " toh momy"
Nan da nan ta nufe falon nasa zuciyarta cike da
tunanin KO wane Kira ne yake Mata ?,
Ganin Ibrahim da sagir ne da tayi da kuma
mahaifan nata yasanya gabanta yashiga faduwa
dole ne tasan akwai maganar da Abbanta zai
mata.
Aysh
Sunday, 19 March 2017
Yazeed ko yaseer
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment