Wednesday, 23 November 2016

Damuwata

[11/23, 6:14 PM] Ayshart one💞: Damuwata
Na
Ayshart Farouq

         61
Bayan kwana biyu da faruwar haka ina guarding zaune tare da hotunan mahaifiyata kasancewar yanxun Ina yawaita mafalkinta yauma da asuba nayi mafalkin ganinan kwance kan cinyarta tana min tsifar Kai.
"Allah sarki"
Nafada tare da kai hoton bakina na sumbata, ban Ankara ba sai ji nayi an zafce hoton daga hannuna

Cikin sauri na daga idanuwana don ganin ko waye,

Sai dai kallo daya namishi na sunkuyar da kaina qasa Ina wasa da yatsuna,

Zama yayi daf Dani yana cewa,
" KO su waye acikin wannan hoton da gani suna da muhimmanci a gurinki"

Ni kuwa da tun tuni kamshin turaren shi yayi awon gaba da tunanina banma ankara ba saida naji ya kira sunana
" muhibbat"

Nayi saurin karbawa da
" uhum" tare da kara matawa gefe,

Bai damu da kara matsowa ba yaci gaba da magna,
" ranar sai kika gudu kika barni ko?"
Ya fada tare da zubomin ido,

Bance komai ba kaina a kasa Ina wasa da yatsuna.

Bai jira nayi magna ba yaci gaba da cewa,
" me yadawo dake gidannan?"

Idanuwana suka kawo kwalla nace,
" gida aka dawo dani"

Dan matsowa yayi kusa dani,
" me yasa aka dawo dake kuma Wa yadawo dake?,"

Wannan karon kam fashewa nayi da kuka ba don banida amsar tambayar ba sai dai don ban san ya zan amsa mishi tambayar ba,

" subhanallah" ya fada
" muhibbat miye abun kuka anan? Ko dai ke don kuka bai miki wahala ne plz kiyi shiru ki amsamun tambayar da namiki ko Allah nasa inada taimakon da Zan baki I don't want see you cry pls ki share hawayin ki, ki fada min matsalarki" yafada tare da mikomin handki

Ban karba ba nasanya hannuna nashafe  hawayen amm kuma bance komai ba,

" uhum inajinki gayamin"

Cikin rawar murya nace,
"Ba komai ni nadawo da kaina"
Na fada tare da mikewa Ina shirin in wuce ban ankaraba sai ji nayi ya jawoni da karfi yana cewa,
" ba gskiya ba ne, kin San Allah baxaki bar gurinnan ba sai kin fadamin matsalarki,
Su waye nan a pic dinnan?,"

Idanuwana suka kawo kwalla inata neman in kwace hannuna in gudu amma Ina qarfi ba dai ba

         62
Cikin muryar kuka nake cewa,
"Dan Allah ka sakemin hannuna Allah fah ya hana,"

Kallona yayi ido cikin ido zan sakeki amma sai kinyi alkawarin bazaki gudu ba,"

Cikin sauri nace " eh baxan gudu ba sake ni"

Ai kuwa yana sakina nayi wuf Zan gudu, ba zato ba tsammani naji ni kan kirjinshi,
Innalillahi wainna ilaihirraji'un "wannan wace irin musiba ce?"
Kuka kawai naashe dashi amma ko a jikin Farouq saima Kara kankameni da yayi yana bubbuga bayana alamar lallashi.

Don kanshi ya sakeni tare da zaunar dani yana kallona,
Cikin wata kasalalliyar murya yayi magana
" oya bani labarinki inajinki"

Ganin babu sarki sai Allah yasanya nakwashe tarihina duka nagayamishi,

Kanshi ya dafe tare da hannayenshi  idanuwab shi sunyi jajur tamkar garwashi, dubana yayi tare da cewa,
" wannan hoton fah?"
Atakaice nace,
" hoton mahaifiyata ne tare da yayarta,"

Kallon hoton yayi sosai yana jujjuya shi,
" wannan hoton ai yayi tsufa da yawa fuskokin suma basu fito sosai ba,"
" uhum" kawai nace don Allah kadai yasan yanayin da nake ciki gashi na matsu yabar gurin ko don gudun abunda kanje yadawo,

" me kike tunani ?" Naji yafada  cikin sarkakkiyar murya,

"Ba komai" nafada tare da mikewa, " zan wuce ciki inada aiki," na fada kaina a qasa a tunanina zai bani hoton sai kuma naga yasanya shi cikin aljihunsa  ya dubeni yana murmushi " idan kina son hotonki kizo nan gobe bayan la'asar ki karba Ina jiranki,"

Bance komai ba juyawa kawai nayi nawuce abuna tamkar Zan fadi sabida tsabgegen saurin da nakeyi,
a raina kuwa sai cewa nake, " ai wlh bazaka ganni ba haka kawai mutum na nema ya jazamin bala' i Allah yamin tsari dakai da kuma dukkan sharrin ka,"
Har na isa gida abunda zuciyata ke rayamun kenan,

Shi kuwa Farouq tunda ta wuce yakasa daina kallonta Alla kadai yasan abunda yakeji game da yarinyar wani abu yakeji Wanda bai tabajin kwatan kwacin irinshi ga kowa ba,
Tsantsar tausayinta ne ya sake dabaibaye mishi zuciya,
" I will help you muhibbat, Zan taimakeki matukar Ina raye Zan fitar dake damuwarki da yardar ubangiji. shi kadai yake magana kamar wani zarrare.




©Ayshart one ©
[11/23, 6:14 PM] Ayshart one💞: Damuwata
               Na
    Ayshart Farouq

              63
Ni kuwa tun ranar nashiga wasar boyo dashi duk wata hanya da nasan zata sadani dashi gudunta nakeyi,

Misalin karfe biyu da rabi na rana  inata hada hadar hada lunch hajiya da nusaiba ne zaune fira suke kasa kasa,

Nusaiba ta dube momyn ta tace,
" kinga fadeela ansamu shiga gurin yaya Farouq tun dazun take gurinshi da alama yau na kwaran nanan,

Hajiya tace, " ai yanxu kwana biyu naga chanji  sosai a tattare dashi game da fadilar tunda har  yana tsayawa suyi fira,"

" dama ai miskilanci ne kawai irin na yaya Farouq yana so yana Kai kasuwa" dukansu suka kwashe da dariya,

Suna cikin cin abincin ne fadeelah ta sauko fuskarta ba alamar fari'a,

Nusaiba ta dubeta cikin tsokana tace,
" kaga sis ansha soyayya anxo Ana wani daddaure mana fuska,"

Dan murmushi tayi kadan tare da kwalamin kira ,
" muhibbat"
Cikin sauri naxo Ina cewa "gani,"
Harara ta watsamin sannan tace,  " kije kije ki hadawa ya Farouq lunch dinshi sannan kuma ki dafa mishi ruwan zafi masu kayan yaji don yanajin zazzabi,"
Tana fadin haka tasami gurinan ta zauna tana cewa,
" momy ya maganar fitar zamunje ko sai goben?"
Banji amsar da tabata ba natafi naci gaba da aikin hada mishi lunch din, amma harga Allah saida naji gabana yafadi da nasan yanda zanyi kada naje da nayi don kar in hadu dashi,

Koda nadawo su nusaibar kawai ne natara fadeela taariga ta koma sama gurin Farouq din.

falon nasame su zaune suna fira sanye yake da dogon wando da singlet, kasa yake zaune kan kafet yadan jingina da kujera tare da pillow remote ce hannunshi yadan fada yayi duhu,
Fadeela kuwa tana zaune kusa dashi sai zuba mishi surutu take da kissa da kisisina

" Assalamu alikum"
Nayi  sallama cikin rawar murya don harga Allah a tsorace nake,
Shi kadai ya amsa a ciki sabida muryarshi bata fita sosai fadeela kam harara ta watsomin tare da nunamin inda Zan ajiyewa da sauri na qarasa gabansu na ajiye ganin duk a kasa suke yasanya na ajiye musu a kasan,
" oya yi saving dinmu "
Fadeelah ta fada tana kallon Farouq da tun shigowata idanuwan shi suke kaina,
" dear ka lallaba kaci duk yanda yake kaji"
Ta sake a fada cikin shagwaba,
" ok"
Kawai yace tare da danyin murmushi yana dubanta dadi kawai takeji tasamu kan Farouq batasan tana kasa tana dabo ba

            

              64
Da sauri na dauke plate da saving spoon Dan zuba musu abincin amma kwata kwata nakasa sabida tsabar rawar da hannuna keyi,

Tsawa ta dakamin " ke wai miye haka ne?"
Saboda tsoro banma San spoon din ya subuce hannuna ba ya fadi kasa idanuwana tuni sun cicciko da kwala,

" kinga fadeela ni fah abincin ma yafita raina bazan iya cinshi yanxu ba"
Farouq ya fada cikin daure fuska,

Idanuwa ta gwalo mishi "haba ya Farouq me kace ne da zakace bazakaci ba yanxu?"
Yace,
" ba komai kawai dai banajin cin abincin ne yanxu"

Hannuna kawai ya mikomin tare da karbar saving spoon din hannuna, yana cewa " kinga Bari inyi saving dinki da kaina idan zakici,"
Cikin bacin rai tace,
" nima na koshi"
Tabe baki yayi tare da zuba Mata ido ganin yanda taketa cika tana batsewa,

Wani kallo ta watsomin tare da yimin tsawa,
" don ubanki tashi ki bacemin da gani tun kafin inyi ball dake kazamiyar banza,

Kwallar da naketa makalewa ban San sanda ta fito min ba,
sumui sumui na  mike  ha nakai bakin kofa naji ta sake dokomin Kira, da sauri nadawo kaina a kasa naji tace,
" jeki ki gyara Mai dakinshi ki wanke toilet din"

Banko dube su ba na wuce dakin domin gabatar da abunda ta sani,

Direct toilet naje nawanke shi tsabal sannan nadawo dakin shima nagyara shi sosai sanna nafita,
Ga mamakina sai na same Farouq shi kadai a falon zaune kan kujera,
Gabana faduwa kawai yake kafafuna kuwa sai sasarfa suke tamkar Zan fadi,

" muhibbat" ya kirani can qasan makoshin shi, tsayawa kawai nayi ba tare da naje ba kuma ni ban wuce ba,

Fuskar shi tamke yayi magana,
" zo ga hoton ki"
Ya fada yana mikomin hoton ko alama fuskarshi ba alamar wasa kwarjinin shi ya bala' in qara fitowa ganin yanayin fuskar ne yasa nayi saurin karasawa don ko ba komai Ina matukar bukatar hoton,

Da sauri na mika hannun don in karba kawai sai ji nayi ya chafke min hahannuna.


©Ayshart one ©
[11/23, 6:14 PM] Ayshart one💞: Damuwata
                Na
     Ayshart Farouq


             65
Fuskar shi a marairaice Yake magana tamkar bashi ba,
" plz muhibbat ki sauna muyi magana Dan Allah I have no one to advise me  i am badly need of you help  buh idan kina ganin kamar wani abu zanmiki bazan takuraki ba zaki iya wucewar ki don  bana so inshiga hakkinki " ya fada tare da sakemin hannu ya lumshe idanuwanshi jikinshi duk ya mutu bashida wani kuzari a tattare dashi.

Ganin yanda yake ne yasanya nima jikina ya mutu duk tausyin shi ya kamani nan take naji bazan iya tafiya inbarshi a halin da yake ciki ba,
a hankali na furta
" Ina tsoron wani yazo ya sameni a nan,"

Har yanxu idanuwan shi a lumshe suke tamakar maijin bacci,
Cikin wata kasalalliyar murya yayi magana " ba kowa a gidan duk sunfita "
Jin haka ne yasanya hankalina yadan kwanta a wani gefe wani gefen kuwa a tashe yake.

Cikin sarqaqqiyar murya nace,
" inajin ka how can I help u?"

Da sauri ya bude idanuwan shi yana dubana,
Murmushi yayi tare da lasar leben shi na kasa da ya bushe,
" zauna a nan"  ya fada yana nunamin kujerar da take kusa da shi,
Batare da nakalle shi ba na nemi guri nan qasa na zauna tare da takure dukkan jikina da kagganni kasan bana cikin nutsuwa,

Shima kasa yadawo ya zauna tare da jinginawa kan  kujera,
" mikomin pillown can yayimin nuni da da pillown da nasame shi kwance a Kai,
Hannuna kawai na zula na miko mishi ya aza don yaji dadin jinginawa da kyau,
" muhibbat" ya Kira sunana yana kallo na,
Kaina a kasa na furta
" na'am Ina jinka"

Wani dan huci yayi tare da furzar da iska mai zafi,
Sannan yace,
" nasan dai kinada labarin auren dolen da ake so a min ko?"

Da sauri na dago kaina muka hada ido dashi nasake yin kasa da kaina a raina nace,
" Kama raina mutane Farouq  ni xaka cewa baka son fadeela  this is not possible "

" it is muhibbat wallahi bana sonta ko kadan"
Da sauri na dubeshi Ina zare ido Ashe a fili na fada,
Gyada min kanshi kawai yayi alamar da gaske yake,
Sannan yaci gaba da maganar shi
" na dauki fadeela tamkar yanda na dauke Nusaiba wallahi tallahi beside dis  I don't have any filling about her,
Bantaba jin sonta ba koda na second daya ol i know tsanar da nake mata da ta wani dalili yanxun nadaina sabida nasamu abunda da nake ganin tamkar ita ce silar da narasa shi, a gsky idan aka auramin ita Zan cuceta in kuma cuce zuciyata ban San ya zanyi ba abubuwa sunmin yawa a zuciya am very sure nasan inada rauni a zuciya na plz tell me wat should I do"

           66
Idanuwan shi sun rine sunyi jajur can ciki har wata kwalla kake hangowa wadda gwarzon namiji ne kadai ke iya riketa,

Yaban tausayi matuka dukda har yanxu ban gasganta magabarshi ba,

Kaina a kasa nace,
" shawarata daya kayiwa iyayenka biyayya kayi abunda suke so idan dai har kana so  kaga dai dai a rayuwarka"

Kallona kawai yake ko kyaftawa bayayi, nan take ni kuwa na
dabirce ba shiri nayi shuru,

" uhum inajinki muhibbat,"

Cikin inda inda nace,
" shi kenan dama"

Murmushi yayi tare da sanya hannayen shi duka biyu ya rike fuskar shi, saida yayi kusan minti biyu a haka sannan yayi magana,
" muhibbat yunwa nakeji bani abinci inci"

Abincin da nakawo mishi yana nan inda yake shi na jawo na zuzzuba mishi ganin har yanxu fuskar shi na cikin hannayen shi ne yasan ya nace,
" ga abincin nan ni Zan wuce"

Da sauri ya dago ya kalleni " no ba yanxu ba ban kare magana ba"

Mika mishi abincin kawai nayi tare da zuba mishi ido,

" xo mu ci" ya fada yana kallo na,

Da sauri nagyada mishi Kai alamar a'a,

Bai sake cewa komai ba saida yayi kusan spoon biyar sannan yace,
" nadade banci abinci ba ko na dauko zanci kasawa nake saboda tunani yamin yawa ko yanxu da ba don ke ba da baxan iya ci ba"

Duk maganar nan da yake bai dubeni ba abincin shi kawai yake ci,
Ni kuwa kallon shi kawai nakeyi don bansan inda zancen shi ya dosa ba,

Saida ya cinye abincin tatasa sannan ya dubeni yayi murmushi bani ruwa a fridge mikewa nayi nadauko ruwan inata mamakin yanda ya cinye abincin nan shida bashi wani cin abinci,

Mika mishi ruwan nayi ya sha tare da yin hamdala sannan ya koma ya gincira yana kallona yana murmushi,

Nima wannan karon murmushin nayi Wanda bansan lokacin da ya subucemin ba.

               67
Ci gaba farouq yayi da maganar shi kamar haka,
" naji shawarar ki nagode kwarai Allah yasaka miki da alkhairi amma kin San wani abu?"

Girgiza kaina nayi alamar a'a,

" zan fah iya rasa rayuwata  idan ban mallaki wadda nake so ba bantaba soyayya ba  sai akanta nasan so nasan minene so wallahi rasata a gareni ba karamin tashin hankali ba ne bazan iya rayuwa ba tare da ita ba"

Ya karashe maganar cikin sarkakkiyar murya,

" subhanallah!  Wannan fah bai dace dakai ba Sam bai kamata ka rika irin wadan nan magangan nu ba duk Dan Adam yanada tashi kaddara ko Mai kyau ko mummuna kuma yarda da wannan kaddarar imani ne so kga irin wadannan magangannu basuda amfani sai ma su sanya mutum yarasa imanin shi dama a rayuwa ba dole ne mutum yasamu abunda yake so ba"

Shikan Farouq mutuwar zaune yayi gurin kallon muhibbat
" wai ashe tana magana haka? ashe tanada ilimin tauhidi a haka?,
Ya subhanallah!" Ya fada a fili

Da sauri na dago na dubeshi tare da mikewa
"nikan Zan wuce kawai ayukkan da zanyi da yawa"

"Tsaya kiji mana" ya fada kanshi a kasa,
" meyasa baki tambaye ni KO wace yarinya ce nakeso da yawa haka ba?,

Bansan lokacin da nasamu bakina da cewa,
" saninta bahida amfani a gare ni"
Na fada Ina duban shi,

" a'a muhibbat kada muyi haka dake ni inaso kisanta saboda ki taimakamin gurin neman soyayyarta coz har yanxun ma ita batama San inayi ba,"

Bansan ya akayi ba na tsince kaina da faduwar gaba ba kalaman shi sun bala'in dagamin hankali ba kamar da nagan shi ya mike ya matso daf Dani,

" plz muhibbat Dan Allah ki taimaka min ki taimaka min ki gayawa zuciyar ki cewa Farouq yana tsananin kaunarta wallahi muhibbat ina son ki  I don't know what to do I just can't live without you plz ki taimakamin don girman Allah,

Ni kam tun sanda yafara maganar shi nake kuka
" innillahi wa'innan ilaihirraji'un na fada tare da ja baya ganin yanda kamannin shi suka chanja baki daya,
" nashiga uku Dan Allah kayi hakuri kada kamin haka wayyo Allah na ni marainiya ce banida kowa banida komai,
Kukan yaci karfina sosai shiyasa na ruga da gudu nabude kofa nafita tamkar raina zaifita don kwata kwata bana ganin gaba na,

Su hajiya naci Karo dasu baki dayansu tambayata suke lafiya suna jijjigani cikin tsananin tashin hankali,



©Ayshart one©
08100376392
Www.ayshartfarouq.blogspot.com

Friday, 11 November 2016

Damuwata

55. Tana cewa kima tashi ki wuce yanxu nan tun
kafin zuciyata ta rufe na balaki don ganin ki ma
zai iya haifar min da Hawan jini Asabe tace ai ba
za ayi haka ba kidai barta ta Qara hutawa Ko
xuwa ayi la'asar ne sai mu hau hanya da kyar
inna wuro ta yarda mukayi la'asar Bayan mun
kare sallar ne ta jefomin wani album tsoho duk
ya lankwashe ya murde tana cewa ga tsiyar ki
nan danagani Cikin Kayan mahaifin ki a sauka lfy,
hannuna har ruwa yake na dauka nasaka a jakata
ba bata lokaci muka isa Tasha jikina kuwa yayi
xafi sosai dama tun gidan inna wuro nake jin
xaxxabi naso ya kamani ga Kaina tamkar ya
tsage saboda ciyon da yake mun Ita kanta
Asaben ta fuskanci haka don har maganin
xaxxabi ta saimin kafin motar mu ta tashi,
Wannan karon bacci bai daukeni ba idanuwa
kawai na xubawa hanya Ina kallon sarautar
ubangiji a raina kuwa sai tasbihi nake Ina bode
wa Allah da yabani sadakar rayuwa, sai a lokacin
na tuna album din da inna wuro ta bani nayi
saurin jawoshi Cikin jakata ina duddubawa
hotona ne da yawa aciki sai dai duk sun lalace
saboda ruwan da ya taba su hotona biyu ne
xuwa uku basu lalace ba na mahaifiyata Allah
sarki isma'il na fada ganin hoto biyu da nagani
Wanda Ada inada su don baxan taba manta
randa ya karbesu ba a cewar shi xaije asibitoci ya
bincika min mama na hoto daya Ita kadai ce tun
tana karama kafin tayi aure Dayan kuma itada
yayar ta ne shima suna qanana sai Dayan da
nagani ynxu Wanda suka dauka su da yawa da
alma duk familyn su ne,Allah sarki isma'il Ko
kana ina ynx? Wata zuciya tace Kila ma ya manta
da ke anya kuwa isma'il xai iya mantawa da ke
duk Irin hallacin da yamiki? Gaskiya bazai iya
mantawa dake ba Inji wata zuciyar Nima Kaina
nafi gasganta ta. Asabe ta katsemun tunani da
cewa toh sarkin tunani yau ba bacci ko jikin ne
kike ji na gyda Kaina alamar a'a taci gaba da
cewa ni dai muhhibbat ina baki shawara da ki
rage yawan tunani ki daina sanyawa kanki
damuwa sauki Yana tare da tsanani Mai hankuri
yakan cimma dadi Kowa kika gani duniyar nan
Akwai abunda ya dame Shi. Ni dai kallon Asabe
kawai nake ashe ta iya xantukka masu dadi haka
tayi ta yimin nasifa da bani shawarwari har bacci
ya kwasheta nikn wannan karon idanuwana biyu
har muka isa garin kaduna

56
Wannan Karon idanuwana biyu har muka isa
garin kaduna koda muka isa Anata kiraye kirayen
sallahr magriba taxi muka dauka har bakin gidan
ras! Naji gabana ya fadi sai nasame bakina da
karanta bismillahi harajna wa bismillahi
walajnawa ala llahi rabana tawakkalna.
Kasancewar Ana sallahr magriba ne yasanya
muka tsaya nan falon qasa muka gabatar da
sallolin mu har xuwa isha'i sannan muka doshe
head quarter hajiya
Xauna take tana kallon news fadeela na
kishingide tana dannar waya mukayi sallama
muka shiga dakyar ta iya buda baki ta amsa
sallamar dukkan mu xubewa mukayi muka
kwashe gaisuwa,
Ta tabe baki ta dube asabe tana cewa ''ai na
dauka ba xakixo ''
Asabe ta washe baki
" ni as wa da baxan dawo ba mota ce dai tayi
wuya,"
Takai dubanta gareni " ke kawai sai kika gudu
bayan Kinsan nabiyaki kuddin ki nawata daya tun
wata na 15 baki Ida Aiken ki ba kika gudu Kinsan
idan naso kamaki da wannan laifin xan iya ko."
Gyada kaina kawai nayi tare da cewa
"ayi hkr kuskure ne,"
Ta yatsine fuska taci gaba da kallon ta batare da
tace komai ba,
Asabe tace " dan Allah hajiya kiyi Hakuri da duk
abunda Ya faru mahaifiyar ta tayi bakin ciki
matuka da komawara ta gida batare da sanin ki
ba, da tarema xamuxo tabaki Hakuri sai kuddin
motar suka kakare mana amma tace dan Allah
kiyi Hakuri ki karbe muhibbat kuma kimata duk
hukuncin da kikaga yadace da ita amma dan
Allah kada ki kureta daga gidan nan domin ke
kadaice gatan su,"
Idanuwa kawai naxubawa asabe Tana shatata
qarya cikin Raina cewa nake wasu mutane basa
tsoron Allah ji yanda asabe ke karaya Bako
tsoron Allah saboda Neman duniyanan
57
Hajiya kam maganar ta mata dadi ta qara
tabbatar da yarinyar ba Iowan kowa ba ce, amma
a zahiri sai Tamara bata fuska tare da cewa
" Ai ni tune na Hakura da muhibbat tunda ba ita
kadai ke iya kulamin da gida na ba don hk ki
dauke ta kawai ki koma da ita nagode"
Wani irin dadi naji hade da sanyi cikin Raina .

57
Hajiya kam maganar ta mata dadi ta qara
tabbatar da yarinyar ba Iowan kowa ba ce, amma
a zahiri sai Tamara bata fuska tare da cewa
" Ai ni tune na Hakura da muhibbat tunda ba ita
kadai ke iya kulamin da gida na ba don hk ki
dauke ta kawai ki koma da ita nagode"
Wani irin dadi naji hade da sanyi cikin Raina .
Asabe ta qara kekashe Murya tare da qara
kaskantar da Kai tanaba hajiya hakuri kan tabrni
inci gaba da aikina,
Rokon Allah nake tayi Allah yasa kada ta Hakura,
Muryarta na tsinkayo tana cewa,
"Toh shi kenan na Hakura amma da sharadin duk
ta sake aikata laifi makamancin wannan xatabar
gidan nan har abada,
Wannan shi ake Kira da adake ka a hanaka kuka
bansan lokacin da hawaye masu xafi suka
xubomin ba Jin wannan maganar ta hajiya take
sai naji hankalina Ya sake tashi ganin nusaiba ta
shigo harda takemun kafa tana cewa,
"Momy Biko kikayi ashe?,"
Fadeela ta karbe da cewa ,
"Ai Kinsan momy bata iya xama sai da wannan
aljanar,"
Duk suka sanya dariya suka taba,
Saida ta sake gindaymin dokokin gidan da
sababbin yan aikin da suka samu sannan sukayi
sallama da asabe ta wuce gidan da take xama.
Haka rayuwa taci gaba da kasancewa cikin
wahala da tsangwamar hajiya da yaranta Yau
Kusan satania biyu da dawowa gidan amma ban
sanya Farouk a Ido na ba hakan ba karamin dadi
yayi mun.
Kasancewar Yau asabar misalin karfe 9 na safe,
sanye nake da wani material da anty hajara ta
dunkamin blue mai ratsen fari dunkin Riga da
sikert Kayan na matukar karbata ko ba komai
xamana gurinta na samu wata wayewa ta daban
jikina kanshi Ya chanja saboda mayukkan da
tasaimin har ynx inada Sauran su, su nake
shafawa karamin hijabi fari na sanya inata
kokarin hada breakfast kan dinning hajiya da su
fadeela duk suna xaune suna Fira ,
Cikin nutsuwa nake jido kaya daga kitchen xuwa
dinning area,
Fadeela ta dube nusaiba tace,
" dadina da talaka bai iya samun guri ba"
Cikin dariya nusaiba tace,
" au dama sai ynx kika sani.,"
"Toh naga aljanar yarinyar ga duk ta chanja ni
fah abun har tsoro Yake bani sai wani fresh take"
" tunda ta dawo na lura da haka har maganar
naso na miki sai kuma na manta,"
" ai kuma kunsan daganin hk ba banxaba don
asabe ta cemun da tabar gidan nan ba gida taje
ba saida suka tsananta addu'a da rokon Allah
sannan ta koma gida, mudai Allah yasa ba a debo
muna mugun Abu ba " inji momy,
Duk suka karba da ameen,
Shigowar Farouk ce falon ta katse firar,
Gabana yayi mummunan faduwa lokacin da muka
hada Ido da Farouk,
Shi kanshi ba karamar rudewa yayi ba da kyar
ma ya iya hada kalmar,
" momy Ina kwana"
Cikin fari'a ta karba yayin da su fadeela suka
gaishe shi suma cikin girmamawa ,
Baimaji gaisuwar suba saboda kwata kwata
hankalin shi baya gurin su har saida suka sake
maimaitawa,
Ni kan tune na dauke idanuwa na naci gaba da
xuxxuba musu abincin ,
Farouk kasa Hakura yayi saida yayi magana,
" momy yaushe kika dawo da yarinyar nan ne"
" Kusan satin ta biyu " ta bashi amsa ,
Baki daya kasa cin abincin yayi sai satar kallo na
Yake,
"Momy tace,
"Lafiyar ka Kuwa katasa abinci gaba kana kallo?",
Mikewa kawai yayi tare da cewa,
"Banjin dadin jikina ne,
"Eyya inji ba xaxxabin ba ne?"
" no kaina ne kawai ke ciyo xanje asibiti ynx ba
dadewa xanyiba ynx xandwo Sai inci abincin"
" da ka daure kaci ko kadan ne sai kasha
magani"
"Xan sha tea idan naje daki",
Har ya juya kuma sai ya dawo yace,
Idan yarinyar nan ladidi taxo kisa ta gyaramin
kayana da aka kawomin jiya suna falo waste,"
Ta karba da cewa,
"Ai na maidata gida jiya, ga dai muhibbat nan
idan ta qare aiki xata gyarama, baice komaiba Ya
haura sama a abinshi amma yaji dadi har cikin
xuciyar shi,
Wuraren qarfe goma na kammala ayukkan hajiya
ta sake nanatamin inje ingyarawa Farouk dakin
shi,
Ba tare da bata lokaci ba na nufe dakin shi
gabana sai dukan uku uku Yake......................,

58
Da sallama nashiga dakin ba kowa sai sanyi a.c
da daddadan kamshin turaren dake tashi a ciki
komai tsare very neat,
cikin raina nace har ynx wannan tsaftar tananan
ba tare da bata lokaci ba nashiga bedroom dinshi
nan ma komai a tsare,
kayan ne kawai da ya karbo gurin wanki cikin
katuwar jaka zube kan gado,
sai drowar dake bude wadda da alama yana cikin
aikin jera kayan ne ya ajiye ya fita.
batare da fargabar komai ba na shiga zazzage
kayan ina jerawa a cikin drower din,
kaman yawa ne dasu shi yasa na dauki tsawon
lokaci kafin in kare,
bayan naqare Ina cikin gyran gado naji anbude
kofa anshigo ansake yiwa kofar key anyi locking
dinta,
a razane na juyo don ganin kowaye ko ban fada
ba nasan ko waye idanuwan na da nashi suka
sarke guri daya,
nayi sahrin saukar da idanuwa na kasa tare da
maida hnkali na kan gyaran gadon da nake
shi bai shigiba kuma baiyi magana ba hannayen
shi kawai ya harde a kirjin shi ya zubamin
matsakaitan idanuwan shi masu tafiyar da
nutsuwar mutum,
kasa juyawa nasakeyi badon ban qare gyaran
gadon ba sai don gudun sake hada idanuwa da
farouq,
ganin bashida niyar barin gurin yasa na juyo tare
da sunkuyar da kaina a kasa,
cikin raunanniyar murya nace,
" Ina kwana"
bai amsaba saima sakin kofar da yayi ya nufato
inda nake,
nan take jikina ya hau rawa na runtse idanuwana
tare da make hannayena a kirjina,
saida ya kawo daf dani yazamana har Ina iya jin
nunfashin sa da bugun zuciyar shi,
cikin muryarshi Mai dadin sauraro yace,
" bazan karba gaisuwar ki ba muhibbat"
idanuwana sukayi raurau tamakar Mai shirin
fashewa da kuka,
a hnkali nayi saurin durqushewa a qasa Ina
maida nunfashi Allah ne kadai yasan abunda
zuciyata take saqamin,
biyoni yayi a qasa shima tare da kiran suna na "
muhibbat"
wani yar naji a jikina saboda yanda yafadi sunan
sai naji kaman duk duniya yafi kowa iya fadin
suna na,
" muhibbat"
yasake cewa a karo na 2,
hawayen da naketa maqalewa suka zubomin,
" oh my god"
ya fada
" baba muhibbat meyasa zakiyimin haka meyasa
zakimin kuka a lokacin da nake muradin ganin
murmushin ki me yasa kika boyemin kanki a
lokacin da nake buqatar ganin ki muhibbat me
yasa kikaqi zuwa ki taimakamin a lokacin da
nake neman taimakon ki?"
kaina ya daure narasa gane me kalaman farouq
suke nufi,
tausayin kaina ya kamani take na sake fashewa
DA kuka tare da cewa,
" don girman Allah farouq ka budemin kofa in fita
"
mikewa kawai yayi tare da komawa kan gado ya
zauna baki daya tunanin shi yatafi wata duniya ta
daban wadda bata mutane ba,
wata rayuwa yake hangowa mafi dadi DA tsanani
a cikin rayuwar duniya
lumshe ido kawai yayi yanajin wani Abu nabin
jikin shi yana ratsawa.
bugun kofar da ake ne ya dawo dasu cikin
duniyar tunanin da suke dukkan su .

Damuwata

By
Ayshart farouq

59

Bugun kofar da ake ne yadawo dasu daga tunanin da suke dukan su,

Da sauri na kalle farouk wanda shima ni yake kallo,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na fada a cikin raina,
Iskoni dakin bashine tashin hankalina ba rufe kofar da akayi ne yafi dagamin hankali tabbas ko waye yaxo yaganni ynda na shiga shock dole yayi zargin wani Abu shin miye ma dalilin rufe kofar?
Bankai ga qare tunani ba naji hajiyo muryar hajiya na fadin,
" shin ko wanka kake ne?
Meye ma abun rufe kofa kana cikin gida.?"

Saboda tsabgegen tsoro har bansan lokacin da wani dan guntun fitsari ya fito
min ba ,

"Na shiga uku farouq ya zanyi"
Na fada Ina duban shi,

Dan murmushi yayi tare da nunamin drower alamar in boye a ciki,

Da gudu natashi nashige cikin drowar har Ina buge kaina da kofa.

Shi kuwa farouk tashi yayi yaje ya bude kofar tare da cewa,
" yi hakuri mom Ina toilet ne,
" dama nayi tunanin haka"
ta fada tana kunno kanta a cikin dakin

Bai hanata ba shima ya koma ya zauna yan facing dinta,

Ganin yanda ta shigo ya tabbatar mishi da akwai magana a tattare da ita.

Wani kallo tayi Mai cikin tuhuma,
" me yasa kayi locking din kofar dakin ka alhali kana ciki,?

Cikin fargaba ya dubeta
" which kind of questions is dis mom?

Hararar shi Tayi sannan taci gaba da cewa,
"  dakata farouq hala kana tunanin duk abunda kake ciki ban sani ba ne? Ko  a tunanin ka zaka iya yimin wayo ne?
Toh Bari kaji duk wani Abu da kake boyewa  ina sane dashi don kajiya,

Nida nake cikin drower sai hada gumi nake hanjin cikina tuni suka koka,
"Shi kenan ni muhibbat karyata ta qare"
Na fada cikin raina,

Shi kanshi farouq din ba qaramar firgita yayiba da jin kalaman mahaifiyar tashi,
Dakewa kawai yayi yasamu ya hada waddan kalmomi,
"Kamar ya mom?
Ya fada yana shafe xufar da yake karyomishi,

" ai yanxun haka xakace bakasan abunda nake nufi ba toh Bari kaji wallahi kayi kadan ka jamin abun kunya dama abunda fadeela ta gayamin gaskiya ne rufe kofarka kakeyi kace kada ta dameka ai ynx sai kafito kacemin ita kake rufewa kofa tunda bakasan halacci ba,
Toh wlh aure kaida fadeela ba fashi kaman anyi shi ne angama,"

Wani malalacin murmushi farouq yayi gami da sauke wata irin ajiyar zuciya ganin abunda take magana daban da wanda yake tunani,
",haba mom taya Zan rufe kofa saboda fadeela KO ba komai ai kanwata ce,
How can i do dis to her,plz mom ki daina daukan maganar yarinyar qarya tamata yawa wlh,
Kofata fa idan akaja ko ba ayi locking ba sai Tayi locking da kanta"

" toh nidai nagaya maka ka maida hankali Ku fuskanci juna

           
              60
Kana ganin ga dan uwankanan ya saki jiki da kanwar ka sun fahimce juna
Yanxun ma nasan don yayi tafiya ne da ba don hk ba da yanxu yana gidan nan"

"Ayi hakuri mom nima xan gyara insha allahu"
Maganar ma yinta dai ne yayi don ya matsu ta kammala maganar ta fita,
Duk hankalin shi na Chan gun muhibbat

" wai me kake tunani ne?
Ta  tambaya tana kallon shi,

"Ba komai mom am just exhausted,"
I need to rest kinsan ban Dade da dawowa ba,"

"Toh koma dai miye xuwa anjima ka kirata kuyi magana hankalinta ya kwanta itama,

" insha allahu mom Zamuyi magana kar kidamu,

" yauwa ko kaifah haka nake so naji,
Jiya muka qare magana da dadyn ku Za'a sanya ranar auren Ku da hajiya safiya ta dawo egypt,"

"Allah yadawo DA ita lafiya"
Ya fada cikin kotsawa,

" Kai ni motsi nakeji a Chan ta fada tare da mikewa tsaye tana nuna gurin da "muhibbat take labe,
Shima farouq mikewa yayi yana cewa ba komai may be labule na da fanka ke hurawa"

Ni kuwa fitsarin da nake rikewa ban San lokacin da yafito ba saboda bala'i,
Duk ilahirin jikina rawa yake nakasa ko kwakkwaran nunmfashi don kar taji,

kallon farouq  kawai tayi tare da tabe baki tanaci gaba da jaddada mishi maganar fadeela,
Shi dai sai eh yake cewa,
Har kofar waje yakaita sannan yadawo yana ajiyar zuciya,

Inajin lokacin da farouq yazo ya bude min yana cewa fito muhibbat ta fita

Ai Ina fitowa ban ko kalle shi ba nayi hanyar waje da gudu
Inaji yana kwalan Kira amma Ina bazan iya tsayawa ba,

Allah ya taimake ni koda na sauka banci karo da kowa ba har na Kai dakina na zube kan katifa Ina maidani numfashi.



Ayshart farouq




©ayshart one©

Damuwata

[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪
          001
Gudu nake  ba ko kyaukyautawa har sai da na kawo bakin wani dutsen da ya zame min tamkar cinyar mahaifiya ta da nake kwanciya nayi kuka a duk lokacin da na tsince kaina cikin kewa ko wani tashin hnkl da tsananin rayuwa,
   Kuka nake sosai tamkar raina  zai fita.
" wannan wace irin rayuwa ce ?
Yaushe zanyi farin ciki a rayuwa ta?
ni muhibbat yaushe zan daina zubar hawaye?
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na fada lokaci daya tare da kife kaina a guiwa  nayi kuka har na godewa ubangiji na,
Lokaci daya na tuna da mahaifi na Wanda shi kadai ne gatana na fada ckn raina
"Allah sarki baba Allah ya jiqan ka yasa ka huta"
take na tuna irin rayuwar quncin da nayi da mahaifi na kafin Allah ya dauke ranshi,

Ni muhibbat Yar asalin hukumar dawakin tofa ce dake a jahar kanon dabo karamar hukuma ce da Suka shahara da sana'ar zuma,
Na fito daga Hausa Fulani mahaifi na bahaushe ne yayin da mahaifiya ta take bafulata na.
Mahaifina mal usman ya hadu da mahaifiya ta fateema wadda yar asalin bauchi ce sun hadu ta dalilin sana'ar zumar shi da take kaishi garuruwa da dama,
Mahaifina yanada mata 2 Matar shi ta farko masifaffiyar mata ce ta qarshe inna wuro tana da 'ya'ya biyu mata Jamila da adawuya  bata bari ya zauna da kowace macce,
yayyi aure yakai Hudu amma ba wadda zata kai shekara daya bata fita ba sbd bala'i da asirin inna wuro,
Mahaifiya ta Fadima ita kadai ce maccen da tajima har ma aka samo rabon ciki,
Hnkln inna wuro yayi matuqar tashi ganin mahaifiya ta da ck ba ta ida   rudewa ba sai da taga ta haife Dan ta namiji ina wuro tashiga yin asiri har taga baya ga yaro ranar suna yaro yace ga garin Ku
Mahaifina yayi maruqar baqin ciki domin a rayuwar shi yana son da namiji.
Anyi hk ba afi shekara ba mahaifiya ta ta sake samun ciki wannan karon inna wuro tayi tayi tazubar da ckin Allah bai nufa ba,
Lkcn da aka haife ni mahaifiyata tashiga wani matsanan cin hali na yau ciyo gobe lfy ga baqar wahalar da inna wuro ke bata yan uwan ta sunzo sunyi sunyi suje da ita mahaifina ya hana dole Suka hkr Suka barta.
Lkcn da na cika shekara biyu lkcn mahaifiya ta ta tashi da wani irin ciyon hauka Wanda duk Wanda ya ganta dole ya tausaya mata sbd halin da take ciki.
Ana cikin hk kwatsam aka tashi aka neme mahaifiya ta aka rasa ta,
Anyi nema har angaji ba' a ganta ba,

Ayshart farouq
📚✏Excellent writers 1⃣✏📚
              
             002
Tun lkcn nake ganin azaba gurin ina wuro mahaifina baya iya cewa komai  ana ckin hk muka koma cikin garin kano da zama sanadiyar   aikin da mahaifina ya samu lkcn da nakai five yrs lkcn  aka Sani prmry skul ko shima dakyar inna wuro ta bari naje
Ganin wahala na nema ta kashe ne ya sanya mahaifina ya kaini boding skul.
Lkcn da na shiga ss1 ne Allah yayiwa mahaifina rasuwa ta sanadiyar ciyon zuciya  tun daga lkcn na daina zuwa mkrn ta na zauna nan gun ina wuro ina ganin azaba yan uwan mahaifina basa iya cewa komai sbd baqin bala'in inna wuro.

Bankai ga qare tunani ba naji andafa ni ana cewa
" haba muhibbat me yasa bazaki daina sa kanki cikin irin wannan damuwar ba?"
idanuwa na jajir na juya na dube shi na ce,
" isma'il yaushe kazo?"
Cikin  tausayawa ya ce,
Ngan ki kinata gudu ne shiyasa na biyo bayan ki nasan nan zaki zo"
Nayi ajiyar zuciya tare da shafe kwalar da ta zubo min na ce,
" kafi kowa sanin DAMUWA TA shi yasa kasan gurin da nake zama a duk lkcn da nake nuqatar isashen tunani"
Yayi murmushi ya ce,
" muhibbat kenan ki kwantar da hnkln ki insha allahu damuwar ki ta kusan zuwa qarshe haqiqa nasan mahaifiyar ki ita ce damuwar ki kuma insha allahu matuqar ina tare da ke zaki samu lbrn mahifiyar ki matuqar tana raye.
Nayi matuqar jin dadin kalaman isma'il shi yasa ko yaushe nake qara kaunar shi,
Nan Isma'il yayita kwantar min hnkl da kalamai masu dadi har maraice ta gabato sannan  nabar wannan dutsen da ke kusa da gidan Mu saida isma'il
Yakaini har bakin gd sannan yawuce gdn su.
          
Ayshart farouq
✏📚Excellent writers1⃣✏📚

           003
Sadaf sadaf nashiga gdn don kada inna wuro taji motsina  cen naji ance toh munafukar Allah jinin hauka mai siffar barayi  Ai na dauka bazaki dawo ba,
Maxa kizo ki wanke mun kaya na kuma ki dama min kullun waina ta ko ni kike so nazo nayi miki wannan aikin
Cikin inda inda  jkna duk ya dau rawa na karba da 
"  toh inna"
Sallaar magariba kawai nayi nashiga aikin da inna wuro ta Sani bani nagama ba sai wuraren shabiyun dare sannan na kwanta duk ilahirin jkina sai ciyo yake dama idan da sabo na saba

Ayshart farouq

📚✏Excellent writers1⃣✏📚
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪
       
            O04
Yau ma kaman kullum tun da asalatun farin na tashi nayi shara nayi wankin kwanukka sannan naje na debo ruwa saida na kammala duk aikin gdn sannan nafita waje inda inna wuro ke toya wainar da take saidawa na kama mata mukaci gaba da toyawa,
Bamu muka tashi ba sai wuraren qarfe daya hk nake cin aiki ko yaushe kamar wata jaka ga diyan inna wuro ko wace sai dai taci tayi wanka taci ado a fita.

Inna zaune ina tuqa tuwo Jamila da Adawuiya sai zagina suke akan naqi saurin qare musu abinci,
Yaro yashigo yace,
" wai ana sallama da muhibbat a waje"
Inna wuro tayi karaf ta fito daki ta  karbe da cewa
" ko dai Jamila aka ce?"
Yace "a'a muhibbat dai aka ce"
Inna wuro tace,
"Karya kake yi koma dai kasake tambayawa"

Ya sake dawowa yace,
"Ance muhibbat"
Inna wuro tace,
"Jamila tashi kije kiga ko waye domin na tabbatar da ba gurin wannan diyar mahaukaciyar aka zo ba"
Jamila tamiqe tana tafe tana rangwada.
da Gudu ta dawo tana fadin wlh inna dagaske ne gurin ta aka zo kuma inna Baki ganshi ba da zungureriyar mota Dan gdn fah Alh, sale mai dukiya ne"
      

        
            005
Inna wuro tayi taslima  ta ce,
" dama naga shishigin shi yayi yawa ko yaushe yana laqe wurin sayen waina Ai wlh sai dai idan bana nunfashi
Wannan baqar mayya ai sai dai ke Jamila ko Adawuiya ba dai wannan baqar kaskar ba "
Jamila ta turo baki tana cewa
" inna kije kawai ki gaya mishi kada yasake zuwa gurin ta inna wlh Baki ganshi ba dama ni ina son shi wlh"
Inna wuro ta ride mayafi ta fita tana masifa.
Ni dama nasan hk zata faru shi yasa tun farko naqi bashi goyon bayan zuwa guri na,
Duk jikina ya mutu sbd bansan irin wulaqancin da inna wuro xata mishi ba,
Tana dawowa ko ta hauni da zagi itada 'ya'yan ta
Adawuiya ta ce,
" wlh  wannan yarinyar ji nake tamkar in kashe ta jiya fah baki gani yanda maniru ke kallon ta ba ita kuma harda qara wata karairaya tana yauqi tamkar bata so ta taka qasa,
Inna wuro takaimin naushi tana cewa Ai indai wannan ce tafi da hk duk kissar uwarta ce ta kwaso to wlh ta Allah ba taki ba diyar mahaukacciya
Wannan kalmar tafi ko wace kalma baqan ta mun rai .
Hk su inna wuro sukayi ta cimin zarafi ina kuka uffan bance musu ba sai da Suka gaji Suka bari don Kansu.

Ayshart farouq
📚✏Excellent writers1⃣✏📚

          006
Ina tsakar gida ina surfe,
Adawuiya zaune tana yankan farce yayin da inna wuro ke qoqarin nasa dawo a tukunya.
" gafaran Ku dai" akayi sallama daga waje,
Na karba sallamar tare da ci gb da aikina
Inna wuro ta dago kai tana cewa wa nake ji hk kamar Asabe?"
" ni ce wlh cikin ranar nan"
"Toh maraba shigo zauna ga yabarma nan" inji inna wuro
Kan wata busasshiyar tabarmaar kaba Suka zauna.
Bayan sun gama gaisawa ne Asabe ta dube inna wuro duba irin na Matar da akace mijin ta zai sake Sabin aure
Ta ce,
"Nazo ne kan maganar nan da mukayi da ke ta zuwan  muhibbat aikatau domin Matar ta matsa asamo mata Yar aikin,
Domin gdn da muhibbat  zatayi aikin gd ne bana wasa ba...........
 

Ayshart farouq
📚✏Excellent writers1⃣✏📚
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪
            
             007

Inna wuro ta katse ta da cewa
" toh ai ni kinga abunda bana so saboda bana qaunar wannan yarinyar da qaruwa ko kadan"
Asabe ta dube ta tace,
" ina fah qaruwa ciki tunda duk abunda aka bata ke zaki dauka  don ina mai tabbata miki kuddin da za'a bata bazaki taba samun su a wainar da kike ba bari ki gani ma" tasanya hannu cikin Yar jakarta ta fito da damen kuddi ta miqawa inna wuro inna wuro duk ta rude ganin kuddi har 50k
Ta ce,
" wadannan name ne ?"
Asabe tayi dariya tace,
"Sune kuddin da za'a dauke yarinya"
Inna wuro tace ,
" kina nufin duk wata su za'a riqa bani?"
Asabe tace,
"Eh mana amma ni xan dauke ashirin in Baki talatin domin abunda yasa ma nazo nace da muhibbat din zamu sbd naji qishin qishin cewa sama'ilan kidan mai dukiya yana son ta,
Na tabbatar da ko idan har ya aure muhibbat to duk shirin ki zai roshe amma ynx idan har naje da ita kinga bai ganta ba ballantana yace zai aure ta ko ya kika gani wuro?"
Inna wuro tayi ajiyar zuciya tace,
" ai ni har kin sa ma na amince ko dan wannan sama'ilan da naga yana so yakawo min  cikas a cikin shiri
na,
kinga idan ma kikaje da ita sai inyi kokarin hadashi da jamila ko ya kika gani?"

Asabe tace,
" ai dama shi nake so ki fahimta"
Sukayi shewa Suka lale,
Inna wuro tace ,
" shin ina ma ne kikace?"
Asabe tace,
" kaduna mana inda nake aiki Ai matar abukiyar uwargijiya ta ce"
" toh yaushe ne tafiyar? Wuro ta tambaya
" ina ga sai nan da kwana 2 " Asabe ta bata amsa
" toh Allah ya kaimu "
Ta karba da
" Ameen"
Tayi sallama da ita tawuce Abun ta.

Ayshart farouq

📚✏Excellent writers1⃣✏📚

          008

Asabe kanwa ce gun inna wuro uwar su daya,
sai dai ita ba irin inna wuro bace domin ita ta nada Dan tausayi sai dai shegen son abin duniya da ya mata yawa bata taba raina hanyar samu duk yanda take,
bata taba haihuwa ba tunda mijin ta ya rasu ta same aikatau wani gida a kaduna da alama tana jin dadin aikin shiyasa batada wata Matsala duk qarshen wata ta kanje dawakin tofa  gurin mahaifiyar ta da kuma kano gurin yayar ta wuro.

Yammacin yau ne natafi bakin dutsen da nake zama a hnkl na shiga rera kuka maicin rai zuciyata tamkar ta fashe saboda baqin ciki kuka nake tun sautin kuka na nafita har yadaina fita,
DAMUWA TA daya ce ynx shikenan banida hope din ganin mahaifiya ta shikenan hk ni zanyi rayuwa ta har abada a cikin qunci INNLILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJ'UN na fada a bayya ne wasu hawaye masu zafi Suka shiga kwararomin,
A hnkl naji andafa kafada ta na juyo mukayi four eyes da isma'il
Ckn tashin hnkl yace,
" muhibbat me yafaru?
Me yasa kike irin wannan kukan?"
Sake fashewa nayi da kuka cikin raina ina cewa ai baima dace isma'il yayimin wannan tmbyr ba...
Ya katse ni da cewa
" kiyi hkr muhibbat hakika komai yayi zafi maganin shi Allah nasan irin baqin cikin da kike ciki, muhibbat bana son wannan zubar hawayen naki ",

Na dago idanuwa na da sukayi jawur na ce,
" isma'il dole ne nayi kuka dole nazubar da hawaye saboda banida gata,
Isma'il banida gata ni muhibbat banida gata banida uwa banida uba Allah kadai ne gata na kuma dashi na dogara
Ya Allah kafitar dani wannan halin ka sanya DAMUWA TA  ta zamo qarshe ya Allah,
Na sake fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Ayshart farouq

📚✏exellent writers1⃣✏📚

               009
  Hankalin isma'il ya tashi matuqa ganin halin da nake  ciki yarasa abunda ke masa dadi ya gurfana gabana yana facing dina yace,
"Muhibbat kidaure Dan Allah kici gaba da hakuri don't give up insha allahu na miki alkawarin cikin satin nan zanjewa iyaye na da mgnr ki a Kaduna nasan zasu fahimce ni muhibbat zakiyi farin ciki zakiyi rayuwa maidadi kamar kowa insha allahu nine zan zamo silar farin cikin ki  bazaki sake damuwa ba har abada.

Jin kalaman isma' il ne yasa na qara tsananta kuka namiqe tsaye ina cewa
"  wannan duk a cikin mafalki ne isma'il mafalkin da nake fatar ya zamo gaky,
Amma kash! Inaga wannan mafalkin bazai zamo gsky ba har abada saboda  nariga  nasan hk zan mutu a cikin wannan rayuwa ta qunci da baqin ciki isma'il nagode kwarai da abunda kayi min Allah yasaka ma da alkhairi bazan taba manta ka ba a rayuwa isma'il inama ka ban kwana gobe zanbar garinnan zuwa wani gari da bansan ko wane gari ba ne aikatau ina roqon Allah da yasake sadamu da alkhairi sai wata rana,"
Ina qare fadin wannan mgn na wuce da Gudu ina kuka.

Ayshart farouq

📚✏excellent writers1⃣✏📚
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

            10
Isma'il da ke zaune duk ilahirin jikin shi yayi sanyi hnklin shi ya tashi matuqa don jin kalaman muhibbat,
Ya fada a fili "AIKATAU a wani gari impossible bazan bar hibbah na taje ko ina ba ina tare da ke muhhibbat nine zankawo qarshen damuwar ki muhhibbat zan taimaka miki infitar da ke wannan quncin I must do something about dis"
shi kadai yake mgnr shi kamar wani zararre,
Miqewa  yayi daga inda yake zaune jikin shi duk ya sake idanuwan shi jajur kamar garwashi da qyar yake tafiya don har wani jiri ke diban shi,
Dakyar ya samu ya isa gd.

Wanene isma'il
Isma'il jika ne gun Alh sale maidukiya ta gefen mahaifiyar shi Hajiya Safiyya  mahaifin shi mashahurin mai kuddi ne Alh Usman waziri Ala   shi ainihin dan kaduna ne auren zumunta ne akayi tsakanin mahaifin shi da mahaifiyar shi sbda zuri'ar su sun fi auren dangi  tsakani su  alhaji usman Ala yanada mata biyu hajiya Safiyya da Hajiya Zara'u hjy Safiyya tabar gdn shi sbd yan wasu matsaloli yayin da ya dauke Matar shi Zara'u yayi kasashen waje da ita saboda ganin dangin shi basa kaunar ta acewar su akan ta yake wulaqan ta yar uwar shi,
Lokaci lokaci yakan zo nan gdan shi na Kaduna da Matar shi hjy Zara sai dai ba wani dadewa yake ba ya koma bakin aikin shi a Europe.
ganin hkanan ya sanya isma'il ya koma hannun mahaifiyar shi yayin da kanwar shi fadila ke gurin kanwar mahaifin shi   wato Hajiya Ameenah.

  Isma'il ya hadu da muhibbat ne tun shekara biyu da Suka wuce gurin sana'ar ta ta waina kasancewa gdn su ba wani nisa ne sosai ba da gdnsu muhibbat kusan ma duk unguwa daya ce.
Isma'il mutum ne mai tsananin tausayi yana tausayawa muhibbat matuqa ganin irin wahalar da take wani lokaci idan yazo ya tarradda ita ita kadai tana toya waina sai ya saye duka yayi sadaka tun muhibbat na Dari dari dashi har ta sake jiki dashi ganin irin kyawawan halayen shi lokaci qanqane soyayya mai tsanani ta shiga tsakanin su.

Wannan shine taqaitaccen tarihin isma'il.

    Ayshart farouq
✏📚Excellent writers✏📚

            11
   
Lokacin da  na koma gd nayi sa'a ba kowa fadawa nayi daki kan keso ta nayi ta kuka har zazzabi ya rufe ni wani azabtaccen son isma'il ya taso min hakika ban san ina matukar kaunar  isma'il ba sai wannan ranar da naga za'a rabani dashi saboda son zuciya,

Isma'il na isa gida ya same mahaifiyar shi da maganar muhibbat take ta taka mishi birki da cewa,
" wannan mgnr kasan mgnr banza kake kafi kowa sanin cewa akwai maganar aure tsakanin ka  da Yar uwar ka Nusaiba kuma kasan baxamu taba bari ka aure bare ba domin nima auren bare ne ya rabani da ubanka don hk tashi ka bace mun da gani tun kafin raina ya baci"  
Shi sai lkcn ma ya tuna da wata Nusaiba innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ke tsakanin ya fada tare da dafe kai dakinshi ya nufa tare da zubewa kan gado shi kadai yasan yanda zuciyar shi ke mashi zafi saboda tsananin baqin ciki.

Tun da sanyin Safiya Asabe tazo dauka ta Hankali na yayi matuqar tashi shikenan ynx zan shiga wata rayu ta daban tare
da wasu mutane na daban,
shikenan nida Sama'ila har abada,
hk zanci gb da rayuwar kunci duk wannan alkawarin na isma'il ya zama na banza kenan Allah Sarki na fada cikin raina tare da tausayin rayuwar da zan shiga ina cikin wannan tunanen naji inna wuro tashigo dakin tana cewa
" dafatar dai kinshirya don ynxu xaku wuce ga Asabe nan tazo"

Ayshart farouq
✏📚Excellent writers1⃣✏📚

             12
A sanyaye na karba da
" eh na shirya"
Tace,
" toh ki fito kina batawa mutane lokaci kuma saura idan kinje kiyi abunda za'a Kore ki daga aikin,
Wlh kika kuskura kikayi laifin da za' a koro ki toh sai dai ki name wani gida cen ki zauna don idan kika kuskura kika tunkaro ni wlh sai na kusa kashe ki,"

Hnkl na ya tashi da jin kalaman inna wuro domin na tabbatar da inna wuro xata iya aikata abunda yafi hk.

Haka natafi cikin bakin ciki  da qunar rai,
natafi ina ta kukan rabuwa ta da mahaifa ta ynx shikenan ban da rabon ganin mahaifiya ta Kenan?,
Da wannan tunani Babar garin kano.

Ayshart farouq

✏📚Excellent writers1⃣✏📚
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

             13
Lokacin da muka hau titi ni tune bacci yayi awon gb dani,
Asabe tasa mata ido tana tunanin tabbas muhibbat zata kawo kuddi tunda tana da hakuri da kawaici gata bata da sanya idanuwa da abun wani, hakika irinta Hajiya keso saboda zata iya daukan wulaqancin Hajiya da yaranta saboda zama da Hajiya Ameenah sai Wanda ya shirya,

Ni dai bacci na kawai nake ban ma San me ake ciki ba sai da Asabe ta tada ni tana cewa toh bakauya ki tashi mun kawo,
Hakika bata fadi qarya ba domin ko a kanon da nake zaune  sunan ina ciki ne kawai amma ban taba zuwa ko wace unguwa ba idan ba tamu ba,
Wata zuciya tace,
To inama kika samu lkcn da zakije wata unguwa keda ko kawaye bakida,
Asabe ce ta katsemun tunani lokaci da take  cewa
" to sarkin tunani ai sai kishiga mota muje ko, sai lkcn naga Ashe har ta tsaida mai taxi,
drop muka dauka kasancewar  unguwar ba gurin shigar su ba ne,

 
Unguwar da muka shiga ita kanta unguwar Abun kallo ce  ko ba' a fada ba kasan unguwar masu hannu da shuni ce,
Bakin wani katafaren gida aka ajemu wanda ko a unguwar banga irinshi ba saboda tsananin kyaunshi da tsaruwar shi gidan  up chairs ne akwai sassa da dama a cikin gidan,
Lkcn da muka shiga gidan ai sakin Baki nayi gurin kallon qatoton prlourn gidan da alama ma aikatan gidan sun San Asabe saboda yanda suke ta gaisawa da ita,
cikin raina nace yau Allah ya kawoni to ko me zan taras oho?!'
Sama muka hau da alama nan dakin hajiyar yake,
Nan fa kallo ya koma sabo, knocking mukayi tare da yin sallama,
" waye" aka fada a cikin dakin,
" ni ce Asabe"  ta fada  tana washe Baki,
saida mukafi minti goma a tsaye sannan aka ce mushiga,

                 14
Harde take cikin daya daga cikin kujerun da da aka yiwa dakin ado dasu,
ga wasu hadaddin yan mata guda biyu da alama 'ya'yan ta ne saboda kamar su,
A hnkl na soma gaishe da Matar
Ciki ciki ta amsa tare da yamutse fuska,
Sannan Asabe ta gaida ta cikin washe Baki  tana cewa
"Hajiya gamu fah Allah ya kawo Mu,"
Ta dago ta kalle ni tace
" ko ban fada ba nasan  wannan itace yarinyar" Asabe ta karba da cewa " Eh itace ranki ya dade sunan ta muhibbat"
Daya daga cikin yan matan ta yatsine fuska tana cewa,
"  yau kuma da wannan Allah ya hadamu wai momy me yasa bakya gajiya da mana kwashe kwashe ne?
Dayar tace,
" ita take kwasowa kuma ita ake gumawa ballanta na ma wannan da ganin ta sai tayi Dan hali "
Hajiyar ta ce,
" to ai danku ake kawowa tunda Ku bakwa iya sawa bakwa fissuwa,?
Ta Dan yamutse fuska tadube Asabe  tace,
" wannan yarinyar fah ban yadda da ita ba saboda naga alamar tanada siffar munahukkai tamaida dubanta gurina tana cewa
"dafatar dai
Angaya miki irin aikin  da zakiyi?"
Gyada kaina nayi alamar
"eh"
sannan taci gaba da jadda da min dokokin gidan da kuma irin aikin da zanyi a gidan,
Na kula da gyara sashenta da na yaranta su ukku,
Sannan tasa aka kaini Dakin da zan zaunna,

Asabe bata jima ba tayi min sallama sai lokacin idanuwana Suka cika da kwalla
Asabe ta dube ni tace
" to muhibbat kukan me zakiyi kuma keda kika samu wannan Daula ai qara nan da inda kika fito cikin raina nace babu gwamma duk kanwar ja ce,
Taci gb dacewa kimaida hnkln ki kiyi duk abunda yakawo ki banda taba abunda ba'a Baki ba xan riqa xuwa  duk qarshen wata ina karbar kuddin,   cikin kuka na karba da
"toh sai kinxo"

Haka Asabe tayi sallama dani ta tafi tabarni da kewa.

Ayshart farouq

📚✏Excellent writers1⃣✏📚
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

             
              15
Wace ce Hajiya Amina?

Hajiya Ameenah mace ce maiji da sarauta ga kuddi ga ilimi Yar siyasa ce kusoshin gwamnati da ita ake damawa a ko ina,
mijin ta Alh  Abbakar sale maidukiya  shima mashahurin maikuddi ne Dan kasuwa ne kuma shima yana harakar siyasa shiyasa baima cika zama ba Shima auren zumun ta ne sukayi shida hjy Ameena kasancewar zuri'ar su shi suke yi, idan kagan shi gida toh iyakacin shi kwana daya ko biyu amma yanada wuya yayi sati daya cikin zuri'ar shi. Sunada Yara  guda biyu Umar Farouq da Nusaiba sai diyar yayan ta da take hannunta tun tana karama wato Fadila wadda kuma Alhj Abbakar sale maidukiya  yakasance Yaya ga mahaifiyarta Hj Safiya yayin da mahaifin ta Alh Usman Ala yake Yaya gun hjiya Amina shiyasa idan kaga fadeelah bazaka taba cewa ba diyar gidan bace saboda kamar su daya da yaran gidan,
Fadeelah tun tana karama take hannun su kasancewar mahifiyar ta bata tare da mahaifin ta,
Gidan Alh Abbakar da hjy Amina gida ne Wanda kowa kecin kashin kansa gida ne Wanda basa kaunar talaka ko kadan sbd acewar su talaka guba ne ko wace mai aiki Suka dauka ita ke guduwa da kanta sbd wulaqanci da tozarcin Rabi da yaranta mafi yawancin masu aikin basa guduwa sai sun Dan yaye wani Abu daga gidan kamar gwala gwallai, laptod, waya da sauran su shiyasa ko wace yarinya aka kawo suke daukan ta matsayin barauniya, 

Umar faruk shine babban dansu ya kammala medicine dinshi a Europ ynx hk yana aiki a wani asibitin mahaifin shi dake Kaduna,
Fadeela da Nusaiba ynx suna ug  2 a jami'a
Wannan kenan.
 

Ayshart farouq

             16
Sannu sannu  harna fara sabawa da Gidan hjy Ameenah saboda bana jin wuyan yin aiki duk yawan shi shiyasa wani lkc nakan ga qara ma zama gun inna wuro da zaman gidan Hajiya saboda su wulaqancin su banma San ko wane iri ba ne domin wani lkcn Abu suke tamkar ba musulmai ba don sau da yawa sukan kushe hijabin da nake sawa acewar su kazamai yan kauye kadai kesa dogon hijabi,
(Kuji fah).

Safiyar yau antashi da iska da wani matsanancin sanyi, tunda sassafe nayi  gyaran gida.
Ina kitchen ina hada break fast naji Hajiya na kwalamun kira,
Da sauri nazo na rusuna nace,
" Hajiya ina kwana"?
" lfy " ta karba tana yamutsar fuska sannan ta dora da cewa
" da fatar kin qare aikin da nasa ki?"
Nakar ba da
" eh"
Fadila ce ta fito cikin kayan bacci da alama ma ko salh batayi ba
Tana cewa,
" wai ina aljanar yarinuar nan?"
Nakarba da gani tunda dama nasan dani take,
Tace,
" ina kayan dana Baki ki wanke mun jiya?"
Nan take jikina yadau kyarma saboda tunowa danayi da rigar da tabani inwanke mata jiya,
Cikin rawar murya nace,
" Dan Allah fadila kiyi hkr wlh namanta, jiya koda kika ban Nusaiba tasani guga tohn..........
Kafin na ida mgnr tune fadila ta cukumo wuyana tana fadin
" wlh Baki Isa ba ya za' ayi inbaki wanki tunjiya kice mun wani Nusaiba ki kayima guga don ubanki ynx wane kaya kike so insa?"
Shiru nayi nakasa cewa komai jikina sai rawa yake sbd duniya naqi jinin naqi jinan ataba lafiyar jikina,
Fadila tasa kafa ta wutsikal dani
Tace,
" nabaki 10 minute kije kiyi duk ynda xakiyi inga rigata wankakkiya gogaggiya",
Loxl

Aushart farouq

     
           17

HK na tashi kwalla duk ta cikamin ido na mike ina shareware,
Hajiya
tace,
" idan kingama wanke mata kije dakin cen nasama ki gyara"
" toh"
nace tare da wucewa,

HK naje na wanke rigar cikin sanyin jikina sai makyarkyata yake nayita firfita rigar har ta tsane ruwan kasancewa rigar ba mai nauyi ba ce,
Cikin 30 minute na goge rigar na kaiwa fadila,

Dakin da Hajiya tace ingyara na nufa,

Chargy yayi halinshi rwly sowie frnds ba hk naso ba wlh

Ayshart farouq

excellent writers
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

             18
A hankali na tura kofar dakin  cikin sa'a kuwa ta bude saboda yau ne karo nafarko da zan shiga dakin sbd ko yaushe natura kofar dakin domin nagyara shi sai najita a kulle,
Cikin zumudi nashiga dakin,
sassanyar kamshin falon ne yadake hanci na saida na lumshe idanuwana a cikin raina ina cewa toh me zangyara a wannan falon? Domin kuwa falon a gyare yake ba inda datti yake saidai Dan abunda ba'a rasa ba,
Naqara gyara falon tsaf sannan na nufe uwar dakin,
a hnkl na tura kofar dakin itama direct nashiga dakin ba tare da fargabar komai ba saboda ni A TUNANi NA ba kowa a cikin dakin saboda ban taba ganin kowa yashiga dakin ba idan ba Hajiya ba ,
Ganin mutum kan gado zaune yasan ya duk na dabirce gabana sai dukan 3 3 yake yi, sanye yake da gajeren wando da singlet wankan tarwada ne kyakkyawa na ajin farko domin kaf gidan yafi su kyau duk da suma ba a baya ba,
Cikin rawar murya nayi sallama,
Bai karba ba kuma bai kalle ni ba ganin hk yasanya naja nayi tsaye tamkar dogarin sarki,
Uwar tsawar da yadaka mun ce tasanya hanjin ciki na kadawa tsoro yakama ni bansan lokacin da na nufe hanyar toilet din shi ba saboda tsananin rudewar da nayi,
Wata tsawar ya sake dakamin tare da cewa,
                   
                  19
" uwar me zakiyimun a toilet?,
Ke diyar gidan uban waye da zaki shigo min daki kai tsaye ba tare da kin nemi izini ba?
Cikin rawar murya nace,
Dan Allah kayi hkr wlh ban San da mutum a ciki ba,
Farouq yasake hasala
" ke kada ki fada min maganar banza ba mutum a ciki hala gurin zaman Aljannu ne,?
Ya nuna mun kofa tare da cewa" oya get out fitar mun daga dakin tun kafin inyi ball da ke wawuyar banza barauniya,
Haqiqa kalmarshi ta karshe ta dake zuciya ta,
Idanuwa na Suka cika da galla kafafuwa na basama iya dauka na saboda sunyi min nauyi,
Dakyar nake takawa Allah kadai ne yafitar da ni domin kwata kwata bana gani,
" wannan wane irin wulaqanci ne da yakai har a kirani da barauniya kalmar da itace kalma ta 2 da natsana a duniya," ina cikin wannan tunani ne naci karo da mutum

               20
Kafin in dago sai ji nayi an wutsilar dani,
Nusaiba ta soma fadin
" ture ni kike so kiyi ki karya ni Don uban ki bakya iya dubin gaban ki ne?,
" na dube ta a raunane nace
" kiyi hkr Dan Allah wallahi bangani ba ne,"
Taja tsaki
" ina ko zaki ganni mahaukaciyar banza Yar kauye,"
Xuciya ta tamkar ta fashe saboda bakin ciki,
Anya kuwa zan iya jure wannan wulaqancin kuwa ?,
Zuciya ta taraya min cewa ko nagudu nabar gidan take kuma na tuna da gargadin inna wuro lokaci daya zuciya ta ta cika da tsoro,
Haka na sauko kasa duk jikina a mace,
Hajiya ta dube ni a wulakance tace,
" ba dai har kin qare gyaran dakin ba?,
Nave,
" a'a yace nabarshi"
Fadila dake zaune tana shan tea tace ,
" ai dole yace tabar shi tunda yagan ta cikin wannan kazamtacciyar shigar..........."
Bata ida rufe Baki ba ya sauko
Cikn yamutsar fuska yace,
" Momy meyasa wai bazaki daina turamin yan aikin nan ba a daki,?
Kuma kinfi kowa sanin bana son yan aiki suna shgar min daki"
Hajiya tace,
" kayi hkr farouq Ai ban San kana ciki ba da ban tura ta duk dauka na night  duty kake yi"
Tsaki yayi tare da cewa dafatar ba abincin ta nake ci ba?,
Tayi murmushi tace
" Ai bana bari ta taba abincin ka"
Fadila da Nusaiba sai kume dariyar su suke domin sun San ba gsky ba ne,
Tsaki yayi ya haura sama abinshi,
Hajiya ta dube ni a wulaqance tace,
" don uban ki ba saida nace miki  ki riqa cire wannan mugun hijabin ba idan zakimun aiki"
Fadila tace,
" Ai dole ya faruk yaji kyan kyamin ta cikin wannan kayan"
Hajiya tace,
" wannan shine last warning duk lokacin da kika sake tabamun kaya da wannan hijabin sai naci ubanki a gidan nan banza Yar kauye bace mun da gani tun kafin in ballaki,
Sum sum nawuce idanuwa na cike da hawaye,
Gardiner gidan na nufa nashiga na zauna domin ynx ita tazame mun makwafin Dustin da nake zama lkcn da nake gun ina wuro,
ynx duk lokacin da naqare aiki na nan nake zuwa nayi zamana ina tunanin Rayuwar duniya........

Ayshart faroq

📚✏excellent writes1⃣📚✏
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

            21
Yau asabar misalin qarfe 10am sanye nake da hijab dina har qasa kasancewar ba kowa gidan,
ina cikin gugar tv naji motsi a bayana,
Faruk nagani cikin shigar shi ta kananan kaya ba karya kayan sun karbe shi nadube shi cikin faduwar gaba nace,
"Ina kwana?"
Ya dube ni sama da kasa batare da ya karba gaisuwa ta ba yace,
" tun yaushe momy ta fita?
" tun karfe bakwai ta fita tace ne tanada meting" nabashi amsa ina duban shi,
Ya dan yamutse fuska tare da jan tsaki yace,
Idan kin qare kije daki na akwai wasu kaya a jaka ki hada mun su cikin wardrof akwai wasu kuma kan kujeran falour ki dauka ki kaiwa maigadi,
Kuma shi kadai nasaki kada ki taba mun kaya don nasan dayawa masu aikin nan sata kawai kuke zuwa idan kika kuskura kika taba mun kaya naduba banga wani abu ba zaki san koni waye",
Kaina a sunkuye na karva da "toh"
Cikin raina nace,
Shi kuwa wannan haka salon wulaqancin nashi yake.
Ko yau ma dakin nashi a gyare yake kaman ko yaushe cikin raina nace,
Wannan mutum kan akwai tsafta don ko su fadeela da ar mata ko yaushe dakinsu yamutse suke fita su varshi sai bayin gidan su sun gyara musu,

               22
Tun lokacin faruk yakan dan sani gyaran daki kamar shara moping da sauran su sai dai bai taba cin abinci na ba ko yaushe hajiyar shi take dafa mishi abincin.

Wata rana ina wankin toilet din fadeela naga wani xube a qasa,
Daukan xoben nayi na ajiye kan madubi naci gaba da aiki nan can ko ya akayi hijabi na yaja zoben sai ganin shi kawai nasake yi aqasa saura qiris ma intaka shi, a hnkli nasake daukan xoben ina jujjuya shi hakika zoben ya hadu matuka domin ko shakka babu zoben gold ne,
Gudun kada nasake ajiye shi yafadi yabi ruwa  ya salwanta yasanya na sanya shi a yatsana da niyar idan na qare wankin toilet din na kaimata abunta
Lokacin da na kare sai kwata kwata Allah ya mantar dani naci gaba da ayukkan gaba na,

              23
Bayan kwana 2 ina sanye da wata kodaddiyar atamfa riga da zane da jamila ta qare yayi tabani dunkin fitet ne mai gajeren hannu ina sanye da katon hijabi na brown mai hannu kaman yanda nasaba
" muhibbat" !
Aka doko min kira daga palon kasa cikin sauri naqarasa cikin palon dukkan su suna zaune farouk yana karatun jarida yayin da su nusaiba keta firar su,
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

              23
Da sauri na qaraso na rusun nace gani,
Wata harara ce da hajiya ta doko min ne yasanya nagane nufin ta,
Mikewa kawai nayi na nufe kitchen  nacire hijab dina don gudun kada asamu matsala,
Sai kuma naji kunyar fita yanda nake saboda duniya natsane inriqa sakin jikina a ko ina sai na dauke  hajib na dan yafa shi a kafada na tamkar mayafi sannan nafara jidar lunch din ina kai musu,
Ganin yanda nayiwa hijab din ne yasan ya duk suka zubo min ido banda faruk dake zaune yanata karatun shi,
" Wai ke muhibbat hala da wanan hijab din aka haife ki ne?" Inji hajiya
Nusaiba ta tabe baki tace,
"Ai dama duk yanda akayi da jiki sai yaci kara ji fah duk irin gargadin da kika mata bataji ba"
Fadelah tayi karaf ta karbe da cewa,
" kin taba ganin talakan da bashida girman kai ai dan kauye girman kan tsiya ne dashi"
Wani kallo da naga fadeelaar namin ne yasanya naji gabana na faduwa,
Tace,
" ke zo nan"
Ras..! Gabana yasake faduwa na ajiye coolar da na dauko sannan na isa gurin ta nace, "gani",
Hannu na ta kamo tare da sakin kalima tana cewa,
" muhibbat ina kika samu wannan zoben?,
Momy ji zoben da nake ta nema hannun wannan yarinyar"
Sai a lokacin faruk yadago ya dubeni dukan su ma ni suke kallo suna taslima suna gunduma min zagi,
Hajiya tace,
" ta faru ta kare yarinya ta fara dauke dauke",
Take hankalina ya tashi jikina ya dau rawa nafara kuka ina cewa,
" wlh ba sace shi nayi ba tsintar shi nayi a toilet kuma da niy...."
Ban ida maganar ba ta buge mun baki tana fadin 
"karya kike wlh sace shi kikayi,"
Gaba dayan su suka hauni da duka da zagi,
Farouq ya daka musu tsawa da cewa,
" stop it meye hk kuke tamkar wasu dabbobi?,
dis is not fear"
Dukan su suka sake ni suka shiga taitayin su ni kuma ina gurfane a qasa inata rusar kuka,
Farouk ya juyo ya dube ni yace,
"tashi bar gurinnan"
Da gudu namike nayi cikin  Garden

              24
Hajiya ta dube faruk tace,
" meye hk ne faruk meyasa bazaka bari a hukunta ta ba?"
Faruk yace,
" luk momy ba hk ake hukunci ba,
Saboda idan har satan shi tayi bashi kadai zata dauka ba akwai tsarka dan kunne abun hannu dukan su sunfi zoben tsada kuma fadeela tace duk a tare suke idan har zata sata toh saida ta sace srqan gold din"
Nusaiba tace,
" ai bari da mutum kasani ko zoben ne yafi burge ta tunda yar kauye ce"
Tsawa yadaka mata
" yimin shiru  dake nake mgn ne da zaki sakamun baki?"
Allah yabaka hkr ta fada tare da hayewar ta sama,
Faruk yaci gaba dacewa
" mom da bakin ki kika cemun kinsha gwada yarinyar ta hanyoyi da dama amma baki taba kamata da laifin sata ba,
Ke kanki kinfi kowa sanin cewa fadeela careless ce, i am very sure misplacing din zoben tayi a wani guri,"
Fadeelah tace,
" haba ya faruk me yasa zakace hk? Wannan zoben yanada matuqar mihimmanci a gare ni tayaya zanrasa inda na ajiye shi wai kai me yake damunka ne akan wannan banzar yar kauyen kake daga sauti "
Ya dan yamutse fuska yace,
" i don' t care ko ma wace irice ni abunda nasani bazan taba goyon bayan rashin gaky ba,
Sau da yawa idan ankama wani yayi sata a gidannan a ka kuma bincika aka tabbatar da hakan ni nake korar shi da kaina amma ynx ta yaya ba tare da bincike ba zakiyi accusing din diyar mutane?"
Take gardama ta sarke tsakanin su,
Ran faruk yayi matukar baci yadaga hannu yace,
" wlh kika sake yimun musu saina mare ki ni warinki ne da ina mgn kinayi?"
Kuka ta fashe dashi ta haura sama cikin ranta tana cewa,
lallai yau sainaci uban muhibbat a gidannan tunda ita tajamin har ya faruq yaqi yarda da ni,"

               25
Hajiya ta dubeshi
tace
"toh me yayi zafi hk akan wata banzar yar kauye kake wannan ciccikan da har kake iqirarin zaka mare kanwar ka kuma yarinyar da muka zabarma a matsayin mata"
" Amma dai momy kinsan halin yarinyar shi doesn't have manners at ol" ya fada cikin facin rai
" ai hk zakace tunda kanajin haushinta to wlh  bari kaji kar kayadda nasake jin kwtan kwacin wannan mgnr ta fito bakin ka sbd idan Dadyn ka yaji sai yayi matukar bata ma rai,
idan har kana mata hk yaushe ne xaku fahimce juna?,
Maza ka tashi kaje ka lallashe kanwar ka,"
Faruk yarasa abunda zaice tsaki kawai yaja ya haye sama a xuciyar shi yana cewa  ba son fadeela ne banayi ba halayyar ta ne natsana buh very soon she will realize her mistake.

Ni kuwa  banma san wainar da ake toyawa ba tunda nafita direct Gardiner na nufa nasamu guri nazauna nakife kai a guiwa inata rusar kuka,
Nadaga hannayena sama ina cewa,
" ya ubangiji hakika kaine masanin abunda ke boye da bayyana ya ubaniji hakika DAMUWA TA jarabawa ce a garene ya ubangiji kabani hkr da juriyar wannan jarabawar kasanya inada rabon ganin mahaifiya ta idan har tana raye idan ko tarigani gidan gsky kasanya haske kabarin ta hakika bawa baya cire rai dasamun rahamarka Allah kazabar mun abunda ar dai dai a gare ni."
da wannan addu'a ce naji nafara samun sassaucin zafin da zuciya ta keyi,
Bani nabar gurin ba saida naji kaina yafara ciyo,
Tun daga lokacin tsana ta ta qaru a idon su hajiya kullun cikin tsangwama ta suke bama kamar fadeela  shi kuwa faruk tun lokacin ban sake sanya shi a ido ba ballantana nayi mishi bayani don naga kaman shi zai fahimta nayanke shawarar zuwa nasame shi na wanke kaina a gurin shi,.........!



Ayshart farouq

Excellent writers
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪
            26
Nayi sa'a ko yau ina cikin aiki naga shigowar shi Zama yayi nan palourn kasa tare da jawo laptod dinshi yana danna  batare da bata lokaci ba nayi hanzarin zuwa gurin shi,
sai dai kuma  narasa ta yanda zan fara yimishi maganar mayawa biyu nayi inje  kitchen indawo inata tunanin  yanda zan bullu mishi cen dai nayi ta maza na dake naje nadan rusuna nace
" ina kwana"
Bai amsa ba kuma bai dago ya dube ni ba dama nayi tunanin hk sbd tunda nake bai taba amsa gaisuwa ta ba,
Nakusa minti 5 a hk shi bai yimin mgn ba ni ban tashi ba, sai cen yace
" kina son wani abu ne?"  Yayi mgnr batare da ya kalle ni ba,
Gyada kai nayi kawai kuma sai nayi shiru cen dai nasake dakewa nace,
" dama kan mgnr kwanakki ne"
Sai nakuma yi shiru sai lokacin yadago yadube ni fuskarnan tashi daure yace,
" idan bazaki fadi ba ki tashi kiban guri"
Nace,
" dama kan mgnr zoben nan ne wlh ba.........."
Ya katse ni tare da daga min hannu alamar ya isa,
Yaci gaba da cewa ,
" idan ma kin dauka intentionally ne yarage kanki amma kisani with tym idan halin ki ne zamu gani"
Cikin mamaki na bude baki da niyar zanyi magana
Yace,
" i don't wnt hear any explanation tashi bar gurinnan"
Maganar shi ta daure mun kai natashi jiki ba kwari na fita sai da nakai bakin kofar dakin nadan juyo ga mamaki na sai naga shima yadago yana kallo na hada idanu mukayi yasakar min harara nikuma na sunne kaina qasa tare da wucewa ta,
Cikin raina ina cewa da nasani da banma yi mishi mgnr ba.

             27
Wataranar laraba misalin karfe 10 na safe hajiya tafito cikin shirin ta na fita,
ta dube ni fuskarta ba fari'a tace,
" idan kika qare ayukan ki kije dakin farouq ki gyra mishi saboda kwana biyu busy yake nasan bazai same lokacin da zai tsaya ya gyara dakin ba kinga ni fita zanyi nasan zan rigashi dawowa sai nayi mishi girki kafin yadawo  idan kuma kikaga qarfe 2 tayi bandawo ba toh kisamu wani abu ki girka mishi kikai mishi dakin shi kuma kika kuskura kika bari yaga wata alamar cewa bani nadafa ba nidake ne a gidannan",
Nakarba da " toh adawo lfy "
Direct dakinshi na nufa saboda dama naqare  ayukkana,
Kai tsaye na bude kofar dakin nashiga a cikin raina nace,
"Lallai faruk busy yake" saboda yanda naga palon shi yamutse duk da ba wata yamutsewa yayi ba nace,
" toh ko wane aiki ne hk yasha kan faruk oho?,"
Hijabi na nacire na nunke  na ajiye kan kujera saboda baki daya ban kawo wa  kaina cewa wani zai shigo dakin ba kafin na qare,
Kai tsaye na shiga uwar dakin nashi,
Kayan bacci ne a jikin shi doguwar riga da wando
Sam ban san yana cikin bedroom din ba,  na shiga toilet nagyara tsaf ,
Nafito bedroom din sai a lokacin na lura da mutum kudundunne cikin bargo nayi saurin dubawa kan gadon nan na tabbatar da faruk ne a kwance take naji cikina yana murdawa jikina tadau rawa da sauri na juya zan fita,
Sai naji yace
"Ke zi nan"
Muryarshi cen kasa irin ta marasa lafiya,
Da kyar kafafuwa na suka kaini gurin da yake,
Na zube a kasa ina cewa ,
" dan Allah kayi hkr wlh ban san kana ciki ba ne",
Ido ya zuba min yana  kallo na,
Nan take na tuna yanda nake rigar jikina ma har ta dan fara yagewa a kafada hannun farar bra ta ya bayyana,
Lokaci daya nasake rudewa ina kokarin banye dankwalin kaina don inrufe jikina,
Tsaki yaja tare da cewa,
" je ki kiramin momy"

             28
Cikin rawar murya nace .
"ta fita"
Yadan sake jan tsaki kadan tare da lumshe idanuwan shi batare da yasake cewa komai ba,
Sanin halin shi ne danayi ya sanya na mike da niyar in fita,
Cen kasan muryar shi naji yace,
''ki dafa min ruwan lipton''
Har yanxu idanuwan shi rufe suke tamkar bashi yayi maganar ba da alama yanajin jiki sosai saboda yanda nunfashin shi ke sauka,
Nan take naji duk tausayin shi yakamani na karba da
''Toh''
Nafita zuwa kitchen batare da bata lokaci ba na dafa mishi ruwan lopton din da suka sha kayan yaji nasan tabbas zaiji dadin su a yanayin da yake ciki,
Naje na rusuna na kai mishi,
Da kyar ya mike ya  zauna kan gadon jikin shi har rawa yake,
Sai naji duk banji dadi ba dama tun cen bana son naga mutum baida lafiya sai naji na tuna baba na a lokacin dayake ciyo bansan lokacin da kwalla ta zubo min ba nace,
" sannu Allah yabaka lafiya"
Yakarba da
"Ameen"
Haka na koma naci gaba da gyaran palon  duk jikina a mace, na sake kara lekowa nace,
''Sannu ko za'a kawo maka wani abu ne?"
Yace,
''Ki dafa min indomie''
Gyada kaina kawai nayi naje nadafa mishi hadaddiyar indomie cikin mintunan da basu wuce 5 ba nakai mishi,
  
           29
A palo na same shi zaune kan doguwar kujera yana sanye da singlet da gajeren wando kallo daya namishi ban sake kallon shi ba saboda yanda nagan shi,
Naja dan qaramin table din glass da ke tsakar dakin na dora  a kai na zuba mishi a cikin plate nasa spoon nace
''a baka ruwa?''
Girgiza kai kawai yayi shima batare da yakalle ni ba yace,
''Miko min wayata bedroom''
Nashiga wayar nakan gado na mika mishi  sannan nagyara cikin dakin na fito yana cin abinci yana waya yana cewa,
''Eh momy tun jiya da dare nadawo saboda jikin yadan wahalar dani nasa ta dafa min ruwan lipton da indomie.......,
Banjira yaqare wayar ba nawuce ina cewa cikin raina yau ne karo nafarko da faruk yasani nadafa mishi abinci,
Fadeela da nusaiba naci karo dasu da alama daga makaranta suka dawo, cikin su ba wadda tamin kallon arziki inda ma ban rabe ba da tureni zasuyi,
Ganin 12 tayi ne yasan ya naje na dora sanwar rana saboda abinci biyu nake dafawa dana masu gida da namu masu aikin gida kamar maigadi maiba fuLawa ruwa da  direbobin gidan.

Ayshart farouq

Excellent writes
[5/11, 10:23 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

             32
Wataranar alhamis misalin karfe goma naqare duk ayukkana haka kawai naji inaso infita saboda tun zuwana gidan kusan wata na biyar da zuwa amma ban taba leka koda bakin gate ba,
Haka ko akayi inasanye da dogon  hijabina har kasa tare da safa,
Na tunkare kofar fita maigadi yace,
"A'a yau muhibbat ina za'a"
Nayi murmushi nace,
" zan dan mike kafa ne",
Yace,
" toh adawo lfy "
Na karba da
" yauwa"
Nafita abina,
Wani titi na miqe da yayi gabas tun fitata ko tsuntsu banga ya gitta ba saboda ungur tsit take bakajin hayaniyar komai kowa yana gidan shi yana sha'anin gaban shi banfi 30 minute ba nadawo gudun kada nakasa maida kaina gida,
Koda nakoma ban ma tarradda maigadin ba cikin raina nace qila toilet yashiga.
Direct wurin xamana na nufa haka kawai bansan dalili ba naji gabana yana faduwa sai dai ban dauke abun matsayin komai ba kasancewar wani lokaci nakanji hakanan,
dagowar da zanyi sai kawai naga mutum ta gabana sai huce yake fuskar nan tashi tamkar wanda yakama matar shi da kwarto lokaci daya bugun zuciya  ta ya tsanan ta saboda ban taba ganin  faruk a wannan yanayi ba,
Cikin tashin hankali nace,
" nashiga uku me yafaru ne?
Wata banzar harara ya sakar min fuskar nan tashi tsuke yace,
'' xaki san ko meye biyo ni''
Batare da bata lokaci ba nabi bayan shi har cikin  dakin shi

            33
Sai da muka kai tsakiyar dakin sannan ya juyo ya dube ni da idanuwan nan nashi da suka rine suka xama jajur yace,
" ina kayan dake kan gadon nan? ,''
Wannan karon hannuwa na duka biyu nasa nadafe kirjina saboda tsananin fargaba,
Nace,
" wadanne kaya kuma?''
Yace,
"Kada ki raina mun hankali waye a gidannan idan bake ba koda nace ki gyara mun daki na dazu laptod dina da aipad da wallet da wayoyina guda biyu duk suna kan gado ynx nadawo naga ban gani ba a wane guri kika dora?
Cikin sarqaqqiyar murya nace,
" wlh koda na gyara dakin banga komai ba'',
''Oh shat"
Yafada tare dafara zagayar dakin sai kuma yasa hannun shi aljihu ya dauko wata karamar wayya wadda naga ya cika amfani da ita kuma da alama itace qarama a cikin wayoyin shi,
Wayoyin shi yashiga kira amma kuma kuma duk an kashe wayoyin,
Yayi kira yafi a qirga duk abu daya ake cewa wato a kashe,
Daga baya hajiyar shi yakira sai dai banji abunda yake cemata ba saboda waje yafita
Cikin mintota ya dawo, nidai ina nan inda ya barni ko motsi nakasa yi saboda tsananin tsoro da fargaba.
Muryar shi kasa kasa
''Yace na neme kayana duk inda nake tsammani ban gani ba  ina rokon ki da Allah idan kinsan kin dauka ki gayamin inda suke inje in dauka ynx hk akwai abunda ake jirana asibiti inkai kuma yana cikin laptod  plz ki gayamin dan Allah wlh idan kika bani namiki alkawarin bazan miki komai ba"
Ni kwata kwata ma narasa abunda zance saboda naga  abun nashi yafara wuce guri so yake in dorawa kaina abunda ban aikata ba,
Yayi juyin duniyar nan akan ince wani abu amma uffan bance ba  saboda nasan komai nace bazai taba yadda da bani nadauka ba

              34
Ganin yanda nayi banxa dashi ne  ya sanya ya  harzuqa ya fisgoni da karfi har bakin gate din gidan maigadi ya taso yana cewa,
''Mai yafaru ne yallabai''
Faruk ya dube shi yace wani ya shigo gidan nan bayan fitar mu"
Maigadi yace,
" ai kamar yanda na gayama daxu ba wanda ya shigo gidan nan tun fitar ku ranka yadade''
Faruk yasake cewa,
" toh wa yafita?"
''Muhibbat kadai tafita gidannan bayan fitar ku"
Faruk yasake tmbyr cewa,
"Ina taje kuma da me ta fita?''
Yace,
'' gaskiya bansan inda taje ba kuma bazan iya cewa ga abunda tafita dashi ba saboda sanye take da dogon hijabi"
Faruk Bai sake cewa komai ba yafigeni sai waje ya wulgar dani idanuwan nan nashi sun qara rinewa sun koma jawur,
cikin kakausar murya yace,
'' hakika kin bata wayon ki saboda kin aikata abunda ban taba tsammanin zaki aikata ba  wannan nutsuwar taki taxama ta banxa tunda kike halin bera  Allah waddan halin ki kuma ki sani zaman gidannan yaqare gareki saboda Mu baza mu iya zama da barauniya ba,
hakika ke kina cikin gurbatacin talakawan nan da basa godewa ubangijin su barauniyar banza jak.........''
'' ya isa haka"
Na katse shi  saboda rayuwata tayi matukar baci da kalaman shi hakika kalaman shi tamkar an watsamun wuta nake jin su bansan lokacin da nafashe da kuka ba nace,
" kafadi maganar ka son ranka amma kasani wannan talakar da kake gani is beyond your imagination Allah yana sama yana gani shi zaimana hisabi dakai ranar alqiyama" ina qare fadar haka najuya kawai natafi da gudu,
Hakika kalaman ta sun taba zuciyar faruk sai dai kafin yayi yunkurin cewa wani abu tune tayi nisa,
Wayar shi daketa ringin yadauka ya kara a kune cikin tashin hankali ya shiga gida batare da yasan indama yake takawa....

Ayshart farouq

Excellent writers

Rwly nid ur prayers fans
Luv yah all
[5/11, 10:24 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

             30
Yau nagaji matuka saboda aikin da nayi sanadiyar dawowar maigidan  wanda duk lokacin da zai dawo akanyi dafe dafen abinci mai yawa kasancewar shi mutum ne mai matukar son jama'a ga kyauta shiyasa idan har yana gida toh  bazaka taba raba gidan da almajirrai da masu roko ba.
Tun safe aiki daya nake bani nasamu kaina ba sai bayan la'asar,
daki naje nadan kwanta saboda yanda kaina kamin ciyo.
Chan har bacci yasoma dauka ta naji ana kirana
''Muhibbat''
Da sauri naje domin karba kiran hajiya.
Dukan su suna zaune cikin falo har Alhaji da qanwar shi hajiya safiyya  da yayan hajiya Ameena wato mahaifin fadeela,
Cikin sauri narusun nagaida su cikin fari'a suka karba take naji gabana ya fadi saboda ganin irin kallon da mahaifin fadeela keyimin,
Cikin tsawa hajiya tace
''Bakiga baki ba ne hala kinxo kin xurwa mutane ido kamar mayya maxa kije ki kawo ruwa,
Cikin sauri namike xuwa kawo musu abin motsa baki
Ina kitchen din ne naji muryar hajiya tana cewa,
'' yanxu dan Allah kai yaya abinda kayi ka kyauta ace kafifita bare akan yaruwar ka?
Yace,
''Ni ban fifita xara'u akan safiyya ba saboda ko ba komai safiyya yar uwa ta ce amma a gaskiya bazan taba rabuwa da mata ta ba saboda ita mata ta bata min komai ba muna zaman lafiya da ita  tayaya zan rabu da ita fusabilillahi?
Dadyn su faruk ya chabe maganar da cewa wlh banga laifin ka ba Usman
Hajiya safiyya tace,
''Yaya kadaina daurewa baban fadeela gindi kai kan ka kasan abunda yake mun baya kyauta mun kai

           31
Kai ya kamata ka fahimce ni idan kowa yakasa fahimta ta kaida muka fito ciki daya da kai,''
''Toh banda ke da abunki safiyya  dan munfito ciki daya dake sai ace kuma in kaucewa gaskiya ai kema kinsan bazai yiyuba
Amma ynx kifadi duk abunda kikasan yana miki gashinan sai ya gyara ni shawara ta a gareki ki koma gidan mijin ki ko dan yaran ki,
Ki duba ki gani fah ynx a matsayin ismai' il da fadeelah bai dace ace iyayen su basa tare ba''
Yace,
'' ai ni banida matsala ko ynx taji tana son ta koma dakin ta  kofa bude take nidai abinda nasani bazan taba sakin zara'u ba saboda ita"
Sallama ta ce ta katse musu maganar da suke,
Ko yanxu dadyn fadeela kuramin ido yayi tamkar mai nazarin wani abu cikin sauri na ajiye kayan nayi gaba abina,
Direct Gardiner na wuce saboda yanda naga fadeela da Nusaiba gaban iyayen su suna shagwaba sai nima  take naji kewar mahaifi na da mahaifiyata  ta kama ni,
xaune nayi na dora hannuna kan kumatu na nashiga tunani bani nabar gurin ba sai da naji anyi kiran magariba,
Ina fitowa naci karo da Faruk,
Kallon sama da kasa ya yimin  sannan yace,
" inata neman ki tun dazu ina kika ajiye mun laptod dina da wallet  don nayita nema ban gani ba,
Ni sai lokacin ma na tuna da yasani gyaran dakin shi da safe naga laptod dinshi da wallet na dora kan wardrobe  muryata sarke nace,
Suna kan wardrobe,
Yayi tsaki yace,
" bana rabaki da tabamun kaya ba ko?"
Nidai bance komai ba na wuce abina
[5/11, 10:24 AM] KAURA: 😪😪DAMUWA TA😪😪

             33
Hankalin faruk bai kara tashi ba saida yashiga cikin gidan yaga hajiyar shi dauke da laptod fadeela dauke da wallet da ipad yayin da Nusaiba ke dauke da wayyoyin shi guda 2 ko wacce fuskarta dauke da fari'a cikin dariya dukan su suka ce
" April fool bros"
Dakin  yaji yana juya mishi saboda tsanani rudewar da yayi,
Dafe kanshi yayi saboda wani jiri da yaji yana daukan shi innalillahi wainna ilaihirraji'un ya fada tare da cewa,
" why did u do dis to me momy ?
Why ?why ?!
momy na cuce muhibbat na zalunce ta,
da gudu yafita gidan yashiga motar shi yabi hanyar da yaga tabi  a tunanin shi zai cimmata tunda batayi nisa ba sai dai kash! Duk inda yake tunani  yagan ta yaduba bai ganta ba kuma ya tabbatar dacewa idan ana gilma mahaifiyar shi a yanka bazata fadi ko wane guri take ba,
  har ya manta da abunda yake nema a laptod dinshi dole kira yayi ya shaida musu bashida lafiya bazai samu damar komawa a asibitin ba,
Lokacin da yashiga gida tamkar wani dan maye saboda tsanani tashin hanklin da yake ciki direct dakinsu fadeela ya isa yasame su ya  hau jibgar su tamkar wanda Allah ya aiko .
da gudu hajiya ta karasa dakin tana kiran
" faruk hankalin ka daya kuwa?
nashiga uku na lalace ni Ameena faruk kashemin yara kake so kayi ne?"
Shi kuwa tamkar qara zugashi ta ke yi,
ganin bashida niyar daina dukan su ne yasanya ta saka kuka tana dukan bayan shi, tana bashi yakuri kan ya qyale su hakanan
Dakyar Yadaina dukan su ganin momyn tashi  tana kuka tana rokon shi,
Shi kanshi idanuwan shi hawaye suke zubar wa,
 
             34
Batare da yakula halin da suke ciki ba kawai yawuce dakin shi yana shiga yafada kan gado yana wani irin kuka mai ban tausayi da nuna tsantsar nadamar abunda yayiwa muhibbat ba abunda yake tunowa irin fuskar ta lokacin da take kuka tana  cewa,
"Allah yana sama yana ganin ka kuma shi zaimana hisabi dakai a ranar alqiyama"
hakika maganar ta gskiya ce,
Cikin kuka yake cewa
"  hakika na tafka kuskuren da ban  taba aikata irin shi ba hakika idan na mutu a yau ba abunda zaisa inshiga aljanna matuqar baki yafe mun ba,
muhibbat ina zangan ki na neme gafarar ki? Innalilallahi wainna ilaihirraji'un ya Allah kayi gaggawar nuna min wannan baiwar taka tun kafin na mutu da alhakin  ta a kaina,
Haka yayita sambatu shikadai  tamkar wani zararre,

Ni kuwa tunda nabar bakin gidan jiri ke dibana ina kawo kan wata kwana na zube a daidai lokacin da wata mota ta kunno kai cikin tashin hankali mai motar ya tsaya wanda yake tare da matar shi batare da bata lokaci ba suka nuface asibiti dani domin ceto rayuwa ta,
Sai wuraren magarib na falka koda na bude idanuwa na sai naganni kwance kan gadon asibiti wata mata zaune dan nesa dani kadan tana ganin natashi tayi hanzarin xuwa guri na tanamin sannu,
Ni kuwa sai  a lokacin na tuna abunda yafaru dani,
wasu kwalla masu zafi suka  shiga zubo min,
Matar tace,
" ba kuka yakamace ki kiyi ba addu'a yakamata kiyi hakika da ganin ki kina cikin damuwa amma a matsayin ki na karamar yarinya bai dace ace ki riqa sawa kanki damuwa irin hka ba ynx hk likita yayi mun bayanin cewa kina gab da kamuwa da ciyon xuciya kin........."
Bata kai da qare maganar ta ba aka turo kofa aka shigo wani mutum ne wanda zaikai kimanin 50 yrs tare da docter,
Likitan yace,
" ynx xaku iya tafiya da ita gida she's out of danger now amma yakamata kuriqa jamata kunne da tadaina tunanin da takeyi na  sallame ku,
idan kunga  kuma akwai wata matsala zaku iya dawowa da ita"
Sukayi sallama likitan ya wuce abinshi,
Nan fah mutanen sukata yimin tambayoyi amma nakasa buda bakina inyi magana sai kuka kawai nake,
Ganin haka ne yasan ya maigidan yace,
" madam yakamata muje da ita gida zuwa da safe idan hankalinta ya kwanta sai ta gayamana gidan su muje mu kaita ko ya kika gani?"
Tace,
" haka yakamata muyi"
Nan ta umurce ni da insaka hijabina da banma san ya akayi ya cire ba,
Batare da bata lokaci ba nasanya hijabi na nabi bayansu har bakin motar su muka shiga muka wuce zuwa gidan su...........

Ayshart Farouq

Excellent writers
[5/11, 10:24 AM] KAURA: DAMUWATA
          
           37
Gidan babban gida ne naji da fada bayan mun shiga  babban falon ne matar ta umurce ni da inxauna bayan na zauna ta gabatar mun da abinci batare da bata lokaci ba nahau ci dama tsinanniyar yunwa nake ji,
Saida nagabatar da sallolin da ake bina sannan nayi magriba da isha'I na kwanta sai dai me juyi kawai nake ina tunanin wulaqancin da Faruk yayi min hakika yayimin abunda ba a taba yimin ba tun zuwana duniya duk bala' in inna wuro bata taba doramun sata ba,aiki na a gidan su faruk ya qare ko kina so ma bazaki koma ba saboda faruk ma bazai barki ba inji wata zuciya  wata zuciyar kuma  tace mun to ynx ke muhibbat ina zakije ko kin manta gargadin inna wuro ne?
Innalillahi wainna ilaihirraji'un  hakika wannan kalma itace kalmar da nake fadi duk lokacin da nasamu kaina cikin wani mawuyacin hali nayita maimaita kalmar har saida naji nadan fara samun nutsuwa a zuciya ta, bansan lokacin da barawo ya sace ni ba saida naji anfara kiran asuba sannnan na tashi,
Nayi alwala nayi sallah na dauki quranin da nagani kan drower nafara karantawa.
Wuraren karfe tara matar gidan ta turo kofar ta shigo ni kuwa narufe quranin na ajiye ina shafa addu'a ta dube ni cikin sakin fuska tace;
" sannu ki ya jikin naki"
Cikin sunkuyar da kai nace naji sauki tare da gaida ta ta amsa tare da cewa zo muje dinning kiyi break fast
Tare muka fito muka nufe dining din maigidan na zaune narusuna nagaida shi  shima cikin sakin fusa ya karba yana min ya jiki,
Nakarba da jiki da sauki Alhmdlh

            38
Bayan munkammala break fast din ne matar ta dube ni tace,
'' ni sunana hajara mijina kuma mu'azzam ke ya sunan ki na sunkuyar dakai nace,
"Muhibbat"
Tace,
'' muhibbat ko zamu iya sanin unguwar ku domun maida ki gida?,
muna so musan gidan ku da kuma dalilin da   yasa muka same ki cikin halin da muka ganki''
Hawaye ne suka soma zilowa a idanuwana bakin cikin abunda yafaru dani ya taso min
Tace,
"A'a muhibbat ba kuka xakiyi ba gayamana zakiyi abunda ya fito dake daga gida"
Na dago kaina na dubesu duka matar baxata wuce 30 yrs ba tanada kyau sosai sbd idan kaganta bazaka taba cewa wannan ne mijin ta ba,
Mijin kuwa zaiyi 50 yrs baki ne mai jiki daka ganshi dai kasan irin maxan nan ne Allah kyauta ga yawan kallo don tunda nazauna yake kallo na,
Cikin kuka na kwashe duk abunda ya faru dani na gayamusu hakika sunyi matuqar tausayamin bama kamar matar,
Mu'azzam yace,
" kada ki damu zamu taimaka miki insha Allahu"
Anty hajara tace,
'' zan zauna dake ki dan riqa kama min aikin gida"
Nayi musu godiya sannan na tambaye ta ko akwai wani abu da zanyi mata,
Tace,
"Kije ku huta kinga bakida isassar lfy ki barshi kawai inyi"
Nayi murmushi
Nace,
"Ai naji sauki"
Dakyar dai tabarni nayi mata shara,

          39
Yau sati na daya a gidan hakika na fahimce anty hajara mace ce mai matuqar kirki da sanin darajar dan Adam sai dai mijin ta ne nake dan shakku shakku dashi saboda duk yafita yadawo zai sawo min wani abu ya bani  kuma baya bani kusa da matar shi sai yayi la'akari tashiga daki ko kuwa ya kwan kwaso min kofa yabani abun yana matuqar daure mun kai ga yawan kallon da yake mun ko ina kusa da matar shi ne wani lokaci har kunya yake bani,
Yau ina kwance kan doguwar kujera har bacci yafara daukata naji kamar ana lalube na da sauri na mike naga mu'azzam ne ya washe mugun bakin nan nashi yana ceewa,
" koma yi baccin ki muhibbat remote nake nema ashe bata cikin ki,
ni kuwa ban ma san lokacin da nayi tsaki ba banma dube inda yake ba nawuce daki abuna ina tunanin wannan abun a zuciya ta,

Shi kuwa faruk xama yayi tamkar tababbe,
Saboda kusan ko yaushe ya kwanta sai yayi mafalkin irin cin zarafin da yayiwa muhibbat su fadeela kuwa ynx bala'in tsoron shi suke saboda ynda ya koma baya sakar musu fuska ko kadan ko hajiyar shi don dai tazama mahaifiyar shi ne yake kula ta,
Faruk har kano yake gurin neman muhibbat don ya roqe gafarar ta amma babu ta babu labarin ta inna wuro kanta ta shiga tashin Henkali saboda da albashin muhibbat ne ta dogara don jallin waina tune ya mutu,
Haka faruk yadawo gida hankalin shi tashe saboda ganin yake komai yafaru da ita shine sila shiyasa ya dukufa da addu'ar Allah ya bayyanar mishi da ita domin ya gyra abunda ya bata,.................wannan kenan,

Ni kuwa gidan anty banida wata matsala face ta mu'azzam don yanxu abun nashi yafara wuce gona da iri,

                 40
Watarana misalin karfe 12 anty hajara tafito cikin shirinta na fita unguwa tare da mu'azzam tace,
"Muhibbat yau kimana fried rice kafin mudawo"
Nakarba da toh
"Anty adawo lfy"
Shi kuwa gogan wani kallo ya watsomin tare da hade yawu yafita matarshi na baye da shi,
Wuraren 1:30 ina kitchen na dukufa da aiki na cen naji motsi bayana cikin tsoro najuyo mu'azzam nagani fuskar shi dauke da murmushi nan take na dabirce cikin un un nace,
"Me kake so ne Alhj"
Sakin kofar yayi batare da ya karba ba ya matso daf dani yace,
" sorry mun barki ke kadai ko?
Na dan dukar da Kaina kasa tare da ja da baya saboda yanda jikina ke kyarma,
Nasake cewa,
"kana bukatar wani abu ne,?"
Yasake matsowa  kusa dani tare da lakatar min hanci yace,
" sarkin tsoro gurin ki nazo magana nake so muyi "
Jiki na yadau rawa nace inajin ka,
Ya sosa keya yace,
Maganar bazata yiyu a tsaye ba,
Batare da yajira me zaice ba ya wuce ni kuwa nabi bayan shi har falo sannan yazauna tare da nuna min kusa dashi wai inxo in zauna nikan kasa na zauna dan nesa dashi kadan sai me ganin mutum kawai nayi yadawo tagabana kusa dani ya zauna,
Cikin hanzari na mike fuska ta cike da tsoro yayi saurin riko min hannu yana cewa haba muhibbat toh meye a ciki taimakon juna fah zamuyi,
Na kwace hannu na cikin muryar kuka nace,
" meye hk?"
Yace,
"Plz muhibbat ki kwantar da hankalin ki bazan cutar dake ba kawai so nake ki bani hadin for once in debe kisar sha'awar ki dake damuna,"
Nakatse shi da cewa,
" banyi tunanin haka a gurin ka ba ni ba fasika nake ba dan allah kayi hkr wlh zanbar maka gidan ka idan hk kake so,
Yace,
" haba yan mata nafasan irinku da bariki ta kakarewa kuna fesawa mutane qarya nasan ba yanda za'ayi ace xuqeqiyar yarinya kamar ki tana aikatau come on ki bani hadin kai zakiji dadi xan mallaka miki gida da mot..........,
Kukan da nafashe dashi ne yakase mishi maganar shi,
Ja da baya kawai nake ina fadin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah yayimin tsare da shaidanin mutum irin ka,
Yayi wata dariya yanufo ni gadan gadan cikin kuka nace,
" wlh idan ka tabani xan maka ihu"
Ya sake fashewa da dariya yace,
" ihun ki na banxa ko kinyi baji xa'ayi ba  kawai kibada hadin kai kici arziqi,
Naja baya saida nakai bango nayi tsaye naruntse idanuwa na, ina ta kuka tare da roqon shi da ya kyale ni amma tamkar wanda nake qara tunxurawa  hannun shi yakai xai  tabani kenan mukaji ana dukan kofa da qarfi,
Wani irin ajiyar zuciya nayi da qarfi tare da bude idanuwa na dake zubar da hawaye,
Shi kuwa mu'axxam take tsoro yakamashi sanin ko waye,
Cikin zafin nama nayi hanyar kofar zan bude,
Mu'azzam ya dakatar dani da cewa,
" idan kikaje a hk hajara xatayi tsammanin wani abu" wata harara na watsa mishi naci gaba da tafiyata cikin zafin nama ya fisgoni ya wulgar dani kan kujera ya nufe kofar ya bude,
Wani kallo anty hajara tashiga yi mana tamkar ta kama barayi,
Ganin irin kallon da take min ne yasa na sake rudewa na fashe da wani irin matsanancin kuka,
[5/11, 10:24 AM] KAURA: DAMUWA TA
         41
Da yake shi namiji munafuki ne sai ya wayance yana cewa "ynx ko nake batun inkira ki kinga daukar wayar da nadawo yayimun anfani don gashi na dawo nataradda muhibbat tana kuka kuma nayi nayi tagayamun me takewa kuka taqi tayi mgn,"

" subuhanallah! Me take wa kuka?
Anty hajara ta fada a taorace,
Yace,
" ina xan sani tunda bata gayamin ba,
Tare suka qaraso gurina tana tambaya ta "muhubbat me ya faru ne?
Ni kuwa saboda tsananin bakin ciki bansan lokacin da nadake fashewa da kuka ba,
Hankalin anty hajara yatashi tazo ta zauna kusa dani tana ta lallashina kan ingayamata abunda ke damuna,
Cikin raina nace idan nagayamiki abunda ke damuna yankamu xakiyi nida azzalumin mijin ki,
Amma a fili nace,
" nayi mafalki ne da mama na Rayuwata tana bani mahaifiya ta tana raye  cikin koshin lfy shiyasa nake so na koma garinmu saboda chan ne kadai zan koma insadu da mahaifiyata dan Allah anty hajara ki taimake ni ki maidani
garinmu"
na fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro,
             
                42
Anty hajara tayi shiru nadan lokaci kadan sannan tace,
" ki kwantar da hankalin ki muhibbat kada kidamu insha Allahu namiki alkawarin nan da sati 2 zan maidaki garin ku yi shiru share hawayen ki,
Mu'azzam dake tsaye jin zan koma take jikin shi yamutu ko maganar da anty ke mishi bai saurara ba ya haura sama abinshi,
              
Tun ranar ba abunda ya sake hada ni da mu'azam saboda bana fitowa sai nayi la'akari da yafita kuma bana yadda anty hajara tafita tabarni ni kadai cewa nakeyi tsoro nakeji  shiyasa duk inda zataje tare dani take xuwa.

Watarana misalin karfe 12 nadare ana gobe xanje garinmu murna kawai nake yayin da tsoro da fargaban bala'in inna wuro ya yayemun a cikin zuciya,
Iska akeyi mai dadi sakamakon hadarin da ya mamaye sararin samaniya,
Kukan tsuntsaye kawai kakeji tare da iskan da ke kadawa,
Bacci  na nake mai dadi,
Cen cikin baccin naji kamar ana shafar min jiki daga farko nadauka mafalki nakeyi sai daga baya nafara jiyo nishin mutum a kaina xunbur na mike tare da salati ganin mutum da nayi fuskarnan tashi murtuqe idanuwan shi jajur tamkar wuta daga shi sai boxer da singlet cikin tsoro na bude baki
             
              43
Zan kurma ihu  yayi saurin toshe mun baki da hannun shi yana cewa,
Kada kimun ihu muhibbat dan Allah ki fahimce ni wlh ina matuqar sha'awar ki dan Allah ki taimaka min ki bani hadin kai ta lalama wlh idan kika qi ta qarfin tsiya xan miki,
Nikan tuni hawaye suka shiga fitowa daga idanuba sai gyada kaina nake tamkar wata kadangaruwa   nashiga hada shi da Allah kada ya keta mun mutumcina amma ina tamkar ma ina qara zuga shi don dayaga ina nema inbashi wahala sai yasanya wani kyalle ya rufe mun baki ya banqare mun hannuwa ta baya ya shiga cire kayan jikina,
Ni kuwa sai ihu nake amma ba maiji na saboda yarufe baki na,
Lokacin da yayi sa'ar ciremun riga ba qaramin fita hayyacin shi yayi ba saboda ganin albarkatun kirji na,
Bakin shi yakai gurin da niyar ya tsotsa ban san lokacin da wani karfi yaxomin ba na mirgina nayi ruf da ciki,
Ganin hk ne yasa ya shiga duka na amma tamau na matse jikina ina wani irin fitinannen kuka,
Abinka da namiji lokaci daya yasake mirginowa dani tare da watsamin wani gigitaccen mari yasa guwayyun shi duka biyu ya danne ni dasu sai yazama ko motsi ban iya yi.
Shi kuwa sai ya shiga nema ya ketamun haddi,

Ayshart farouq

Excellent writers

©Ayshart one©
[5/11, 10:24 AM] KAURA: DAMUWATA

         44
Cikin raina kam innalillahi wa'inna ilaihirraji'un nake fada Allahumma ajirni fi musibati wakhalifni khaira minha duk addu'ar da tazomin fadi nake domin nema Allah tsari daga sharrin mu'azzam,
Yana gaf da keta haddi na muka ji an turo kofa da karfti ana  buga salati,
Anty hajara ce tsaye cikin kuka ganin yanda mijin ta ke nema ya keta mutuncina,
Kuka take tana cewa "nashiga uku ni hajara  mu'azzam me nake shirin gani hk,?"
Lokaci daya yadawo hayyacin shi jikin shi yayi lakus duk ya mutu hk ya dagani bako kunya ballantana tsoron Allah yabi matarshi daketa rusar kuka,
Ni kuwa da aka bubbugw kasa tabuka komai nayi sai hawayen dake fita idanuwana  muryata duk ta shaqe ko fita bata yi saboda tsananin azabar da nasha sai dai a zuciyata Allah kawai nakewa godiya da yasake kubutar dani hannun mu'azzam batare da yaketa mun mutunci na ba.

              45
Wata zuciya tace mun ynx ke muhibbat da wane ido xaki kalle anty hajara ko kuwa da wane baki xakiyi mata mgn,
Nasake fashewa da kuka ina cewa ya Allah kayi gaggawar daukan rayuwata yanxu yanxunnan hakika Allah kaine gatana kuma gareka na dogara kai ke kashewa kuma kake rayawa kai ke fitar da rayayye a cikin matacce ka kuma fitar da matacce a cikin rayayye ya Allah ina rokon ka da kadauke rayuwata idan mutuwata ce Alkhairi a gareni  ya Allah idan kuwa rayuwata ce alkhairi a gareni ina roqon ka da kasanya DAMUWATA tazamo tarihi a gare ni ka kareni da sharrin mashairan ta kasanya Aljanna tazamo makoma ta hakika ni qasqantatta ce maraya talakar da tarasa gata sai naka ya Allah hkika duk wanda yasamu gatan ka yasamu gatan kowa ya Allah ka qara bani hakuri da juriyar rayuwar dana fuskance kaina a cikin ta,
Irin wadannan Adduo'in nayi tayi har nadan samu zuciya ta tarage zafin da takemun sai dai kaina tamkar ya tsage saboda kukan da nayi,
Cen wata xuciya tace mun ki gaggauta barin gidannan tun kafin ki hadu da anty hajara da mu'azzam,
Ai kuwa nan ta ke namiqe naje na doro alwala nafara jero nafilfili har aka kira asuba,
Ina qare sallahr asuba wuraren qarfe shidda da rabi  nabar gidan anty hajara,

              46
Nakama hanya ga hadarin da baiyi ruwa ba jiya yau yayi baki kirin sai chida ake da walqiya ni kuwa ban damu ba fatana kawai inganni tashan shiga mota nayi tafiyar 30 minute ban hadu da kowa ba cen na hange wani mutum zai shiga gida da sauri na tsaida shi tare da cewa "Assalamu alaikum "
"Wa'alaikissalam" ya karba yana dubana cikin mamaki,
Ban damu da duban da yake mun ba nace,
" dan Allah ina ne tashan shiga mota,?"
Dariya naso nabashi sai dai yadake yayi murmushi yace,
" ke ba yar garin nan bace da alama"
" eh" nafada a takaice,
Yace,
" om toh gsky daganan unghwar zuwa tasha akwai nisa sosai sai dai ki miqe hanyar nan straight xaki hau wani babban titi may be nan xaki iya samu abin hawan da zaikaiki  amma kuma da kinshigo daga nan kin dan rabe naga anfara ruwa,
Girgixa kaina kawai nayi tare da cewa,
"Nagode sauri nake"
Bai damu ba ya shige gida abinshi,
Nikuwa nahau hanya ruwan da ake sai qara karfi suke amma duk da haka nakasa tsayawa tafiyata kawai nake cikin ruwan da ake sheqawa tamkar da bakin kwarya nidai fatana kawai insamu abin hawa,
Nahau titin sosai inata tafiya iska tamkar ya dauke ni chidar da akema tafi bani tsoro ba ruwan ba,
Tafiya nake tamkar wadda kwai yafashewa a ciki  saboda yanda nake jin kaina tamkar ya tsage ga jiri ina ji bana ko iya ganin abunda ke gabana saboda ruwan da ake,
Chan naji anja birki da karfi ta gabana,
           
              46
Mutuwar tsaye nayi saboda yanda motar ta tsaya,
Da sauri mutumen ya fito yana mgn,
Sai dai me ni kaina kasa gasganta idanuwana nayi lokacin da na hango fuskar shi cikin lemar da ya dauko don kare kanshi daga dukan ruwan,
Nakasa furta kalma daya saboda ynda hauruna suka datse,
Shikan ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin muhibbat din da yake nema ruwa jallo,
Nikan ja da baya nariqa yi saboda banma san me zance mishi ba ko sunan shi nakasa furtawa ballantana insan me xance mishi xuciya ta tasake tunkushewa idanuwa na hawaye kawai suke fitarwa hauruna sai kar kar kar suke saboda tsananin sanyin da ya tasomin jikina ya shiga rawa ga fuskata duk ta kumbura ,
Cikin wani yanayi faruk ya sake lemar hannun shi yaqara so gurina saidai kash kafin yakaraso tune na yanke jiki nafadi kasa somamma............!!

Abubuwa sunmin yawa shiyasa kukajini shiru,

Luv u all my fans

Ayshart farouq

Excellent writers

©Ayshart one©
[5/11, 10:24 AM] KAURA: DAMUWATA
       47
Cikin tashin hankali faruk yayi kanta yana jijjigata muhibbata! Muhibbat! Ba alamar wani motsi a tare da ita,
Tallabarta yayi baki daya tamkar wata yar tsana bai damu da ruwab dake tsalala jikin ta ba yasanya ta mota sai asibiti,
Saida nasamu gurin awa biyu sannan na falka koda na bude idanuwa na kwance naganni sanye da wata riga anja bed sheet  anrufe min jikina dashi  mamaki nayi ynda aka cire kayan jiki na aka sanyamin wasu a hnkl nayunkura na mike zaune idanuwana tas akan faruk dake tsaye nesa dani kadan ya nade hannayen shi a kirji yana kallon sillin komai yake tunani oho
Ganin na falka yasa  yayi saurin karasowa gareni yanamin sannu,
Kwata kwata bana bukatar ganin shi saboda wata irin tsanarshi nakeji domin a  ganina duk shine silar shigata halin da nake ciki,
Rufe idanuwana nayi tare da furta natsane ka faruk na tsane ka, sai dai muryata  bata fitowa baima san me nake cewa ba,
Hawaye suka shiga sintiri a fuska,
"Oh God"!
Ya fada tare da xama kan gadon da nake kwance zubamun idanuwa kawai yayi yana sauraron kukan da nake wanda bashida sauti, kukan da  ya tsuma zuciyar shi da gangar jikinshi cikin wani yanayi da bazan iya mislta wane iri bane najini jikin farouq tsakiyar fadadden kirjin shi,
             48
Zuciyar shi bugawa take tamkar tafito idanuwan shi dauke da hawaye yana cewa,
"Muhibbat na cuce ki na zalunce ki muhibbat don girman Allah kiyafe min,
Ni kuwa kalma daya takasa fitowa bakina gashi banida wani karfi da zan ture faruk jikina nima kawai sai nasake wani kukan da banma san ya akayi muryata ta fito ba sai lokacin ya sakeni tare da rikemun hannu,
A hnkl yake maga
" hakika tunanina da hankalina duka sun gushe a lokacin da nazamo mai son kai a gare ki, just give me one more chance i will correct ol my mistake muhibbat idan har baki yafe mun ba nasan baxan taba samun peace of mind ba, yasake hannuwana tare da xube duka guwayyun shi qasa yana min magiya akan in yafe mishi,
Hakika naji tausayin shi ganin duk girman shi da matsayin shi yau shine a kasa yana roqo na cikin qarfin hali nace,
" xan yafe maka amma da sharadi,
Da sauri ya mike yana cewa,
" ki gayamun ko mene ne xan miki idan dai har xaki yafe min,"

Ayshart Farouq

Excellent writers

©Ayahart one©
[5/11, 10:24 AM] KAURA: Damuwata
         
            49
Nace,
" zaka maidani garin mu gaban iyaye na"
Da sauri ya dube ni cikin wani yanayi na fargaba,
Na gyada kai tare da fashewa da kuka ina cewa,
Baxan iya xama gidan ku ba faruk baxan iya sake xama karkashin kowa ba face yan uwa na na rokeka da girman Allah ka taimake ni ka maidani gidan mu,
hakika ya tausaya mata matuqa ganin halin da tashiga lokaci daya,
Muryarshi chan qasa yake magana,
" ki kwantar da hankalinki namiki alkawarin sadaki hannun iyayen ki  amma sai kin same karfin jikin ki,
Idanuwana jajur na dube shi nace,
" idan har xaka taimake ni don Allah ka kaini yau wlh baxan iya sake kwana daya garin nan ba,
Natsane garinnan da mutanen dake ciki  idan nasake kwana a ciki mutuwa zanyi dan Allah ka taimake ni,
Faruk ya rasa me xaice saboda ganin yanda narude lokaci daya,
Yamaida ajiyar xuciya tare da mikewa tsaye yafita batare da yace min komai ba,
Kusan minti goma shabiyar suka shigo tare da wani likita da wata  nurse,
Bayan yayi yan rubuce rubucen shi ya dube farouk cikin harshin turanci yace,
Docter farouk a matsayin ka na kwararren likita bai dace kabar yar uwar ka cikin irin wannan damuwar ba gashi inda bamuyi da gaske ba da sai anmata aiki a zuciya sbd tasamu rauni a zuciyar ta idan har kuka bari tasake shiga hali makamancin wannan toh komai zai iya faruwa da ita,
Xufa ne ya karyewa faruk tamkar wanda ya hadiye kunama hankalin shi idan yayi dubu ya tashi ganin yake tamkar shine ummul khaba'isun shigar muhibbat halin da take ciki mgnr da  docter keyi baimaji ba bashi hannu kawai yayi  tare da mishi godiya docter ya wuce abin shi nurse din da ke tsaye ta duban cikin murmushi tace sister me yasa baxaki bari kiqara mirmijewa ba kika tasarwa da oga hankali kan sai an sallame ki,
Na danyi yaqe tare da cewa nasamu sauqi ai idan naje gd xanci gb da shan mgn,
Ta ban wasu yan shawarori tare da yin sallama dani tayi gb abunta,
Faruk kam tsaye yake har ynxu da alama baima ji me muke cewa ba sbd yayi nisa cikin tunani,  
Sai da namishi mgn yakai sau biyu sannan ya dawo hayyacin sa,
                 
                   50
Ya dubeni a raunane yace,
" muhibbat kinji abunda docter yace ko?,
Na dan tabe baki sbd ba yau nasaba jin irin haka va saida nima yau abun ya tsorata  ni,
Nace,
" duk abunda ya faru da bawa jarabawa ce daga Allah nagidewa Allah da jarabawar da yayimun kada ka damu komai xaizo qarshe,
Gyada kanshi kawai yayi tare da cewa bari naje nasamo miki abunda xaki ci sai muwuce,
Ba tare da ya saurare mai zance ba ya wucewar shi,
Misalin karfe 12 naci avinci nakammala komai aka bani takardar sallama muka kama hanyar garin dabo,
Tunda muka hau hanya ba wanda yayi magana,
Ni kaina sai lokacin naji jikina yayi sanyi nafara tunani abunda xan tarad gurin inna wuro ni ba sanin dangin mahaifiyata nayi ba ballanta na ince yakaini yola dawakin tofah kuwa ba inda xanje tunda yan uwan mahaifina duk qarqashin inna wuro suke gurin inna wuro ne kawai mafita a gare ni,
Shi kuwa faruk Allah kadai yasan abunda yake tunani lolkaci lokaci yakanyi ajiyar zuciya tare da jan gajeren tsaki,
Muna cikin haka bacci barawo ya sace ni dama kuma  akwai shi a ido na,
Shi kan faruk ido kawai ya zuba mata yana kallon halittar ubangiji hakika muhibbat ba qaramar mace bace tana da baiwar kyau da tsari komai nata yana burge shi, Allah kadai yasan abunda yakeji game da yarinyar tun da dadewa,
Lokaci daya yamaida hankalin shi ga abunda yake tare da sanya karatun alqur'ani mai girma har suka shiga garin kano,
Ni kuwa sarkin bacci sai lokacin nafarka tare da salati ya juyo muka hada ido yasakar min murmushi tare da cewa " sarkin bacci kinsha bacci "
Gyada kaina kawai nayi har muka isa unguwar mu......

Ayahart farouq

Excellent writers

©Ayshart one©
[5/11, 10:24 AM] KAURA: Damuwata
 
            51
Nayi mamaki sosai ganin faruk yana shiga cikin unguwarmu tamkar wanda yasan guri,
Yadube ni yayi murmushi tare da cewa,
" kinyi mamakin yanda nasan gdn ku ko"
Nagyda kaina alamar eh,
Yace ,
" ranar da nagane gsky ranar na nemo asabe takawoni gdn,
nan fah yaci gb da bani lbrn irin wahalar  nemana da yayi har muka isa kwararon gidan mu da yake gurin mota bata shiga nan yayi parking ya dube ni jikin shi duk yayi sanyi,
Ni kuwa qirjina dukan 3 3 kawai yake cikin qarfin hali yace,
" gashi har mun kawo gd amna bakice kin yafe mun ba,
Kwallar da ta taru ido na ta sauko cikin muryar kuka nace,
" na yafe ma amma ina rokonka abu daya,"
Ina jinki ya fada a kasalance,
Kayi alqawarin ko miye zakayi,
Batare da ya damu da komai ba yace nayi alkawarin ko miye xanyi idan dai har xai saki farin ciki,
Na danyi yaqe tare da cewa,
" ina so ka ajiyini daga nan in shiga gida kuma bana so ka rakani bakin gida saboda bana son iyaye na su ganni tare dakai kuma ina rokonka da Allah kada kaxo nemana a gidan mu ko da wasa ne,
abunda ya hadani dakai da ganan ya qare Allah yasake sada fuskokin mu a aljanna,
Kuka yaci qarfina na bude murfin motar na fito da sauri,
Farouk yayi saurin tarar gabana yana rokona da in saurare shi inji me zaice,
Zuciyata ta rufe baxan iya tsayawa ba juyowa kawai nayi tare da cewa Alkawari fah kaya ne,
Yayi turus ya tsaya tare da dafe kai hakika da yasan hk xata mishi da baiyi saurin cewa yayi ba amma kuma ba ynda ya iya dole ya hakura sbd yasan muhimmancin alqawari,

Cikin wani irin matsananci sauri naga na shanye kwararon gidan mu nashiga wani wanda zai sadani da gidan babban dalilin da yasa nayiwa faruk hk nasan matukar mukaje tare dashi gida to inna wuro bazata barni na zauna ba sai tayi maqar qashiyar da tasa ya koma dani ni kuwa ynda na tsane mutuwata haka natsane xamana qarqashin wani a matsayin boya,
Qara duk azabar da xangani gun inna wuro inganta tunda nasan gdn ubana ne,

Faruk kan yafi minti talatin tsaye dafe dakai dakyar ya iya daga kafar shi yashiga mota  nan ma kasa jan motar yayi sai kawai yakife kanshi a sityari yana kiran sunan Allah yafi awa daya sannan ya tada motarshi yayi gidan kanwar mahaifin shi dake zaune nan garin kano dan ya dan samu ya huta abin haushi sai yataradda gidan a rufe sai a lokacin ya tuna da suna gidan su na kaduna,
Cikin rashin kuzari yaja motarshi yakama hanyar komawa inda yafito

              52
Lokacin da  nakawo bkin gida wani sanyi naji hade da bugun zuciya kirjina yayimun nauyi gabana sai faduwa yake kafafuwana kuwa dakyar ma nake taka su saboda tsananin tsoro da fargabar tunkarar inna wuro,
Sunan Allah kawai nake ambata cikin raina,
Da sallama nashiga cikin gidan cikin rashin sa'a kuwa duk suna tsakar gidan bama babban tashin hnkli irin ido biyun da nayi da Asabe xaune da jaka a gabanta da alama tafiya xatayi,
Gabaki dayan su juyowa sukayi suka zubamin ido sunamin kallon mamaki cikin karfin hali nakarasa gurin su nazube qasa ina gaidasu,
Inna wuro ta doko salati tana fadin wa nake shirn gani haka a gidannan?
Bayan kinje kin qare yawon iskancin ki xakixo min gida ki xauna ai wlh baki isa ba qila ma wani  abun kunya kika kwaso  kika xomin gida toh bari kiji tun wuri ma ki kama gaban ki don bakida gurin xama a gidan nan don bazan zauna da karuwa ba,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.
Hakika kalaman da ke fita bakin inna wuro  jin su nake tamkar ana yanka naman jikina,
Ban san lokacin da na fashe da kuka ba ina fadin wlh banje ko ina ba su suka kor........,
Bugemun baki tayi tana cewa qarya kike mutanen da har gida sukaxo neman ki xakiwa qazafi kice korarki sukayi,
ynx haka ma su suka turo asabe tazo tagani ko kin dawo,
Dama nasan ai don  kimin bakin ciki kika gudu ki kabar gidan ai angayamin ma saurayi kikabi ynx don shima ya gaji dake ya koroki xaki tunkaro ni toh qaryarki tasha qarya wlh diyar mahaukata,

Nikan kuka kawai nake nama kasa samun kalma daya da zanfada saboda jin wannan qazafin da inna wuro kemun,
Asabe daketa kallona tun randa na shigo  da alama murna ta kasheta
tace,
Baxa ayi hk ba wuro ynx dai ki saurara ayi  magana,
Ke muhibbat share hawayen ki muyi magana kinji,

Ayshart farouq

Excellent writers

©Ayahart one©
[5/11, 10:24 AM] KAURA: Damuwata
         
           53
Tafin hannuna nasa nashafe hawaye na tare da rakubewa gefe don Jin makomata jamila ko da adawiya ko wace fuska tasha mai sun qara gogewa  abinsu cikinsu ba wadda na isa ko kallon banxa dariyar su kawai suke suna shewa tare da qara xuga inna wuro,
Asabe tayi gyaran murya tace,
" ynx dai sai mugodewa Allah da yasa yarinyar  tadawo gida dama shine abunda ya maidani garinnan saboda hjy Ameena ta matsamin akan yarinyar yanx hk ma takanas Ta kano  ta tadoni don inxo ingani idan muhibbat ta dawo gida idan kuwa bata dawo ba inje insamo mata wata mai irin halin muhibbat saboda tun lokacin da tabar gidan  na tsawon wata daya yarinya biyu suna daukowa suna barin gidan ynx hk ma wata ce wadda ke musu shara da yan goge goge amma bata dafa dafa musu abinci sbd kamana ce hajiyar tayi iya kokarinta mijin ta yabari ta dauko namiji mai dafa abinci yaki yadda acewar shi wannan ba tsarin shi ba ne,
Yaranta kuwa malalata ne basa iya barkatawa kansu komai dan hk ynx tunda Allah yasa muhibbat din tadawo sai ta tashi mu kama hanya yanxunnan mu koma kar dare yayi mana a hanya ko ya kika ce wuro,
Inna wuro ta tabe baki tace,
" karma taje din idan bataje ba  wlh ina mai rantsuwa da rayuwata baxata zaunamin gida ba  sai dai ta neme wani guri daban ta zauna, amma dai kan ba nan gidan wuro ba.
                
                  54
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un itace kalmar da nake fadi a zuciyata,
Wannan karon hawayena ma kafewa sukayi narasa kalar kukan da zanyi,
Hakiika banyi tunanin xan taradda haka ba a gidan ubana,
wata zuciya tace kiyi hkr muhibbat ki tashi kibi asabe wannan itace kaddarar ki hakika Allah s w t Allah yana cewa inna ma'an usurun yusura ma'ana duk inda tsanani yake
yana tare da sauki,
Allah yayi gsky hakika dukkan tsanani yana tare da sauki,
Nabarwa ubangiji lamurrana saboda shi yasan abunda ke boye da bayyane ,
Bazan taba ja da ikon shi ba tunda hk ya rubuta rayuwata xata kasance tun kafin inxo duniya,
Lokaci daya naji Allah ya yayewnun duk wani kunci a zuciyata sai ma nariqa ganin wautar kaina da na matsawa faruk yamaidoni gida gaban iyayena na manta cewa ni marainiya ce banida wasu iyaye da xasu ganni suji sanyi banida wasu iyayen da zanyi kuka a gaban su in basu labarin azzalumin da yayi yunkurin wargaza tarbiyar yarsu da roshe rayuwarta ta hanyar  rabata da mutuncinta.
Wannan karon wasu hawaye masu xafi suka fitomin nasanya bayan hannuwana na goge tare da maida hankalina kan maganar da inna wuro keyi,.


Ayshart farouq

Excellent writers

©Ayshart one©