[11/23, 6:14 PM] Ayshart one💞: Damuwata
Na
Ayshart Farouq
61
Bayan kwana biyu da faruwar haka ina guarding zaune tare da hotunan mahaifiyata kasancewar yanxun Ina yawaita mafalkinta yauma da asuba nayi mafalkin ganinan kwance kan cinyarta tana min tsifar Kai.
"Allah sarki"
Nafada tare da kai hoton bakina na sumbata, ban Ankara ba sai ji nayi an zafce hoton daga hannuna
Cikin sauri na daga idanuwana don ganin ko waye,
Sai dai kallo daya namishi na sunkuyar da kaina qasa Ina wasa da yatsuna,
Zama yayi daf Dani yana cewa,
" KO su waye acikin wannan hoton da gani suna da muhimmanci a gurinki"
Ni kuwa da tun tuni kamshin turaren shi yayi awon gaba da tunanina banma ankara ba saida naji ya kira sunana
" muhibbat"
Nayi saurin karbawa da
" uhum" tare da kara matawa gefe,
Bai damu da kara matsowa ba yaci gaba da magna,
" ranar sai kika gudu kika barni ko?"
Ya fada tare da zubomin ido,
Bance komai ba kaina a kasa Ina wasa da yatsuna.
Bai jira nayi magna ba yaci gaba da cewa,
" me yadawo dake gidannan?"
Idanuwana suka kawo kwalla nace,
" gida aka dawo dani"
Dan matsowa yayi kusa dani,
" me yasa aka dawo dake kuma Wa yadawo dake?,"
Wannan karon kam fashewa nayi da kuka ba don banida amsar tambayar ba sai dai don ban san ya zan amsa mishi tambayar ba,
" subhanallah" ya fada
" muhibbat miye abun kuka anan? Ko dai ke don kuka bai miki wahala ne plz kiyi shiru ki amsamun tambayar da namiki ko Allah nasa inada taimakon da Zan baki I don't want see you cry pls ki share hawayin ki, ki fada min matsalarki" yafada tare da mikomin handki
Ban karba ba nasanya hannuna nashafe hawayen amm kuma bance komai ba,
" uhum inajinki gayamin"
Cikin rawar murya nace,
"Ba komai ni nadawo da kaina"
Na fada tare da mikewa Ina shirin in wuce ban ankaraba sai ji nayi ya jawoni da karfi yana cewa,
" ba gskiya ba ne, kin San Allah baxaki bar gurinnan ba sai kin fadamin matsalarki,
Su waye nan a pic dinnan?,"
Idanuwana suka kawo kwalla inata neman in kwace hannuna in gudu amma Ina qarfi ba dai ba
62
Cikin muryar kuka nake cewa,
"Dan Allah ka sakemin hannuna Allah fah ya hana,"
Kallona yayi ido cikin ido zan sakeki amma sai kinyi alkawarin bazaki gudu ba,"
Cikin sauri nace " eh baxan gudu ba sake ni"
Ai kuwa yana sakina nayi wuf Zan gudu, ba zato ba tsammani naji ni kan kirjinshi,
Innalillahi wainna ilaihirraji'un "wannan wace irin musiba ce?"
Kuka kawai naashe dashi amma ko a jikin Farouq saima Kara kankameni da yayi yana bubbuga bayana alamar lallashi.
Don kanshi ya sakeni tare da zaunar dani yana kallona,
Cikin wata kasalalliyar murya yayi magana
" oya bani labarinki inajinki"
Ganin babu sarki sai Allah yasanya nakwashe tarihina duka nagayamishi,
Kanshi ya dafe tare da hannayenshi idanuwab shi sunyi jajur tamkar garwashi, dubana yayi tare da cewa,
" wannan hoton fah?"
Atakaice nace,
" hoton mahaifiyata ne tare da yayarta,"
Kallon hoton yayi sosai yana jujjuya shi,
" wannan hoton ai yayi tsufa da yawa fuskokin suma basu fito sosai ba,"
" uhum" kawai nace don Allah kadai yasan yanayin da nake ciki gashi na matsu yabar gurin ko don gudun abunda kanje yadawo,
" me kike tunani ?" Naji yafada cikin sarkakkiyar murya,
"Ba komai" nafada tare da mikewa, " zan wuce ciki inada aiki," na fada kaina a qasa a tunanina zai bani hoton sai kuma naga yasanya shi cikin aljihunsa ya dubeni yana murmushi " idan kina son hotonki kizo nan gobe bayan la'asar ki karba Ina jiranki,"
Bance komai ba juyawa kawai nayi nawuce abuna tamkar Zan fadi sabida tsabgegen saurin da nakeyi,
a raina kuwa sai cewa nake, " ai wlh bazaka ganni ba haka kawai mutum na nema ya jazamin bala' i Allah yamin tsari dakai da kuma dukkan sharrin ka,"
Har na isa gida abunda zuciyata ke rayamun kenan,
Shi kuwa Farouq tunda ta wuce yakasa daina kallonta Alla kadai yasan abunda yakeji game da yarinyar wani abu yakeji Wanda bai tabajin kwatan kwacin irinshi ga kowa ba,
Tsantsar tausayinta ne ya sake dabaibaye mishi zuciya,
" I will help you muhibbat, Zan taimakeki matukar Ina raye Zan fitar dake damuwarki da yardar ubangiji. shi kadai yake magana kamar wani zarrare.
©Ayshart one ©
[11/23, 6:14 PM] Ayshart one💞: Damuwata
Na
Ayshart Farouq
63
Ni kuwa tun ranar nashiga wasar boyo dashi duk wata hanya da nasan zata sadani dashi gudunta nakeyi,
Misalin karfe biyu da rabi na rana inata hada hadar hada lunch hajiya da nusaiba ne zaune fira suke kasa kasa,
Nusaiba ta dube momyn ta tace,
" kinga fadeela ansamu shiga gurin yaya Farouq tun dazun take gurinshi da alama yau na kwaran nanan,
Hajiya tace, " ai yanxu kwana biyu naga chanji sosai a tattare dashi game da fadilar tunda har yana tsayawa suyi fira,"
" dama ai miskilanci ne kawai irin na yaya Farouq yana so yana Kai kasuwa" dukansu suka kwashe da dariya,
Suna cikin cin abincin ne fadeelah ta sauko fuskarta ba alamar fari'a,
Nusaiba ta dubeta cikin tsokana tace,
" kaga sis ansha soyayya anxo Ana wani daddaure mana fuska,"
Dan murmushi tayi kadan tare da kwalamin kira ,
" muhibbat"
Cikin sauri naxo Ina cewa "gani,"
Harara ta watsamin sannan tace, " kije kije ki hadawa ya Farouq lunch dinshi sannan kuma ki dafa mishi ruwan zafi masu kayan yaji don yanajin zazzabi,"
Tana fadin haka tasami gurinan ta zauna tana cewa,
" momy ya maganar fitar zamunje ko sai goben?"
Banji amsar da tabata ba natafi naci gaba da aikin hada mishi lunch din, amma harga Allah saida naji gabana yafadi da nasan yanda zanyi kada naje da nayi don kar in hadu dashi,
Koda nadawo su nusaibar kawai ne natara fadeela taariga ta koma sama gurin Farouq din.
falon nasame su zaune suna fira sanye yake da dogon wando da singlet, kasa yake zaune kan kafet yadan jingina da kujera tare da pillow remote ce hannunshi yadan fada yayi duhu,
Fadeela kuwa tana zaune kusa dashi sai zuba mishi surutu take da kissa da kisisina
" Assalamu alikum"
Nayi sallama cikin rawar murya don harga Allah a tsorace nake,
Shi kadai ya amsa a ciki sabida muryarshi bata fita sosai fadeela kam harara ta watsomin tare da nunamin inda Zan ajiyewa da sauri na qarasa gabansu na ajiye ganin duk a kasa suke yasanya na ajiye musu a kasan,
" oya yi saving dinmu "
Fadeelah ta fada tana kallon Farouq da tun shigowata idanuwan shi suke kaina,
" dear ka lallaba kaci duk yanda yake kaji"
Ta sake a fada cikin shagwaba,
" ok"
Kawai yace tare da danyin murmushi yana dubanta dadi kawai takeji tasamu kan Farouq batasan tana kasa tana dabo ba
64
Da sauri na dauke plate da saving spoon Dan zuba musu abincin amma kwata kwata nakasa sabida tsabar rawar da hannuna keyi,
Tsawa ta dakamin " ke wai miye haka ne?"
Saboda tsoro banma San spoon din ya subuce hannuna ba ya fadi kasa idanuwana tuni sun cicciko da kwala,
" kinga fadeela ni fah abincin ma yafita raina bazan iya cinshi yanxu ba"
Farouq ya fada cikin daure fuska,
Idanuwa ta gwalo mishi "haba ya Farouq me kace ne da zakace bazakaci ba yanxu?"
Yace,
" ba komai kawai dai banajin cin abincin ne yanxu"
Hannuna kawai ya mikomin tare da karbar saving spoon din hannuna, yana cewa " kinga Bari inyi saving dinki da kaina idan zakici,"
Cikin bacin rai tace,
" nima na koshi"
Tabe baki yayi tare da zuba Mata ido ganin yanda taketa cika tana batsewa,
Wani kallo ta watsomin tare da yimin tsawa,
" don ubanki tashi ki bacemin da gani tun kafin inyi ball dake kazamiyar banza,
Kwallar da naketa makalewa ban San sanda ta fito min ba,
sumui sumui na mike ha nakai bakin kofa naji ta sake dokomin Kira, da sauri nadawo kaina a kasa naji tace,
" jeki ki gyara Mai dakinshi ki wanke toilet din"
Banko dube su ba na wuce dakin domin gabatar da abunda ta sani,
Direct toilet naje nawanke shi tsabal sannan nadawo dakin shima nagyara shi sosai sanna nafita,
Ga mamakina sai na same Farouq shi kadai a falon zaune kan kujera,
Gabana faduwa kawai yake kafafuna kuwa sai sasarfa suke tamkar Zan fadi,
" muhibbat" ya kirani can qasan makoshin shi, tsayawa kawai nayi ba tare da naje ba kuma ni ban wuce ba,
Fuskar shi tamke yayi magana,
" zo ga hoton ki"
Ya fada yana mikomin hoton ko alama fuskarshi ba alamar wasa kwarjinin shi ya bala' in qara fitowa ganin yanayin fuskar ne yasa nayi saurin karasawa don ko ba komai Ina matukar bukatar hoton,
Da sauri na mika hannun don in karba kawai sai ji nayi ya chafke min hahannuna.
©Ayshart one ©
[11/23, 6:14 PM] Ayshart one💞: Damuwata
Na
Ayshart Farouq
65
Fuskar shi a marairaice Yake magana tamkar bashi ba,
" plz muhibbat ki sauna muyi magana Dan Allah I have no one to advise me i am badly need of you help buh idan kina ganin kamar wani abu zanmiki bazan takuraki ba zaki iya wucewar ki don bana so inshiga hakkinki " ya fada tare da sakemin hannu ya lumshe idanuwanshi jikinshi duk ya mutu bashida wani kuzari a tattare dashi.
Ganin yanda yake ne yasanya nima jikina ya mutu duk tausyin shi ya kamani nan take naji bazan iya tafiya inbarshi a halin da yake ciki ba,
a hankali na furta
" Ina tsoron wani yazo ya sameni a nan,"
Har yanxu idanuwan shi a lumshe suke tamakar maijin bacci,
Cikin wata kasalalliyar murya yayi magana " ba kowa a gidan duk sunfita "
Jin haka ne yasanya hankalina yadan kwanta a wani gefe wani gefen kuwa a tashe yake.
Cikin sarqaqqiyar murya nace,
" inajin ka how can I help u?"
Da sauri ya bude idanuwan shi yana dubana,
Murmushi yayi tare da lasar leben shi na kasa da ya bushe,
" zauna a nan" ya fada yana nunamin kujerar da take kusa da shi,
Batare da nakalle shi ba na nemi guri nan qasa na zauna tare da takure dukkan jikina da kagganni kasan bana cikin nutsuwa,
Shima kasa yadawo ya zauna tare da jinginawa kan kujera,
" mikomin pillown can yayimin nuni da da pillown da nasame shi kwance a Kai,
Hannuna kawai na zula na miko mishi ya aza don yaji dadin jinginawa da kyau,
" muhibbat" ya Kira sunana yana kallo na,
Kaina a kasa na furta
" na'am Ina jinka"
Wani dan huci yayi tare da furzar da iska mai zafi,
Sannan yace,
" nasan dai kinada labarin auren dolen da ake so a min ko?"
Da sauri na dago kaina muka hada ido dashi nasake yin kasa da kaina a raina nace,
" Kama raina mutane Farouq ni xaka cewa baka son fadeela this is not possible "
" it is muhibbat wallahi bana sonta ko kadan"
Da sauri na dubeshi Ina zare ido Ashe a fili na fada,
Gyada min kanshi kawai yayi alamar da gaske yake,
Sannan yaci gaba da maganar shi
" na dauki fadeela tamkar yanda na dauke Nusaiba wallahi tallahi beside dis I don't have any filling about her,
Bantaba jin sonta ba koda na second daya ol i know tsanar da nake mata da ta wani dalili yanxun nadaina sabida nasamu abunda da nake ganin tamkar ita ce silar da narasa shi, a gsky idan aka auramin ita Zan cuceta in kuma cuce zuciyata ban San ya zanyi ba abubuwa sunmin yawa a zuciya am very sure nasan inada rauni a zuciya na plz tell me wat should I do"
66
Idanuwan shi sun rine sunyi jajur can ciki har wata kwalla kake hangowa wadda gwarzon namiji ne kadai ke iya riketa,
Yaban tausayi matuka dukda har yanxu ban gasganta magabarshi ba,
Kaina a kasa nace,
" shawarata daya kayiwa iyayenka biyayya kayi abunda suke so idan dai har kana so kaga dai dai a rayuwarka"
Kallona kawai yake ko kyaftawa bayayi, nan take ni kuwa na
dabirce ba shiri nayi shuru,
" uhum inajinki muhibbat,"
Cikin inda inda nace,
" shi kenan dama"
Murmushi yayi tare da sanya hannayen shi duka biyu ya rike fuskar shi, saida yayi kusan minti biyu a haka sannan yayi magana,
" muhibbat yunwa nakeji bani abinci inci"
Abincin da nakawo mishi yana nan inda yake shi na jawo na zuzzuba mishi ganin har yanxu fuskar shi na cikin hannayen shi ne yasan ya nace,
" ga abincin nan ni Zan wuce"
Da sauri ya dago ya kalleni " no ba yanxu ba ban kare magana ba"
Mika mishi abincin kawai nayi tare da zuba mishi ido,
" xo mu ci" ya fada yana kallo na,
Da sauri nagyada mishi Kai alamar a'a,
Bai sake cewa komai ba saida yayi kusan spoon biyar sannan yace,
" nadade banci abinci ba ko na dauko zanci kasawa nake saboda tunani yamin yawa ko yanxu da ba don ke ba da baxan iya ci ba"
Duk maganar nan da yake bai dubeni ba abincin shi kawai yake ci,
Ni kuwa kallon shi kawai nakeyi don bansan inda zancen shi ya dosa ba,
Saida ya cinye abincin tatasa sannan ya dubeni yayi murmushi bani ruwa a fridge mikewa nayi nadauko ruwan inata mamakin yanda ya cinye abincin nan shida bashi wani cin abinci,
Mika mishi ruwan nayi ya sha tare da yin hamdala sannan ya koma ya gincira yana kallona yana murmushi,
Nima wannan karon murmushin nayi Wanda bansan lokacin da ya subucemin ba.
67
Ci gaba farouq yayi da maganar shi kamar haka,
" naji shawarar ki nagode kwarai Allah yasaka miki da alkhairi amma kin San wani abu?"
Girgiza kaina nayi alamar a'a,
" zan fah iya rasa rayuwata idan ban mallaki wadda nake so ba bantaba soyayya ba sai akanta nasan so nasan minene so wallahi rasata a gareni ba karamin tashin hankali ba ne bazan iya rayuwa ba tare da ita ba"
Ya karashe maganar cikin sarkakkiyar murya,
" subhanallah! Wannan fah bai dace dakai ba Sam bai kamata ka rika irin wadan nan magangan nu ba duk Dan Adam yanada tashi kaddara ko Mai kyau ko mummuna kuma yarda da wannan kaddarar imani ne so kga irin wadannan magangannu basuda amfani sai ma su sanya mutum yarasa imanin shi dama a rayuwa ba dole ne mutum yasamu abunda yake so ba"
Shikan Farouq mutuwar zaune yayi gurin kallon muhibbat
" wai ashe tana magana haka? ashe tanada ilimin tauhidi a haka?,
Ya subhanallah!" Ya fada a fili
Da sauri na dago na dubeshi tare da mikewa
"nikan Zan wuce kawai ayukkan da zanyi da yawa"
"Tsaya kiji mana" ya fada kanshi a kasa,
" meyasa baki tambaye ni KO wace yarinya ce nakeso da yawa haka ba?,
Bansan lokacin da nasamu bakina da cewa,
" saninta bahida amfani a gare ni"
Na fada Ina duban shi,
" a'a muhibbat kada muyi haka dake ni inaso kisanta saboda ki taimakamin gurin neman soyayyarta coz har yanxun ma ita batama San inayi ba,"
Bansan ya akayi ba na tsince kaina da faduwar gaba ba kalaman shi sun bala'in dagamin hankali ba kamar da nagan shi ya mike ya matso daf Dani,
" plz muhibbat Dan Allah ki taimaka min ki taimaka min ki gayawa zuciyar ki cewa Farouq yana tsananin kaunarta wallahi muhibbat ina son ki I don't know what to do I just can't live without you plz ki taimakamin don girman Allah,
Ni kam tun sanda yafara maganar shi nake kuka
" innillahi wa'innan ilaihirraji'un na fada tare da ja baya ganin yanda kamannin shi suka chanja baki daya,
" nashiga uku Dan Allah kayi hakuri kada kamin haka wayyo Allah na ni marainiya ce banida kowa banida komai,
Kukan yaci karfina sosai shiyasa na ruga da gudu nabude kofa nafita tamkar raina zaifita don kwata kwata bana ganin gaba na,
Su hajiya naci Karo dasu baki dayansu tambayata suke lafiya suna jijjigani cikin tsananin tashin hankali,
©Ayshart one©
08100376392
Www.ayshartfarouq.blogspot.com
No comments:
Post a Comment