55. Tana cewa kima tashi ki wuce yanxu nan tun
kafin zuciyata ta rufe na balaki don ganin ki ma
zai iya haifar min da Hawan jini Asabe tace ai ba
za ayi haka ba kidai barta ta Qara hutawa Ko
xuwa ayi la'asar ne sai mu hau hanya da kyar
inna wuro ta yarda mukayi la'asar Bayan mun
kare sallar ne ta jefomin wani album tsoho duk
ya lankwashe ya murde tana cewa ga tsiyar ki
nan danagani Cikin Kayan mahaifin ki a sauka lfy,
hannuna har ruwa yake na dauka nasaka a jakata
ba bata lokaci muka isa Tasha jikina kuwa yayi
xafi sosai dama tun gidan inna wuro nake jin
xaxxabi naso ya kamani ga Kaina tamkar ya
tsage saboda ciyon da yake mun Ita kanta
Asaben ta fuskanci haka don har maganin
xaxxabi ta saimin kafin motar mu ta tashi,
Wannan karon bacci bai daukeni ba idanuwa
kawai na xubawa hanya Ina kallon sarautar
ubangiji a raina kuwa sai tasbihi nake Ina bode
wa Allah da yabani sadakar rayuwa, sai a lokacin
na tuna album din da inna wuro ta bani nayi
saurin jawoshi Cikin jakata ina duddubawa
hotona ne da yawa aciki sai dai duk sun lalace
saboda ruwan da ya taba su hotona biyu ne
xuwa uku basu lalace ba na mahaifiyata Allah
sarki isma'il na fada ganin hoto biyu da nagani
Wanda Ada inada su don baxan taba manta
randa ya karbesu ba a cewar shi xaije asibitoci ya
bincika min mama na hoto daya Ita kadai ce tun
tana karama kafin tayi aure Dayan kuma itada
yayar ta ne shima suna qanana sai Dayan da
nagani ynxu Wanda suka dauka su da yawa da
alma duk familyn su ne,Allah sarki isma'il Ko
kana ina ynx? Wata zuciya tace Kila ma ya manta
da ke anya kuwa isma'il xai iya mantawa da ke
duk Irin hallacin da yamiki? Gaskiya bazai iya
mantawa dake ba Inji wata zuciyar Nima Kaina
nafi gasganta ta. Asabe ta katsemun tunani da
cewa toh sarkin tunani yau ba bacci ko jikin ne
kike ji na gyda Kaina alamar a'a taci gaba da
cewa ni dai muhhibbat ina baki shawara da ki
rage yawan tunani ki daina sanyawa kanki
damuwa sauki Yana tare da tsanani Mai hankuri
yakan cimma dadi Kowa kika gani duniyar nan
Akwai abunda ya dame Shi. Ni dai kallon Asabe
kawai nake ashe ta iya xantukka masu dadi haka
tayi ta yimin nasifa da bani shawarwari har bacci
ya kwasheta nikn wannan karon idanuwana biyu
har muka isa garin kaduna
56
Wannan Karon idanuwana biyu har muka isa
garin kaduna koda muka isa Anata kiraye kirayen
sallahr magriba taxi muka dauka har bakin gidan
ras! Naji gabana ya fadi sai nasame bakina da
karanta bismillahi harajna wa bismillahi
walajnawa ala llahi rabana tawakkalna.
Kasancewar Ana sallahr magriba ne yasanya
muka tsaya nan falon qasa muka gabatar da
sallolin mu har xuwa isha'i sannan muka doshe
head quarter hajiya
Xauna take tana kallon news fadeela na
kishingide tana dannar waya mukayi sallama
muka shiga dakyar ta iya buda baki ta amsa
sallamar dukkan mu xubewa mukayi muka
kwashe gaisuwa,
Ta tabe baki ta dube asabe tana cewa ''ai na
dauka ba xakixo ''
Asabe ta washe baki
" ni as wa da baxan dawo ba mota ce dai tayi
wuya,"
Takai dubanta gareni " ke kawai sai kika gudu
bayan Kinsan nabiyaki kuddin ki nawata daya tun
wata na 15 baki Ida Aiken ki ba kika gudu Kinsan
idan naso kamaki da wannan laifin xan iya ko."
Gyada kaina kawai nayi tare da cewa
"ayi hkr kuskure ne,"
Ta yatsine fuska taci gaba da kallon ta batare da
tace komai ba,
Asabe tace " dan Allah hajiya kiyi Hakuri da duk
abunda Ya faru mahaifiyar ta tayi bakin ciki
matuka da komawara ta gida batare da sanin ki
ba, da tarema xamuxo tabaki Hakuri sai kuddin
motar suka kakare mana amma tace dan Allah
kiyi Hakuri ki karbe muhibbat kuma kimata duk
hukuncin da kikaga yadace da ita amma dan
Allah kada ki kureta daga gidan nan domin ke
kadaice gatan su,"
Idanuwa kawai naxubawa asabe Tana shatata
qarya cikin Raina cewa nake wasu mutane basa
tsoron Allah ji yanda asabe ke karaya Bako
tsoron Allah saboda Neman duniyanan
57
Hajiya kam maganar ta mata dadi ta qara
tabbatar da yarinyar ba Iowan kowa ba ce, amma
a zahiri sai Tamara bata fuska tare da cewa
" Ai ni tune na Hakura da muhibbat tunda ba ita
kadai ke iya kulamin da gida na ba don hk ki
dauke ta kawai ki koma da ita nagode"
Wani irin dadi naji hade da sanyi cikin Raina .
57
Hajiya kam maganar ta mata dadi ta qara
tabbatar da yarinyar ba Iowan kowa ba ce, amma
a zahiri sai Tamara bata fuska tare da cewa
" Ai ni tune na Hakura da muhibbat tunda ba ita
kadai ke iya kulamin da gida na ba don hk ki
dauke ta kawai ki koma da ita nagode"
Wani irin dadi naji hade da sanyi cikin Raina .
Asabe ta qara kekashe Murya tare da qara
kaskantar da Kai tanaba hajiya hakuri kan tabrni
inci gaba da aikina,
Rokon Allah nake tayi Allah yasa kada ta Hakura,
Muryarta na tsinkayo tana cewa,
"Toh shi kenan na Hakura amma da sharadin duk
ta sake aikata laifi makamancin wannan xatabar
gidan nan har abada,
Wannan shi ake Kira da adake ka a hanaka kuka
bansan lokacin da hawaye masu xafi suka
xubomin ba Jin wannan maganar ta hajiya take
sai naji hankalina Ya sake tashi ganin nusaiba ta
shigo harda takemun kafa tana cewa,
"Momy Biko kikayi ashe?,"
Fadeela ta karbe da cewa ,
"Ai Kinsan momy bata iya xama sai da wannan
aljanar,"
Duk suka sanya dariya suka taba,
Saida ta sake gindaymin dokokin gidan da
sababbin yan aikin da suka samu sannan sukayi
sallama da asabe ta wuce gidan da take xama.
Haka rayuwa taci gaba da kasancewa cikin
wahala da tsangwamar hajiya da yaranta Yau
Kusan satania biyu da dawowa gidan amma ban
sanya Farouk a Ido na ba hakan ba karamin dadi
yayi mun.
Kasancewar Yau asabar misalin karfe 9 na safe,
sanye nake da wani material da anty hajara ta
dunkamin blue mai ratsen fari dunkin Riga da
sikert Kayan na matukar karbata ko ba komai
xamana gurinta na samu wata wayewa ta daban
jikina kanshi Ya chanja saboda mayukkan da
tasaimin har ynx inada Sauran su, su nake
shafawa karamin hijabi fari na sanya inata
kokarin hada breakfast kan dinning hajiya da su
fadeela duk suna xaune suna Fira ,
Cikin nutsuwa nake jido kaya daga kitchen xuwa
dinning area,
Fadeela ta dube nusaiba tace,
" dadina da talaka bai iya samun guri ba"
Cikin dariya nusaiba tace,
" au dama sai ynx kika sani.,"
"Toh naga aljanar yarinyar ga duk ta chanja ni
fah abun har tsoro Yake bani sai wani fresh take"
" tunda ta dawo na lura da haka har maganar
naso na miki sai kuma na manta,"
" ai kuma kunsan daganin hk ba banxaba don
asabe ta cemun da tabar gidan nan ba gida taje
ba saida suka tsananta addu'a da rokon Allah
sannan ta koma gida, mudai Allah yasa ba a debo
muna mugun Abu ba " inji momy,
Duk suka karba da ameen,
Shigowar Farouk ce falon ta katse firar,
Gabana yayi mummunan faduwa lokacin da muka
hada Ido da Farouk,
Shi kanshi ba karamar rudewa yayi ba da kyar
ma ya iya hada kalmar,
" momy Ina kwana"
Cikin fari'a ta karba yayin da su fadeela suka
gaishe shi suma cikin girmamawa ,
Baimaji gaisuwar suba saboda kwata kwata
hankalin shi baya gurin su har saida suka sake
maimaitawa,
Ni kan tune na dauke idanuwa na naci gaba da
xuxxuba musu abincin ,
Farouk kasa Hakura yayi saida yayi magana,
" momy yaushe kika dawo da yarinyar nan ne"
" Kusan satin ta biyu " ta bashi amsa ,
Baki daya kasa cin abincin yayi sai satar kallo na
Yake,
"Momy tace,
"Lafiyar ka Kuwa katasa abinci gaba kana kallo?",
Mikewa kawai yayi tare da cewa,
"Banjin dadin jikina ne,
"Eyya inji ba xaxxabin ba ne?"
" no kaina ne kawai ke ciyo xanje asibiti ynx ba
dadewa xanyiba ynx xandwo Sai inci abincin"
" da ka daure kaci ko kadan ne sai kasha
magani"
"Xan sha tea idan naje daki",
Har ya juya kuma sai ya dawo yace,
Idan yarinyar nan ladidi taxo kisa ta gyaramin
kayana da aka kawomin jiya suna falo waste,"
Ta karba da cewa,
"Ai na maidata gida jiya, ga dai muhibbat nan
idan ta qare aiki xata gyarama, baice komaiba Ya
haura sama a abinshi amma yaji dadi har cikin
xuciyar shi,
Wuraren qarfe goma na kammala ayukkan hajiya
ta sake nanatamin inje ingyarawa Farouk dakin
shi,
Ba tare da bata lokaci ba na nufe dakin shi
gabana sai dukan uku uku Yake......................,
58
Da sallama nashiga dakin ba kowa sai sanyi a.c
da daddadan kamshin turaren dake tashi a ciki
komai tsare very neat,
cikin raina nace har ynx wannan tsaftar tananan
ba tare da bata lokaci ba nashiga bedroom dinshi
nan ma komai a tsare,
kayan ne kawai da ya karbo gurin wanki cikin
katuwar jaka zube kan gado,
sai drowar dake bude wadda da alama yana cikin
aikin jera kayan ne ya ajiye ya fita.
batare da fargabar komai ba na shiga zazzage
kayan ina jerawa a cikin drower din,
kaman yawa ne dasu shi yasa na dauki tsawon
lokaci kafin in kare,
bayan naqare Ina cikin gyran gado naji anbude
kofa anshigo ansake yiwa kofar key anyi locking
dinta,
a razane na juyo don ganin kowaye ko ban fada
ba nasan ko waye idanuwan na da nashi suka
sarke guri daya,
nayi sahrin saukar da idanuwa na kasa tare da
maida hnkali na kan gyaran gadon da nake
shi bai shigiba kuma baiyi magana ba hannayen
shi kawai ya harde a kirjin shi ya zubamin
matsakaitan idanuwan shi masu tafiyar da
nutsuwar mutum,
kasa juyawa nasakeyi badon ban qare gyaran
gadon ba sai don gudun sake hada idanuwa da
farouq,
ganin bashida niyar barin gurin yasa na juyo tare
da sunkuyar da kaina a kasa,
cikin raunanniyar murya nace,
" Ina kwana"
bai amsaba saima sakin kofar da yayi ya nufato
inda nake,
nan take jikina ya hau rawa na runtse idanuwana
tare da make hannayena a kirjina,
saida ya kawo daf dani yazamana har Ina iya jin
nunfashin sa da bugun zuciyar shi,
cikin muryarshi Mai dadin sauraro yace,
" bazan karba gaisuwar ki ba muhibbat"
idanuwana sukayi raurau tamakar Mai shirin
fashewa da kuka,
a hnkali nayi saurin durqushewa a qasa Ina
maida nunfashi Allah ne kadai yasan abunda
zuciyata take saqamin,
biyoni yayi a qasa shima tare da kiran suna na "
muhibbat"
wani yar naji a jikina saboda yanda yafadi sunan
sai naji kaman duk duniya yafi kowa iya fadin
suna na,
" muhibbat"
yasake cewa a karo na 2,
hawayen da naketa maqalewa suka zubomin,
" oh my god"
ya fada
" baba muhibbat meyasa zakiyimin haka meyasa
zakimin kuka a lokacin da nake muradin ganin
murmushin ki me yasa kika boyemin kanki a
lokacin da nake buqatar ganin ki muhibbat me
yasa kikaqi zuwa ki taimakamin a lokacin da
nake neman taimakon ki?"
kaina ya daure narasa gane me kalaman farouq
suke nufi,
tausayin kaina ya kamani take na sake fashewa
DA kuka tare da cewa,
" don girman Allah farouq ka budemin kofa in fita
"
mikewa kawai yayi tare da komawa kan gado ya
zauna baki daya tunanin shi yatafi wata duniya ta
daban wadda bata mutane ba,
wata rayuwa yake hangowa mafi dadi DA tsanani
a cikin rayuwar duniya
lumshe ido kawai yayi yanajin wani Abu nabin
jikin shi yana ratsawa.
bugun kofar da ake ne ya dawo dasu cikin
duniyar tunanin da suke dukkan su .
Damuwata
By
Ayshart farouq
59
Bugun kofar da ake ne yadawo dasu daga tunanin da suke dukan su,
Da sauri na kalle farouk wanda shima ni yake kallo,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na fada a cikin raina,
Iskoni dakin bashine tashin hankalina ba rufe kofar da akayi ne yafi dagamin hankali tabbas ko waye yaxo yaganni ynda na shiga shock dole yayi zargin wani Abu shin miye ma dalilin rufe kofar?
Bankai ga qare tunani ba naji hajiyo muryar hajiya na fadin,
" shin ko wanka kake ne?
Meye ma abun rufe kofa kana cikin gida.?"
Saboda tsabgegen tsoro har bansan lokacin da wani dan guntun fitsari ya fito
min ba ,
"Na shiga uku farouq ya zanyi"
Na fada Ina duban shi,
Dan murmushi yayi tare da nunamin drower alamar in boye a ciki,
Da gudu natashi nashige cikin drowar har Ina buge kaina da kofa.
Shi kuwa farouk tashi yayi yaje ya bude kofar tare da cewa,
" yi hakuri mom Ina toilet ne,
" dama nayi tunanin haka"
ta fada tana kunno kanta a cikin dakin
Bai hanata ba shima ya koma ya zauna yan facing dinta,
Ganin yanda ta shigo ya tabbatar mishi da akwai magana a tattare da ita.
Wani kallo tayi Mai cikin tuhuma,
" me yasa kayi locking din kofar dakin ka alhali kana ciki,?
Cikin fargaba ya dubeta
" which kind of questions is dis mom?
Hararar shi Tayi sannan taci gaba da cewa,
" dakata farouq hala kana tunanin duk abunda kake ciki ban sani ba ne? Ko a tunanin ka zaka iya yimin wayo ne?
Toh Bari kaji duk wani Abu da kake boyewa ina sane dashi don kajiya,
Nida nake cikin drower sai hada gumi nake hanjin cikina tuni suka koka,
"Shi kenan ni muhibbat karyata ta qare"
Na fada cikin raina,
Shi kanshi farouq din ba qaramar firgita yayiba da jin kalaman mahaifiyar tashi,
Dakewa kawai yayi yasamu ya hada waddan kalmomi,
"Kamar ya mom?
Ya fada yana shafe xufar da yake karyomishi,
" ai yanxun haka xakace bakasan abunda nake nufi ba toh Bari kaji wallahi kayi kadan ka jamin abun kunya dama abunda fadeela ta gayamin gaskiya ne rufe kofarka kakeyi kace kada ta dameka ai ynx sai kafito kacemin ita kake rufewa kofa tunda bakasan halacci ba,
Toh wlh aure kaida fadeela ba fashi kaman anyi shi ne angama,"
Wani malalacin murmushi farouq yayi gami da sauke wata irin ajiyar zuciya ganin abunda take magana daban da wanda yake tunani,
",haba mom taya Zan rufe kofa saboda fadeela KO ba komai ai kanwata ce,
How can i do dis to her,plz mom ki daina daukan maganar yarinyar qarya tamata yawa wlh,
Kofata fa idan akaja ko ba ayi locking ba sai Tayi locking da kanta"
" toh nidai nagaya maka ka maida hankali Ku fuskanci juna
60
Kana ganin ga dan uwankanan ya saki jiki da kanwar ka sun fahimce juna
Yanxun ma nasan don yayi tafiya ne da ba don hk ba da yanxu yana gidan nan"
"Ayi hakuri mom nima xan gyara insha allahu"
Maganar ma yinta dai ne yayi don ya matsu ta kammala maganar ta fita,
Duk hankalin shi na Chan gun muhibbat
" wai me kake tunani ne?
Ta tambaya tana kallon shi,
"Ba komai mom am just exhausted,"
I need to rest kinsan ban Dade da dawowa ba,"
"Toh koma dai miye xuwa anjima ka kirata kuyi magana hankalinta ya kwanta itama,
" insha allahu mom Zamuyi magana kar kidamu,
" yauwa ko kaifah haka nake so naji,
Jiya muka qare magana da dadyn ku Za'a sanya ranar auren Ku da hajiya safiya ta dawo egypt,"
"Allah yadawo DA ita lafiya"
Ya fada cikin kotsawa,
" Kai ni motsi nakeji a Chan ta fada tare da mikewa tsaye tana nuna gurin da "muhibbat take labe,
Shima farouq mikewa yayi yana cewa ba komai may be labule na da fanka ke hurawa"
Ni kuwa fitsarin da nake rikewa ban San lokacin da yafito ba saboda bala'i,
Duk ilahirin jikina rawa yake nakasa ko kwakkwaran nunmfashi don kar taji,
kallon farouq kawai tayi tare da tabe baki tanaci gaba da jaddada mishi maganar fadeela,
Shi dai sai eh yake cewa,
Har kofar waje yakaita sannan yadawo yana ajiyar zuciya,
Inajin lokacin da farouq yazo ya bude min yana cewa fito muhibbat ta fita
Ai Ina fitowa ban ko kalle shi ba nayi hanyar waje da gudu
Inaji yana kwalan Kira amma Ina bazan iya tsayawa ba,
Allah ya taimake ni koda na sauka banci karo da kowa ba har na Kai dakina na zube kan katifa Ina maidani numfashi.
Ayshart farouq
©ayshart one©
No comments:
Post a Comment