AM] Ayshart one: Yazeed ko
Yaseer
Nah
Ayshart Farouq
Nagarta Writes Association
©NWA©
.
25
Guri ta samu ta zauna tare da cewa, " Abba Ina
wuni, gani ance kana nemana"
" lafiya kalau Afnan" ya karba yana kallon ta cikin
fari'a da kulawa irin ta da da mahaifi,
Ci gaba yayi da magana yana kallon Ibrahim da
Sagir, "dama ba komai yasanya nataraku anan na
ga face Ku zamo shaida a gare ni akan Afnan a
matsayinku na yayunta"
Gaban Afnan yayi matukar faduwa toh me
Abbanta ke nufi ne? Tsura mishi ido tayi cikin
tsanani tashin hankali don jin me zai fada,
Wannan Karon baki daya annaurin fuskar shi ya
chanja lokacin da yake magana, "Alhamdulillahi
nasan nabaku tarbiya gwargwadon ikona
musamman ma ke Afnan, saboda babu wani Dare
da zan runtsa face nayi tunani matsayin hakkin ki
da yarataya a kaina, wani lokaci banma sanin
lokacin da hawaye suke zubo min idan na tuna
cewa ke diya mace ce tarbiyantar dake yanada
matukar wahala saboda idan kika lalace toh duka
al'umma sun lalace haka kuma idan kika gyarau
duka al'umma sun gyaru, hakika ban fahimce
abunda nake miki na shiga hakkin ki ba sai jiya
da mahaifiyar ki take Kara tuna min, ban kara
gane maganar ta tayi tasiri a kaina ba saida naji
kina waya jiya misalin karfe biyu na dare"
Wannan karon Afnan fashewa tayi da kuka tana
kallon mahaifinta, cikin ranta kuwa sai cewa ta
keyi, " nashiga uku ni Afnan yanxu duk Abba yaji
maganar da muke jiya,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta fadab tuna firar
da sukayi jiya duka akan aure ne tana bawa
Yazeed hakuri akan cewa suma iyayen su biyayya
suyi abunda suke so ita kanta tana bukatar
auren,.....
Katse Mata tunani yayi da cewa,
"hakika sai jiya na tabbatar da cewa aure shine
mutuncin duk wata diya macce da take rayuwa a
doron kasar nan, tabbas Afnan na tauye miki inci,
na shiga rayuwarki da yawa na hanaki walwala
da sukuni akan kawai ingina rayuwarki don
zamowa Mai dogaro da Kai Ashe ban sani ba
kara ruguza miki rayuwa nayi, ta hanyar tsananin
da nake miki gashi kin koyi yin karya karatun ma
da nakeso kiyi shi kanshi yanzun bayi kikeyi ba
soyaya kikiye right ?" Yafada yana kallonta,
Girgiza mishi Kai tashigayi "a'a Abba Dan Allah
kayi hakuri kamini rai wlh Allah bazan karaba
Abba wayar tawama ka karbe duk wani Abu
dazakayi min kamin amma Dan Allah abbana
kada kayi fushi dani, ka hukunta ni ta ko wace
hanya amma Abba kada ka hukuntani ta hanyar
yin fushi Dani" kuka ta fashe dashi Mai tsanani,
Mikewa mahaifin nata yayi tare da komawa kusa
da ita yajawota jikin shi,
" yi shiru Afnan bakimin laifin Komai ba facema
birgeni da kikayi da kika nuna biyayya ma
iyayenki yafi komai muhimmanci a gurin ki dukda
cewa wani guri ki kaucewa iyayen naki amma duk
da haka ni nafi kowa laifi akan abunda kika
aikata na saving number namiji da sunan mace,"
Juyawa yayi tare da kallon momy da dasu
Ibrahim " Ku zama shaidata ni Usman nabaiwa
Afnan damar
ta gayawa wanda takeso ya turomin magabatan
shi"
Wata irin dagowa tayi tana kallon mahaifinta,
Duk da cewa maganar tamata dadi amma ita
harga Allah ba haka taso ba,
Gyada mata Kai yayi am serious Afnan kice mishi
ya turo min magabatan shi, Ina so infita hakkin
ki ne, inaso inaga magabatan shi shi zai sanya in
yadda da gaske yakeyi koda kuwa ba da wuri
za'ayi auren ba idan da wuri za'ayi ma walillahil
hamdu a shirye muke",
Kunya ta Kama Afnan "a'a Abba ni nafasa
karatuna zanyi"
" kaji ja'irar yarinya karatun ma da kika jama
baya taya zakiyi karatu ai idan muka barki zamu
tabka babban kuskure a rayuwar mu gashi tun
yanzu anfara haka ina gaba" inji momy
Abba yace, " a'a zainab ko gaba bama ganin
komai da yardar Allah,
Afnan ai aure baya hana boko hakama boko baya
hana aure kaman yanda mahaifiyar ki ta
gayamin,
Idan har minjin ki ya baki damar kici gaba da
karatu walillahil hamdu idan ma hanaki ci gaba
yayi duk daya ne Allah dai yamana jagora a
rayjwarmu kawai,"
Dukan su suka karba da "Amin"
26
Afnan kam har kaguwa tayi Abba ya sallameta
taje ta fadawa Yazid dinta wannan good news
din,
Kaman Abba yashiga ranta " toh uwata aje a
gayawa surikin nawa Ko"
Kunya ta kamata "uhm ni fah Abba na fasa"
Ibrahim dake zaune ya galla Mata harara " ai
haka zakice ki rika mawa momy karya kina satar
hanya kuna haduwa"
" ya subhanallah wai me suke nufi ne? Ba dai duk
abunda take suna hankalce da ita ba?"
Kukan shagwaba tasanya " Abba ka ganshi ko?"
" kyaleshi uwata shima na bashi nan da sati biyu
yafadi yarinyar da yake so aje amishi magana"
" zaro idanuwa yayi yana sosa keya, "uuhm dama
wlh Abba Ina so muyi magana da Kai kan wata
yarinya amma ban San ta inda Zan Fara ba,"
Dariya akayi duka momy tace, " yanzu ai
kanwarku ta buda muku ta inda zaku Fara don ko
sagir nasan can akayi"
Sagir yace, " tab momy rufa min asiri ni ai har
yanzu yaro ne ga dai su big bros nan masu
shema'u da Hafsa"
Harara Ibrahim ya watsa mishi " Ina wasa da kai
ne?"
Dady yayi murmushi yace, " kasameni anjima
muyi maganar" ya fada tare da mikewa,
Momy ma mikewa tayi tabi bayan shi,
Afnan dai kasa mikewa tayi don gudun tsokanar
Sagir don tasan tana mikewa zai hauta da
tsokna,
Ibrahim ya harareta "toh ai sai ki tshi ko kinxo
kin muna zaune kina kinibibi"
Zunburo baki tayi tare da mikewa dama abunda
take so kenan,
Dariya suka hauta da ita don tune sun ganota,
bata kulasu ba ta wuce abunta tana murna,
Tana shiga daki kan gado ta fada tare da kiran
Yazid,
Bugu daya ya dauka tamkar dama jiraye yake da
ita,
" albishirinka habibina" yanda tayi maganar saida
ya lumshe ido saboda dadin muryarta,
" goro" yafada a kasalance, " amma Allah yasa
bani ke akayi"
Dariya tayi,
" Kai wani lokaci haka kake tamkar aljani,"
Mikewa yayi daga kwancen da yake don jin me
zata fada,
" Ina jin ki plz na kagara inji"
Dariya tayi tare da kwashe duk yanda sukayi da
abbanta ta gaya mishi,
Yanda yaji maganar yana tunanin a duniya ba
Wanda yakaishi jin dadi " Afnan da gaske kikeyi
kuwa ko tsokana na kikeyi" ya fada cikin tsantsar
farin ciki,
" Allah da gaske nakeyi Yazid Abba yace ka turo
magabatan ka"
"Alhamdulillahi Afnan nayi farin cikin jin wannan
maganar taki sosai insha allahu nan da 1 wk
zasuzo amma kafin hakanan yau zanzo zance
gidanku nasan dai ba matsala ko?" Ya fada
tamkar yayi tsale yaganshi gurinta,
" Zan sanarda Abba duk yanda yace sai in sanar
dakai duk da bana tunanin zai hana,"
" toh ba damuwa sai naji ki".
Haka dai sukata waya suna jin su tamkar sunfi
kowa farin ciki a fadin duniyar nan,
Bama kaman Yazid da yake ganin yakusa cimma
burin shi kan Afnan don yana ganin wannan
hanyar ce kadai zaibi don ganin yasamu abunda
yake so a gurinta.
Dan Allah masu karatun wanna novel kuyi hakuri
da yanda kuka samu typing din nasan dole a
samu kura kurai da yawa a ciki kasancewar
wayata tanada matsala don mota ta takata
wannan ma da kyar nayi shi saboda sizing din da
wayar keyi.
Nagode
©Ayshart one©
[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko
Yaseer
Nah
Ayshart Farouq
Nagarta Writers Association
©NAW©
27
Haka Afnan taje ta sanar da mahaifinta yanda
sukayi da Yazid din,
Yaji dadi sosai har yabashi damar yazo amma
yau ka dai don shi baya son yawan firan nan ba
tare da anyi tsayayar magana ba,
Haka taje ta sanar da Yazid, yayi murna sosai da
jin maganar ta ai kuwa 8:00 ya isa gidan su.
Lokacin Afnan taci kwalliya tamkar wadda zataje
gasar kyau, falon baki ta kaishi yayin da ta hada
mishi kayan motsa baki iri iri,
Lokacin da ta shigo falon suma ne kawai baiyi ba
gurin kallonta, don baki daya ta tafi da tunanin
shi da hankalin shi har baima San lokacin da
mike yaje gabanta ba.
Ganin haka ne yasanya tayi tsaye cak tana kallon
shi don ganin abunda yake shirin aikatawa,
Ai kuwa kafin kace mi tuni ya rungumota yana
shin shinar kamshinta duk ilahirin jikinshi rawa
yake idanuwan shi sunyi jajur tamkar
mayunwacin maye,
Cikin tsananin tashin hanakali ta tureshi daga
jikinta,
Cikin tsawa take magana, " meye haka ne Yazid?
Me yasa kai sam baka tsoron aikata abunda Allah
yayi hani dashi? nifa ba matarka ba ce meyasa
kake son tabamin jiki?,"
Dafe kanshi yayi da hannayen shi duka biyu, " oh
my God! Me nake shirin yi ne?, Afnan am totally
out of my control wlh jina nake yau tamkar
ankawo min ke a matsayin matata plz Dan Allah
kiyi hakuri wlh shaidan ne ya rudeni plz Afnan,"
Yanda yayi maganar tamkar yayi kuka,
Abunka da so nan take tausayin shi ya kamata,
Hararan shi tayi, " toh naji amma kaji kasake min
irin haka Dan Allah"
" insha allahu bazan sake ba" ya fada yana sosa
keya, " but plz kimin alfarma in rika hannunki in
kaiki ki zauna" ya fada cikin sigar zolaye harda
kanne ido,
Dariya tayi tare da wucewa "idan zaka zo ka
zauna ka zo idan bazaka zo ba ga hanya nan
Allah raka taki gona,"
Shima cikin dariyar yazo ya zauna kusa da ita
yana kallon ta "wai kin ganki? Allah tamkar
amarya"
" uhhm! Allah ko?"
Gyada Mata Kai yayi "sosai kuwa my Afnan"
Agogon hannunta ta duba "kaga fah lokaci na
wucewa gashi bakama ci komai ba" ta fada tare
da Fara zuba mishi abincin,
Haka yaci abincin dukda bayaji yunwa, yasan
idan yace bazaici ba rigima kawai zasuyi,
Fira suka shigayi sosai tamkar ranar suk Saba
haduwa,
Bashi yabar gidan ba sai kusan 10:30 shima ba
don yaso ba sai dai don ba yanda zaiyi ne.
Yau sati biyu da faruwar haka amma ba Yazid ba
samatar sa, hankalin Afnan yayi matukar tashi
gashi ko ta Kira wayar shi bata zuwa,
Kwance take kan gado idanuwanta na kallon
sama hawayene keta sintiri a fuskarta, tunani da
yawa a zuciyarta " toh me yasame Yazid ne?, ko
kuwa dama bayada ra'ayin aurena ne?, Kai
wannan bazaima yuyuba Yazid yana sona nasan
bazaimin haka ba"
Wata zuciya tace, " kika sani ko matsala ya samu
daga iyayen shi ne" wata zuciyar kuwa cewa tayi,
kila kuwa wani Abu ya sameshi Kai kilama
mutuwa yayyi baki sani ba.
Ai kuwa tamkar wani ne ya gayamata, ta shiga
rera kuka tamkar ranta zai fita,
Wayarta ce tayi ringing da sauri ta mika hannu ta
dauko tana addu'ar Allah yasa Yazid dinta ne,
Sai dai kash! Ba Yazid idanuwanta suka gani ba
sunana mahaifinta ta gani, ai kuwa lokaci daya
hankalinta ya sake matukar tashi don tasan
wannan kiran bama na lafiya ne ba,
Cikin muryarta da ta dusashe ta dauki wayar,
Sallama kawai mahaifin Nata ya karba tare da
cewa, " uwata kizo Ina neman ki yanzunnan" bai
tsaya yaji Mai zatace ba kawai ya kashe wayar,
28
Wayar Afnan ta tsurawa ido " toh me ke shirin
faruwa ne? Dole ne ma nasan maganar Yazid
abba zaimin toh me zance masa?"
Ganin batada mahita ne yasanya ta mike taje ta
wanke fuskarta sannan ta nufe gurin kiran da
Abban nata ke Mata.
Da sallama ta shiga dakin mahaifin nata, bayan
ta gaidashi ya karba cikin fari'ar shi, yamata izini
da ta zauna, bayan ta zauna ya dubeta " me yake
damun ki ne naga idanuwanki sunyi ja,"
Murmushi ta kakalo "ba komai Abba daga bacci
na tashi,"
" eyya ai kuwa da nasan bacci kike da ban takura
miki ba"
" a'a wlh Abba ai ba komai dama lokacin tashina
yayi ai"
Yace, " OK dama na kiraki ne kan maganar yaron
da kika ce kina so,"
Ras! Gabanta ya fadi
Yaci gaba da magana, " naji dadi sosai kan
abunda yaron yayi don haka da yayi shi zai nuna
yaron kirki ne kuma da gaske yakeyi don kusan
kwana biyu kullun sai ya kirani ya gaidani, yanzu
haka ma bamu dade da kare waya dashi ba shida
mahaifin shi,
Ya bani hakuri kan cewa basu samun zuwa
wannan satin sai bayan sati biyu saboda
ankwantar da Yazid din bashida lafiya kuma wai
zaiyi tafiya a wannan satin sai dai yadawo,"
Gaban Afnan ya fadi hankalinta yayi matukar
tashi, duk da kwarai taji dadin maganar da
mahaifin nata yayi amma jin rashin lafiyar Yazid
sai taji duk ta kara rikicewa,
Abba yaci gaba da magana "yanzu dai nace masu
suyi hakuri nan da sati biyu masu zuwa sai ayi
maganar saboda nima tafiya zanyi a yau kuma
ina tunanin zanyi sati biyu ban dawo ba shi yasa
na kiraki ingaya maki don infitar miki da hakkinki
dukda nasan wannan maganar ba dole ne sai
kinjita ba amma abun ne yayi matukar birgeni na
ganin mutanen sun San hakkin Dan Adam sosai.
Afnan tayi murmushin jin dadi, " adawo lafiya
Abba Allah ya tsare yakai lafiya"
"Ameen" ya fada tare da cewa, "amma fah uwata
baki kyauta ba da baki gayamin surukin nawa ba
lafiya ba"
Rufe idanuwanta tayi "ai Abba yaji sauki"
" toh Allah bida lafiya" yafada tare da mikewa,
" ki kiramin momyn ki lokacin tafiyata na
matsowa,
"Toh abba" ta fada tare da mikewa.
KaromKaroma taci da momyn zata shiga falon
shi yasa bata gaya Mata ba ta wuce kawai
dakinta ta fada kan gado tana hamdala.
Number Yazid ta sake dialing amma still number
bata zuwa, tsaki tayi tare da wulgar da wayar,
Hakika tasan tana muradin jin muryar shi tare da
marmarin ganin kyakkyawar fuskar shi.
Safiyar yau ma haka ta tashi da mafalkan Yazid
iri iri, ji take yau bata iya rayuwa idan bata ganshi
ba ko taji muryar shi ba, haka ta shirya taje
makaranta jikinta duk ba dadi
Bayan sun kare lectures ne sun fito tana zaune
kan wata kujera tana Danna wayarta taji anmata
sallama,
Amsawa tayi ba tare da ta dago fufuskarta ba jin
ya Kira sunana ta da Afnan ne yasanya tayi
saurin dago fuskarta,
29
Karaf suka hada ido da Yusuf abokin Yazid,
Murmushi tayi tere da cewa,
" a'ah manya gari kwana biyu ka buya kaida
abokin ka ya jikinshi?"
Murmushi yayi shima, " Alhamdulillahi he's
getting better amma fah fushi ya keyi da ke,"
Zaro idanuwa tayi "fushi fah kace?, "
" eh mana, ace yanzu duk rashin lafiyar da Yazid
yayi kikasa zuwa dubasa gashi kullu cikin kiran
sunan ki yake duka gidansu ba Wanda bai sanki
ba har su Kansu sunyi mamakin rashin zuwanki
asibiti duba shi,"
Jin an ambace asibiti yasanya tayi saurin dagowa
ta dube Amnu, asibiti fah kace? shi Yazid din ne
ya kwanta asibiti?
" uhum sosai kuwa yanzu haka ma yana can"
Idanuwanta cike da kwalla, "Allah ni ban san ma
bashida lafiya ba sai jiya don kona Kira wayar shi
bata zuwa"
Aminu ya dubeta cikin tausayawa " gaskiya Yazid
bai kyauta ba amma yanzu ya kamata kije ki
dubasa tunda kinji "
" wane asibiti aka kwantar dashi?"
Ya gayamata sunan asibitin yayi,
Duban shi tayi cikin damuwa " kash gashi
nasarawa hospital ba a shiga yanzu sai 4"
" gskiya kam ba a shiga amma idan yanzu zakije
muje in ajiyeki don Ina cikin masu jinyar shi za'a
barni nashiga dake"
Ganin wannan ce kadai damar da zata iya zuwa
dubashi ya sanya ta amince,
Cikin farin ciki aminu ya dauketa a motar shi
suka nuface asibiti,
Suna isa likaita ya tabbatar musu da an
sallameshi yanzunnan,
Haka suka fito jikin Afnan duk yayi sanyi gskiya
tana son ganin Yazid,
Ameenu ya dubeta " yakamata gsky kije gidansu
ki dubashi"
"A'a gaskiya bazan je gidansu bah idan naje mi
zance?"
Murmushi yayi " ai ba kya isko mum dinshi sai
daiko kannen sa"
Afnan bata so zuwaba amma aminu yata yimata
dadin baki har ta amince da maganar shi ta bishi
gidansu Yazid,
Kallo daya zaka Mata ka gane cewa bata cikin
nutsuwarta, har suka isa gidan ita dai bite kawai
take da shi gidan
Gidan ba Kara min kyau yayi Mata ba, cikin ranta
tace, " gske dai Yazid yake Dan gata"
Batare da fata lokaci ba aminu ya kaita dakin
Yazid din, nuni yamata da ta zauna, zama kawai
tayi amma duk ilahirin jikinta rawa yake,
Yazid ne yafito daga wata kofa tamkar wand bai
taba ciyoba don har kiba yadan Kara,
Wanni kallo sukayiwa junan su shida Aminu, take
aminu yabi ta kofar da yazid din yafito yafita
yana Dan murmhshi,
Ganin haka ne yasanya hankalin Afnan yakara
tashi,
Cikin fari'a Yazid ya karaso yana cewa,
" wow Ashe dai kinyi missing Dina da yawa my
princess"
Wani kallo tayi mishi cikin tuhuma, " me kake nufi
Yazid ba dai lafiyarka kalau ba"
Murmushi yayi tare da zama kusa da ita tamkar
ya shiga jikinta,
",dama gwadaki kawai nayi don Inga irin son da
kikemin"
Mikewa tayi, " miye haka Yazid? Kada kasake min
irin wannan wasar bana so?"
" oh common baby" ya fada tare da fizgota ta
fado jikin shi "am sorry plz baby na wlh nayi
missing dinki,
Yanda yake maganar yayi matukar bata tsoro don
haka ta ganshi tamkar ba Yazid dinta ba
idanuwan shi sunyi jajur,
" don girman Allah ka sakeni in wuce gida jirana
akeyi"
"Nasani mana amma ai bazakije haka ba bakisha
ko ruwa ba"
" uuhm a'a ni nagode"
" murmushi yayi tare da sakinta ya mike yayi
gurin fridge, tana ganin hakanan tayi wuf zata
fita sai dai kash an rufe kofar ta baya,
Tana ganin haka ta fashe da kuka,
" na shiga uku ni Afnan don girman Allah Yazid ka
budemin kofarnan infita,
Bai kulata ba sai murmushin ketar da yakeyi, molt
ta dauko ya nufota,
"Sai kinsha ruwa zan bude miki kifita " ya fada
yana mika Mata molt din,
Da sauri ta amsa ta Dan kurba,
" toh gashi nasha muje"
" naki wayon" ya fada tare da amsar molt din ya
shiga dura Mata ita saida yga ta shanye kaf
sannan yajata da karfi suka fada kan kujera,
Kallo daya zaka mishi ka gane baya cikin
hayyacin shi,
" plz Afnan dan Allah ki taimaka min wlh ina cikin
tsananin bukatar ki"
Kuka tashigayi na tashin hankali tana rokon Yazid
da yayi hakuri kada ya keta Mata mutuncin ta
amma Ina baxai iya ba shedan yariga yayi mishi
huduba.
Tun tanada karfi tana kokowa dashi tana tureshi
har ta galabaita kasancewar karfi ba guda ba.
Tanaji tana gani Yazid ya rabata da mutuncin ta
Wanda koni kaina marubuciyar saida nayi kuka
ganin halin da Afnan take ciki.
No comments:
Post a Comment