Sunday, 19 March 2017

Yazeed ko yaseer

           Yazeed ko yaseer
                  Nah
        Ayshart Farouq
                 
                 NWA
   

              5_10

Dariya Yazeed din yayi tare da lakuce Mata hanci " sarkin tsoro to wasa nakeyi",

Afnan tayi ajiyar zuciya tare da cewa "toh bana son irin wannan wasar ka daina plz"

" Allah ya huce ran gimbiya  nadaina"

Yanda yayi maganar saida yabata dariya kasancewar shi mutum ne Mai barkwanci,

Shima dariyar yayi tare da cewa,
" wallahi Afnan Ina son aure "

Gaskiya ya bata tausayi yanda yayi maganar sai dai tafishi zama abun tausayi kasancewar cewa ita mace ce tanada rauni sosai hardai wannan zamani da muke ciki a yanzu,

Muryarshi ce ta katse Mata tunanin ta,  "  Afnan nasan bakya jin yanda nakji ko?" Ya fada tare da zuba Mata idanuwa,

Cikin muryar tausayi tace, " ko inaji ya muka iya?  dole mu hakura da abunda iyayen mu suke so shekara biyu ai kaman gobe ne,"

" ai bama tani ba ni, ke nake dubi tunda kema ra'ayin mahaifin ki kenan kiyi karatu Mai zurfi kinga kuwa ba shekara biyu ba akwai sauran lokaci da yawa tunda na tabbatar da cewa ko mahaifin ki zai miki aure sai kin Kai UG 4 ko five  gashi yanxun kike UG 1"

Gabanta ne ya Fadi tuna maganar mahaifinta, lokaci daya damuwarta ta karu harma da guntuwar kwallarta
Cikin sanyin jiki ta dubeshi,
" toh ya kenan? Nasan bazaka iya jirana ba ko?"

Murmushi ya kakalo " haba ya zakice haka? Zan jiraki mana ko shekara goma ne kuwa na miki alkawari"

Wani sanyi taji a ranta tare da Kara jin sonshi yana shigarta ta KO ina,
Cikin ranta kuwa haushin akida takeji irin ta mahaifinta,

Hannunta ya Dan Kama tare da murza yatsunta, " me kike tunani ne?"
 
Da sauri ta kwace hannunta tare da hararan shi, " miye haka? bana son irin haka fah"

Kunnuwan shi ya Kama tare da marairaice fuska " am sorry plz"

Wayarta ce tayi ringing da sauri ta duba ganin mahaifiyarta ne yasanya taji  gabanta ya fadi,
Cikin  tsoro ta dube Yazeed dake kallonta,
Tace, " nashiga uku momy ce"

" dauka kice Mata kina hanya" ya fada cikin  rada,

Cikin ladabi ta dauki wayar,   "momy Ina hanyar dawowa," tafada tere da katse wayar ,

A gurguje sukayi sallama da Yazeed  duk da cewa ba haka yaso ba ita kanta ma ba haka taso ba sai dai don ba yanda suka iya ne, haka suka rabu cikin kaunar junan su tare da kewa Mai tsanani,
Kasancewar satinsu uku basu hadu ba ta dalilin Hutun da Afnan din keyi na makaranta.

Ayshart one

No comments:

Post a Comment