Sunday, 19 March 2017

Yazeed ko yaseer

              Yazeed ko Yaseer
                         
                         Nah
       
                 Ayshart Farouq

                           NWA

                       1_5

         Zaune take kan sallayarta ta idar da sallar la'asar tana istigfari, mace ce 'yar kimanin shekara  arba'in da biyu zuwa da uku, amma Sam batayi Kama da shekarunta ba saboda irin kyaun jikin da Allah ya Mata da kuma kasancewar ta 'yar Hutu, idan ance ka fadi shekarunta zaka iya  rantsewa 'yar talatin ce,
Kyakkyawa ce mai cikar mutunci da kamala,

     Wata kyakkyawar yarinya naga tafito cikin shirinta da alama fita zatayi don sanye take da hijab Mai hannu iya  gwiwa, hannuwanta riqe da yar post dinta kalar takalminta ko ba'a fada ba kasan cewa diyar hajiya zainab ce saboda tsantsar kamar da sukayi duk da cewa yarinyar bazata wuce shekara  goma shatakwas ba.

   Gurfanawa tayi gaban mahaifiyar tata tana murmushi tare da cewa,
" momy naga kina ta kallo na " ta fada cikin shagwaba,

" ba dole in kalleki ba naga kinci uban ado haka kuma kinsan yau ba islamiya"

b'ata fuska tayi , " haba momy nafa gaya miki ina so inje gurin kawata maryam in karbo wani littafi da nake so in koya gurin malaminmu"

Cikin fada fada momyn tata take magana,
" kin San dai mahaifinki baya son irin wannan yawon ko ? Ko so kike yadawo bai ganki ba  ya hauni da fada? Gskiya abunda kike mun Afnan Sam ba na son shi kin fi kowa sanin halin mahaifin ki amma ke Sam ba kya gudun abunda kanje ya dawo,"

Cikin ladabi da girmamawa Afnan take magana " Dan Allah momy kiyi hakuri insha allahu Abba bazai dawo yasame bana nan ba amma idan har bakya son fitar na hakura sai wani lokaci sai inje in karbo"
Ta karashe maganar tare da mikewa idanuwanta cike da kwalla ta juya zata koma,

Cikin sanyin ta ta kirata da " Afnan kije amma kada ki dade kinji autar momy plz kada kiyi kuka ki b'ata kwalliyar ki",

Cikin murna da jin dadi Afnan tayi godiya sannan ta juya ta fita tana murna.

     Ahankali ta ke tafiya saida tayi nisa da gida kadan sannan ta bude post dinta ta fidda wayarta kusan 12 miss call ta gani kasancewar wayar silent take,
Murmushi tayi lokaci daya ganin wani kiran ya shigo da number da akayi saving da maryam2,

Cikin muryarta Mai dadin sauraro  take karba wayar, " dan Allah kayi hakuri gani nan na kusa karasowa kasan fitar saida dubaru, OK toh sai na karaso ta fada tare da kashe wayar ,

Tafiyarta takeyi cike da nutsuwa har takai bakin wata mota kirar prado jib baka wulik sai sheki take,

Murmushi suka sakarwa junan su lokacin da idanuwan su suka sarke guru daya ,

    Ahankali ya bude motar ya fito wanda lokacin da naganshi saida nakusa fita hayyaci na saboda tsananin haduwar shi wadda duk yanda ka Kai gurin kushe mutum bazaka taba kushe shi ba  don bazaka taba iya cewa ga munin shi ba,

Cikin fari'ar shi yake cewa, " amma fah gskiya ya kamata ace nayi fishi da ke my princess sai dai kuma kash bazan iya ba,
        
Murmushi Afnan tayi irin Wanda ke karamata kyau da annuri ,

" ki daina min irin wannan murmushin yana kara zuzutar da ni, wani murmushin ta sakeyi Wanda yafi na farko kayatarwa,

" kaifah YAZID akwaika da abun dariya wlh" ta fada tana duban shi

" Allah ko princess?" Ya fada shima yana Mata wani irin shu'umammen kallo tare da cewa,
" kin San wani Abu?"
Tace ," sai ka fada"

Kanshi ya dan sosa " Allah KO wace irin shiga kikayi kyau kike yi"

Wannan Karon tuntsirewa Afnan  tayi da dariya " Allah yazeed ka cika abun dariya nufah duk daukana abun kwarai zaka fada"

Shima cikin dariya yace, " au wannan ba abun kwarai ne ba kena?"

Murmushi tayi tare da cewa,
" toh yanzu ya ake ciki ne? Kasan karya na zubawa mom  tace kada nadade banaso nabata Mata rai gobe ta hanani,

" haka ne kam" ya fada tare da sosa keya " gashi kuwa ma naso ki rakani wani guri"

Zaro idanuwa tayi tare da daure fuska "amma dai wasa kakeyi ko?"


 
Ayashart one

No comments:

Post a Comment