Saturday, 29 October 2016

Nayi nadama na ayshart farouq

[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
            By
Ayshart💞
           1-5
zaune take ita kadai acikin harabar gidan  zuciyar ta sai tunano mata irin kyakkyawar fuskar da Allah ya hadata da ita tun
bayan sati biyu da suka wuce,
Ita kanta tana mamakin ynda Allah ya jarabeta da son mutumin da batasan shi ba, bata san asalin shi ba.
tayi ajiyar zuciya alokacin dataji andafa kafadar ta
"Humaira wai tunanin me kike haka?"
Sai alokacin tagane mai magana khairiyat ce qawarta.
tayi murmushi sannan ta ce,
"khairat yaushe kikazo ne?"
mtsw taja tsaki
Ta ce,
"haba humaira tun yaushe nake mgana kina cen kina tunani, wai ma Dan Allah humee miyake damunki ne? Ina fa lura dake kwanan nan duk haka kike bakida sukuni koyaushe  cikin tunani kike please kigayamin abinda ke damunki mana"
"uhum"
tadan tabe baki bakomai khairat rayuwa ce kawai."
cikin bacin rai khairat tace
"toh shikenan tunda hakane Allah ya kyauta ni zan wuce",
humaira taja hannunta
" haba dear am sorry naga kin bata ranki  zauna zan gaya miki abinda ke damuna" Tamika mata dayan kujeran datake zaune akai,
sa'an nan ta soma bata labarin haduwarta da hadadden saurayi LAWAL.

House of novella📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: NAYI NADAMA 😭
          Nah
💞Ayshart💞
        10-15
Alh Usman Ahmad mahaifi ga fadimatul humaira su ukku ne ga mahaifinsu Alh Ahmad mai fata,
Abbakar shine nafari yanada mata daya hjy suwaiba wadda ake kira da umma diya biyar Ahmad Wanda yaci sunan kakanshi suna kiranshi da fahad sai habib, Umar, ummul kursum and Mimi wadda bata wuce 3 yrs ba, suna kiran Alh abbakar da
Abba,
shi kuma alh Usman yanada matar aure daya hjy salmatu wadda suke kira da momy tare da diya hudu mustapha, sabir zayyad and Fatima waddda taci sunan kakarta ana kiranta da humaira, director ne na s.s
gidan babban gidane Wanda yaci sunanshi part uku ne kowa da nashi har yakumbo wato kakarsu,
Alh Ahmad  ya dade da rasuwa tun suna kanana sai qanwarsu da take aure abuja amina,
Allah ya dauka ka su ga uwa uba hadin kai,
fahad da mustafha suna karatu England humaira and kursum ynx suke s s 2 Kansu hade yake tare suke zuwa school class dinsu daya basa kula kowa sai qawa daya dasuke da ita khairat itama Halinsu Yazo daya shiyasa ake ganin kaman sunada jin kai.

House of novella📚📚
O8100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Na
Ayshart💞
           5-10
Ranar frdy bayan muntashi school lkcn kin wuce ina jiran driver yazo.
nasamu wata inuwa nan kusa da school nazauna, nadade zaune harnafara tunanin ko achaba zan hau ne,
kuma wata zuciya tace dady fa idan ya ganki,
Ban smu mafita ba kawai sai ji nayi anamin sallama ina daga kaina zuciyata naji tana bugawa dalilin ganin wata kyakkyawar fuska  dauke da murmushi gani ni kuwa da son Abu mai kyau sai namutu gurin kallon shi
   ban ankaraba sai jin nayi ya sake cewa "Assalamu aliki" 
na amsa cikin sakin fuska nima ina dauke da murmushi,
yasake murmushi akaro nabiyu saida fararen hakoranshi suka bayyana
sa'an nan ya ce,
"tun dazu naganki nan gashi har naje  nadawo nasake tarar dake gashi  kuma lokacin  shiga masallaci nayi,
kina jirne axo daukan ki ne?"
Na daga kai alamar
"eh"
yaduba agogon hannun shi,
"idan baza ki damuba muje in sauke ki a inda zaki, wace unguwa kike?"
"Governor road amma kayi hakuri gskya babana zai min fada idan yaganni cikin motar wani"
nafada,dama kaina qasa yake lkcn da nake magana banji yace komai ba dagowar da xanyi sai kawai muka hada ido Ashe dama ni yake kallo
nima sai nasamu kaina da kura mashi idanuwa,
ahankali naji wani Abu yadake zuciyata, nasaukar da idanuwana kasa ina murmushi,
shima murmushin yake,
yayi mgn cikin kasala kamar Wanda kwai yafashewa cikin ciki
"ya sunan ki?"
na ce,
"Fatima amma humaira ake kirana"
" wow nice name"
yafada  yana kallo na San nan
ya ce,
"Ni sunana Lawal"
a lokacin ne naga motar gidan mu tana yowa wurina namiqe inacewa anzo daukata Lawal yakuran ido shikenan ba matsala yafada atakaice,
banyi mgana ba sbd wani abu da yadake zuciyata,
kawai dai nakama hanya na isa inda driver yayi parking nashiga batare da bata lokaci ba yaja muka wuce har lokacin Lawal nawurin sai kallona yake yana daga mun hannu.
Ta dubi khairat tayi ajiyar hrt
"toh kinji wlh tun ranar nakasa samun sukuni narasa walwala komai nayi shi nake gani abinci ma idan zanci idan natuna dashi kasa ci nake,
shiyasa nake xuwa nan ina Dan samun sukuni gashi kursum ba lafiya ballantana inji ko akwai mafita kekuma nasan halinki tsiya zakimin shiyasa nakasa gayamiki,
khairat tayi murmushi mai hade da tsaki "amma wlh ke banza ce humaira ina kinka taba ganin anyi haka baifa ce yana sonki ba"
humaira tayi murmushi
"bazaki gane ba khairat"
ta fada tana yatsine fuska,
khairat tace,
"shi kenan zamuyi magana gobe yanzu mom nacen tana jirana dama jikin kursum nazo dubawa naga tasamu sauqi,"
tafada tana mikewa,
itama humaira mikewa tayi suka fita tarakata.

House of Novella📚📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
     💞Ayshart💞
     
               20-25
Exchanging Nmbr sukayi  San nan yawuce.
A haka tasami su kursum ta gayamusu duk yanda sukayi, fatan alkhairi Suka yi mata,
sannan suka kama  mata tsiya kursum
ta ce,
"Watoh Allah ne ya nuna miki  abun ki  humaira  lokaci daya kin fara dandana azabar so ina gaya miki  wulaqanta samari ba kyau amma ke bakiji kina wani ce wa ba ayi saurayin da zaki so ba toh ynx ba ga shi ba?" 
Khairat
ta ce,
" ynx dai kema kin shiga don haka sai adaina yimana tsiya,"
suna haka akazo daukan su,
Da khairat suka wuce kasan cewar  bayan layinsu take.    
  kwance take rub da ciki tana jiran kiran abin kaunarta,
tana so ta kirashi tana gudun zubar da ajinta haka dai tayita saqe saqe har marece tayi babu kiran Lawal har tasa nmbr shi da niyar ta kira bata kai gayin dialing ba sai jin wayarta tayi tana ruri,  cikin zumudi ta dauka da
"Assalamu alaikum"
cen cikin sasssanyar muryar shi ya karba da
"Wslm"
Sa'an nan ya kara da
Ce wa,
" humaira kizo gani kofar gidan Ku" yakashe wayar,
cikin mamaki
ta ce,
"yaushe Lawal yasan gidanmu tunda banyi mishi kwatance ba?
Ko dai biyomu yayi ne?"

House of novella 📚📚
  08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
       💞Ayshart💞
              
                25-30
Cikin Palo ta tarda momyn ta
"Ke humaira ina zaki haka?,
Cikin inda2
Ta ce,
momy wannan Lawal din nan   ne  da nabaki lbr yana waje  yazo,
ta fada a dabirce,
sabir nagefe
Ya tabe baki
Ya ce,
"kema kin fara tara samarin ne?"
Ta turo baki
"toh miye ruwanka aciki nifah kaga bana son sa ido,
Momy kice yafita harakata"
tafada cikin shagwaba Momy ta ce,
"tafiyanki kyale shi kar ya bata miki kwalliya" ya ce,
" Momy wlh ke kinka qara shagwaba wan nan yarinyar"
"Eh din anyi idan fisari banza ne kaza tayi"
ta fada tana murguda baki
aiko yayo kanta zai kaimata naushi ta kwasa da gudu sai waje,
yadawo yana ta kwasar bala'i
Momy dai kallon su kawai take don idan da sabo ta saba.                        rakube ta same shi yajingina jikin  motar shi yadaura hannayen shi a kirjin shi,
"salamu alaikum" tafada cikin jin
kunya .
"wslm"
yafada yana
Dubanta,
tsawon mintuna uku babu Wanda yayi mgn " humaira "!
Yakirata tare da zuba mata ido,
"na'am"
Takarba batare da takalleshi ba
Yayi murmushi
Ya ce,
"Humaira ina so kibani Aron hnkln ki Dan Allah",
"  uhum ina jin ka" 
ya sake kiran sunan ta a karo na 2
"Humaira"
wannan karon bata amsa ba kallon shi kawai tayi,
yaci gaba da fadin
"Nagode kwarai da hadin kan da kika bani, nagade da kika karbe soyayya ta,
Humaira ina so inturo mgbt na kaman ynda kika buqata,
Naso ayi komai da komai kafin inyi tafiya amma hkn bazai yuyuba,
Sai lkcn ta dago ta kalle shi cikin mamaki
Ta ce,
" tafiya fah kace?"
Ya yi shuru nadan wani lkc, sannan ya ce
"Eh wani cos aka turani na tsawon  wata shidda, 
kuma tafiyar ce tazo cikin gaggawa,
Hmaira ki sani cewa ina sonki son da zan iya rasa rayuwata idan har  narasa ki",
ta sake  dauban shi cikin tashin hnkl,
ya ce,
" humaira kiyimin alkawarin xaki kulamin da soyyaya ta har inje indawo",
"xan kulama da kaina insha allahu "
Ta fada tana share kwalla,
"Nagode sosai"
Yafada yana bude mota
kayane yafito dasu masu yawa,
humaira kallon shi kawai take
" ga wan nan ba yawa Dan Allah kada kice bazaki karba ba "
Ta bata rai
Ta CE,
" gaskiya baxan karba ba Lawal gida fada xa ayimin ,
gsky kayi hakuri bazan karba ba,
haka dai yayita lallashinta dakyar ta karba tayi godiya tawuce tana kwalla sbd xatayi missing din abin kaunarta tsawon wata shidda gashi ko waya baxasuyi ba tunda yana cikin ruwa navy ne,

House of novella📚📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
          Na
💞Ayshart💞
       15-20
Yanayin yau ne na ranar mndy, suna zaune khairat keba kursum labarin saurayin humaira kursum sai dariya take tana cewa,
"lallai humaira ba marar hankali irinki yaushe daganin mutum zaki kamu da son shi Baki sanshi ba daga ganinshi sau daya, lallai kina tare da aiki,"
humaira tanajinsu bata ce komai ba  Dora  kanta tayi kan desk tanata tunanin abin kaunarta,
haka dai sukayi ta yi mata surutu har aka tashi school,
sunfito suna tsaye suna fira sai ganin mutum sukayi kaman daga sama fuskar nan dauke da murmushi yayimusu sallama
Asslm alaikum"
suka karba da
"wslm"
Daka kalle fuskar Humaira kasan tana dauke da farin ciki,
" malama humaira"
ya ambata yana kallonta,
Itama kallonshi take tana murmushi,
"Lawal yayi murmushi mai dunkule da abubuwa"
ya ce,
"wadan nan qawayen ki ne"
ta amsa
Da "eh"
" sannun Ku"
yafada yana dubansu
" sannu"
Suma suka fada lokaci daya
"Dan Allah idan baku damuba Ina son yin mgn da kawar Ku "
ba damuwa"
Inji khairat "
"nagode"
Yafada yana kalllon humaira ya ce,
"muje cen"
yayi nuni dawani wuri nesa kadan dasu khairat
Sukaje
"humaira manya" yafada cikin wata siririyar murya
"kinfa wahalar dani da yawa"
tadago ido tadan kallai cikin jin kunya
"kaman ya"
tafada tana sunkuyar da kai
yayi murmushi
"kinfi kowa sani,
wlh humaira bazan boye miki ba tun randa Allah ya hadani dake nakasa samun sukuni ynx haka kullun sai nazo nan ko xanganki amma sai yau har nayi niyar bada cigiyarki cikin skul dinku "  tadanyi murmushi saida siririyar wushiryarta ta bayyyana
"uhum ina jinka "
tafada atakai ce
" humaira ina so inje gidanku ko anmiki miji?,
Kina sona humaira?" Yajero mata tmby HK lkc daya ko inbaki lkc kiyi tunani tace eh yace OK xan xo anjima idan kinyi shawara
tace,
"Anjima fa kace "
" eh mana" yafada yana kallonta uhum toh muyi exc
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
       Nah
     💞 Ayshart💞
           35-40
kwance tashi su humaira sun kammala s s c e dinsu,Kumar  iyayen ta  sun San da mgnr Lawal,  
fahad da mustapha sun kammala karatun su  na likitan ci gida ya  kaceme sai murna ake gaba daya anhalarta sashen yakumbo anata fira xa aje tarbosu  a airport, murna kawai humaira keyi xataga yayanta da har ta manta kamannin sa sbd tunda sukaje basu dawo gida ba,
kursum cikin doki
Ta ce,
" humee wlh har namatsu banga Yaya musty ba dan gida na  kin tuna lkcn da muna yara ya musty yace nice kanwar shi yarika tare mun idan ya fahad zai dake ni,"
Humaira ta ce,
"nima hk wlh,
ina so inga Yaya fahada Dan gidana " haka dai sukaje sunata hira  a mota har airport,
basufi 20 minute ba jirginsu fahad ya sauka,
tsarki yatabbata ga Allah lkcn da fahad yasauko sanye yake da wasu fararen kaya idanuwan shi dauke da wani farin madubi duk Wanda yakale shi sai yaso yasake duban  shi,
Irin mazan nan ne da ake kira da  first class,
haka shima musty kallon su kawai ake yi, lokaci daya iyayen su suka rungume su suna murna,
haka ma su  humaira  rungume yayan ninsu sukayi cikin  murna da dokin juna,
Musty yadube fahad  ya ce,
" wai kaga yanda yaran nan suka girma"
Fahad yayi murmshi da yake shi bai cikan son  yin mgn ba, kallon da fahad keyi mata ne yasa taji duk ta takura ''Yaya wai kallon miye wannan''
tafada a kunyace, uhum!
yayi murmushi ,
"naga kin girma ne kaman ba wadda nake tarewa fada ba da dukan sabir"
ta turo Baki cikin shagwaba
ta ce,
"Toh ai ko kursum ma ta girma"
sai abin yabasu dariya,
Musty ya CE,
" wato dai  har ynx kurciyar nan tananan?"
haka dai suka yita hira har suka isa gida anata raha,
sashen yakumbo suka isa dukan su
fahad yarungume yakumbo yana
ce wa,
I misst   u Yar tsohuwa ta"
yakumbo
Ta CE,
" kai ni ban son shegantaka baturen England  nayi fishi  ka koma bana so,
Fahad yace,
"Haba tsohuwa kanki fah naje nayi karatu fannen idanuwa Dan inzo ingyara miki naki kidaina sa wannan madubin,
"Ashe kuwaza ayi  rigima a gidan nan don sai kin zabi Wanda kikafi so cikin mu"
inji musty duk aka san ya dariya gaba daya.

House of novella 📚📚📚
08100376392 for comment and correction
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
         Nah
💞Ayshart💞
        40-45
Bayan sun Dan samu sunci abinci sunyi wanka  sun huta fahad yanufe sashen yakumbo,
yazauna sunata fira yaushe rabo,
dayake jininsu ya hadu sosai duk cikin jikokinta ba Wanda take so kaman fahad azahiri sai dai ita kuma humaira basa shiri da yakumbo ko kadan.

      Humaira  na Palo tana kallon zee aflan wani film suke veer tana  son film din sosai saijin wani lallausan hannu tayi anrufe mata idanuwa ga kamshi duk ya game dakin
uhum!
" haba kursum miye haka?"
tafada duk da tanada tabbacin cewa  ba kursum din ba ce "   cikin wata murya mai daukan hankali
Ya ce,
"kinji ki toh ba ita ba ce"
ya sake ta tare da  zagayowa ta Gavan ta
"lah Ya fahad Kaine dama?"
"Eh nine,
jiya kina jina INA miki mgn kika kyale   ni ko?" Ta ce,
"Allah ya fahad banji ba"
Uhum,
"hk zaki ce ai
Kallo kawi ake yi?"
" eh"
tafada tana kallon t.v wayarta ce tayi kara sai dai number ce kawai ba suna
sai taqi dagawa,
"ba wayar kice ke ringing ba?"
" itace "
ta fada a takai ce
Ya ce,
"toh bazaki daga ba?"
        "Eh"
tafada tana qara maida hankalinta kan t.v
karo na biyu aka sake kira  tana
ringin

House of novella📚📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
          Nah
  💞Ayshart💞
         55-60
taraba shi ta wuce batare da tace mishi komai ba
"waye wancen?"
Yafada cikin tsawa
Ta ce,
Acikin raunanar murya "lawal ne, Abba yasan da mgnr shi
bata jira abinda zaice ba tawuce abinta.

Soyayya mai  karfi humaira kewa Lawal sai dai ita wani lokaci takan rasan ganewa gaskiyar Lawal saboda sau da yawa zaiyi magana watarana idan yazo sai taji ya chanja. abin yana daure mata kai sai dai kuma so hana ganin laifi yauma kwance take dakinta tanata tunani tunaninta Momy ce tazo kiranta
ta ce,
"humaira abbanki na Neman ki kisame shi a Palo"
ta ce,
" to Momy gani  nan zuwa"
ta tashi taje sai ta tarar dashi tare da dadyn su fahad
Bayan tagaidasu suka amsa ta nemi wuri ta zauna
Ta ce,
" Abba gani kana nemana"
ya ce,
       "Eh humaira" dadyn su fahad
Ya ce,
" dama kan maganar yaron dakikace kina so ne,
toh gsky munyi bincike akan yaron amma bamu gane asalin shi ba ga baki daya don  haka gskiya ki hakura dashi  don bazamu aurar dake ga wannan mutun ba,
ki bashi hkr kawai kije kikawa wani wnda kike so za Mu aura miki ko waye,"
kafin kace me humaira sai kuka tana
Ce wa,
" haba dady bafa nan garin yake ba Dan yola ne har cen kukaje kukayi bincike"
Abba ya katseta cikin tsawa kada ki raina mana hankali mana ya ana gayamiki mgn kina so kiyi mana musu,
ko so ki ke ki gaya mana ne bamusan abinda muke bane ko me  ye ,?"
dady
ya ce,
" kyaleta tashi kije xamu nemeki idan anyake shawara"
wani irin kuka take kaman ranta zai fita wato ana nufin za a rabata da Lawal dinta kenan wlh bazata yarda ba koma meye za ayi,
musty taci karo dashi "ke miye haka?
wayataba ki keke wan nan kukan haka?"
" dady ne "
ta fada cikin kuka,
yaja tsaki yawuce abinshi,
haka tashiga daki tayita rusar kuka ita kadai ba mai lallashinta don ga alama kowa yasan da maganar cikin gdn.

House of novella📚📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
💞Ayshart💞
         50-55
Ringing tadauka muryar dabazata taba mantawa da ita ba taji "hello my baby" humaira tayi murmushi ta rufe ido wani farin ciki ta rikaji,
Yace,
"kifito gani kofar gida" yakashe wayar.
Sai lkcn ta tuna fahad da  bata ganshi ba wata zuciya tace  yafita abun shi ,
oho dama Ai  bani nakawo shi ba taja tsaki wannan mutum yana so ya takura ma muta ne,
tafada cikin ranta,
tadauko mayafinta ta nata dokin ganin masoyinta,
fahad tagani nan zai shiga gida
ta ce ,
"Ya ashe ka fito?",
yadan bata fuska
     "Eh dama nashigo ne ingaida Momy sai kuma ban sameta nan Palo ba"
ta ce ,
"Eyya tana cikin daki bacci take yi?"
   "OK"
yafada a takyce ya shiga gida abinshi batare da yasake cewa komai ba ,
tabe Baki tayi tawuce Abun ta,
tsaye tasame shi kaman kullum
bayan sun gaisa ne yake
Cewa ,
"humairah nayi kewarki da yawa wata takwas fa marabina da ko inji muryar ki"
Tayi murmushi
Ta ce,
"ni wlh har katada min da hnkl ko yaushe wayarka switch up" uhum!
" humaira kenan,
kinsan irin yanayin aikin mu "
Ta ce ,
hakane kuma Ai ba laifi kayi ba kawai dai hnkl na bai kwanta ba  gudun kar wani Abu ya sameka"
ya ce ,
Allah sarki ba abunda yasameni baby sai dai kullum cikin kewarki nake"
Tayi
murmushin jin dadi "Allah ko "
takalleshi tana mai Neman qarin bayani
   "Eh mana"
Yafada shima
"dama ina so in tmby ka"
Ya ce,
yi tmbyr ki ina jin ki "dama dady ne yace sun yi bincike akan inda kake zama kuma su gane cewa ba uncle dinka ba ne,
Shine ya ce yana son cikakken address dinka na yola,"
Dam! Gaban shi yafadi yafara kame kame yane cewa, wannan ba uncle dina ba ne    abokin shi dai ne ba na gayamiki cewa ni Dan yola ba  ne iyayena duk sun rasu banida kowa sai dangin su  wannan uncle dina shi yariqe ni tun ina karami
shekarar Mu 2 da barin nan  Kaduna muka koma a gombe wannan da nace miki abokin uncle ne tare Suka tashi ina zuwa ne wurin shi idan nazo nan Kaduna aiki ko zumunci
idanuwan shi Suka cika da kwalla take tausanyi shi yakamata
ta ce,
Eyya Allah yajikan su "
Ya karba da
"Ameen,
Ynx hk ma
kanki nazo garin nan" uhum!
" Allah sarki toh nagode "
tafada tana sakar mishi murmushi,
Haka dai sukayi sallama cikin  so da kaunar juna,
yawuce tana daga mishi hannu, saida ta daina hange shi san nan ta juya,
juyawar dazatayi tashiga gida sai fahad tagani yana mata wani irin kallo mai dauki da harara fuskar shi daure ita kanta humaira sai da ta tsorata.

House of novella 📚📚08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
          Nah
💞 Ayshart💞
          60-65
Tun lkcn da akayi mgnar humaira ta daina walwala kwana biyu haka take batada wata walwala kursum ce ka dai ke  lallashinta tana Dan bata magana.
Kuma gashi wayar Lawal ko takira bata zuwa,
Shin ko su Abba sun koreshi ne?
Batada Wanda zai amsa mata tmbyr ta. Kiran da akayimata ne shi ya katse mata tunanin da take yi,
sabir taji yana
ce wa,
"kizo ana nemanki su dady suna part din yakumbo"'
faduwar gaba taji,
to lfy?
sbd ta tabbatar akwai muhimmiyar mgn tund aka ce aje part din yakumbo,
haka taje kamar wadda kwai yafashewa ciki
bata qara razana ba saida taga dakin cike da mutane
ita kadai ake jira.
Cen taje tazauna kusa da kulsum,
yakumbo tafara mgn kamar haka
''Dama mgnr da ta taramu nan ba wata mgn ba ce face mgn kan kulsum da mustapha"
Uhum!
Humaira tayi ajiyar zuciya,
sai dai kuma hankalin ta yatashi dataji  yakumbo
ta ce,
" da kuma fahad da humaira"
A tsorace humaira ta kalle  fahad sai dai kuma  taga shi ko a jikin shi,
a salima fuskar shi cike da annuri.
Yakumbo ta sake cewa,
"Dama dai abinda kowa yasani ne kursum da mustapha suna son junan su don haka Alhmdlh babu wata matsala nan bangaren,
sai dai bangaren humaira domin a gaskiya da dadewa fahad ya dade da gamin yana son humaira sai dai kuma yace
yaga kaman tana son wani  ne,
toh ynx tunda wanda take so angano ba mutumin kirki bane, shike nan sai ahada su tunda shi dama yana son ta,!"
Wata kara da  humaira tayi ita tajawo hankalin su akan ta
Kuka take mai tsanani tana kiran
"dama shi ne dalilin da yasa aka rabani da lawal domin  ahada ni da ya fahad  shi ne za ayiwa Lawal kazafi toh wlh bazan yarda........."!
wani mari tji yasauka kuncen ta
"ke kinada hankali yakumbo ta yi mgn kice ba hk ba abban ta
ne a harzuqe, 
kowa saida yayi mamaki abinda ba'a taba gani ba Abba ya dake humaira,
ita kuma yakumbo sai ce wa, take yi
"Ai wlh idan kina   kukan jini  sai kin aure fahad tunda yana son ki,
miqewa tayi cikin kuka tabar dakin,
shima fahad miqewa yayi  ya bita yana kiran ta
House of novella📚📚
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
         Nah
   💞 Ayshart💞
           65-70
Dakinta direct tawuce ta dora kai a gwuiwa tanata rusar kuka.
shi kan fahad tsaye yayi bakin dakinta yana kallonta,
a hankali yaje kusa da ita yaxauna yajawota jikinshi yana mgn cikin sanyin shi duk  tausayin ta ya kama shi
Ya ce,
"haba humaira miye abin kuka anan? 
don nace kawai ina son ki zai sanya ki bata tarbiyar ki,?
Humaira ykk so nayi da rayuwata ne?,
wlh humaira ina son
ki, "
ji tayi kamar anwatsa mata  ruwan zafi saboda haushi
bata san lkcn da ta janye jikin ta daga nashi ba tana
fadin,
" ynx kai bakajin kunyar ce wa kana so na,
ya fahad nadauke ka matsayin yayana uwa daya uba daya,
dan allah kafitar min daga daki tun kafin girmanka yaqara zubewa idona,
na tsane ka,
na tsane ka fahad, tafada da qarfi,
fahad yarasa abinda ke masa dadi yayi yayi ta fahimce shi amma abun yaci tura
haka yabar dakin ta jikin shi a sanyaye, yana fita taja kofa da qarfi ta rufe ta fada kan gado tana rusar kuka.               

lkcn hankalin fahad gaba daya baya jikin shi,
zuciyar shi duk ta jagule,
"anya zan samu soyayyar humaira?"
wata zuciya ta fada. ashe dama humaira batada saukin kai, 'innalillahi wa'inna ilaihir raji'un
yafada yana dafe kai kafadar shi yaji andafa, "haba fahad yazaka wahalar da kanka akan abinda kasan kanada tabbacin zaka samu plz bros dan allah kadaina kada kajama kanka wata matsala",
yadago idanuwan shi da Suka rine  kaman garwashi sbd tsananin jan da sukayi,
ya ce,
" musty kasan ina kaunar humaira tun ba yau ba,
musty humaira    yau da bakinta take cewa ta tsane ni,
Ya sunkuyar da kansh kasa cikin bacin rai,     haka dai musty yayita lallashin fahad har yadan samu nutsuwa,

  yanxu ke humaira me fahad yarasa da baki son shi,
inji khairat
uhum!
, kulsum ta ce
Kedai fada mata,
    wlh khairat ba dan yay fahad na yayana ba amma kema kinsan yafi lawal din nan"
Cikin bacin rai humaira ta daga mata hannu,  "ai haka zakice tunda ke kina son ya musty wlh kulsum da kinji yanda nake ji da baki fada min haka ba"
Khairat ta ce,
"me kike ji?
kawai idanuwanki sun riga sun rufe ne amma gsky humeee ki qara tunani
idan ma t kyau ne kinsan fahad ya nunka lawal goma
"dan allah ya isa haka" humaira ta fada,
ku barni inji da abinda ke damuna why cn't u understand me?
pls ku kyale ni hk Dan allah "
tamike tabar musu wuri tayi tafiyanta kallonta suke cikin mamaki
"Lallai humaira tayi nisa "
inji khairat,
Kursum ta tabe Baki tace  ai mu idan da sabo mun saba, khairat ta ce,
"toh allah ya kyauta" haka suka dan taba fira basu dade ba suka koma cen wurin humaira suka raka kairat tawuce gda

House of novella
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
               Nah
          💞Ayahart💞
                 70-75
Fahad kwance duk abin duniya yadame shi,
yanata tunanin wai ya akayi haka ne?,
miyasa nake son humaira da yawa? Wasu zafaffin hawaye suka riqa fita idanuwan shi lkcn da yake tuna zaman shi england har dukan mata yake,
mata biyar shi suke har gidan shi amma Sam baya kulasu,
sai gashi kanwar shi da ya girma da sonta tun tana karama yake son ta,
gashi ta tsane shi. tashi yayi ya nufi sashen su humaira ko ganinta yayi yaji sanyi. Koda yaje sai yatarar da musty da kulsum sunata fira cikin jin dadi da kaunar juna, HK shima yazauna akayita fira tare dashi baifi 2 mint ba sai ga humaira tashigo palon tana ganin fahad tadaure fuska har tayi niyar ta koma sai kuma dai ta tsaya sbd tasan musty bazai barta ba. Kulsum da musty kawai ke firar su cikin dabara musty
ya ce,
"kulsum zo ki raka ni wani guri"
suka fice suka barsu su biyu a palon.                         Ba Wanda yacewa wani ci kan ka ,
kowa da abinda yake saqawa a cikin ransa. Ganin haka humaira tamiqe zata bar Palon. Cen qasa da murya taji yakira sunanta,
''humaira!"
Tsayawa tayi cek tabashi baya,
yayi ajiyar zuciya sannan
ya ce,
"humaira zauna muyi mgn,"
"Ina jinka"
Ta fada batare da ta juwo ba,
"Humaira
Dan Allah ki tausayawa rayuwata wlh idan narasaki zan iya rasa rayuwa ta,
tajuyo tayamutse fuska
"karasa rayuwar ka mana,
wlh ya fahad da na aure ka kara na mutu taja tsaki
'"mtsw''
Sanya kai tayi zata wuce a karo na
biyu.
Bata Ankarba ba sai ji tayi yajawo ta da qarfi yana hawaye yana fadin
" pls humaira Dan Allah ki saurare ni,
humaira zuciyata zafi take zata fashe,
Cikin tsawa
Ta ce,
"Kai malam ka sake ni ko in ma rashin mutunci ynx wlh,
nace bana son ka, fahada bana son ka bana kaunar ka shin bazaka qyale ni na aure wnda nake so ba,?
Fahad
ya ce, cikin wani irin bacin rai da ko ita humaira saida ta tsorata,
ganin wata wuqa da yazaro,
" wlh humaira ki ka koma furta kalmar da kika furta ynxu sai na sanya wa kaina wuqar nan!"
Wata irin dariya tayi "hehehe"
Fahad ban San ka haihu ba kuma kana Kauna ta ba har  sai ka kashe kan ka,
Fahad idan ka kashe kanka kamutu kafiri,
ni I don't even care, sai ma in aure wanda nake s.........!,
karaf taji lkcn da yafadi kasa jini naxuba 'innalillahi wa'inna ilaihir raju'un tafada tana ihu Ya fahad!
Ya fahad!
kulsum da musty ne aguje suma sai suka sanya ihu,
tuni humaira tayanke jiki tafadi qasa somamma...

House of novella📚📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
              Nah
        💞 AYSHAT💞
             80-85
Kursum na shiga dakin sai tasamu humaira ta farfado tana kuka tadan tabe baki
ta ce,
"wai humaira kukan me kike haka?
kukan bai isa haka ba ne?
Duk dai abinda zai faruwa yariga
yafaru, 
ta kalle kursum cikin jajayen idanuwan ta
ta ce,
"haba kursum haka ma zaki ce?,
yakamata ai ke
ki fahimce ni idan ma kowa yakasa fahimta ta,
kursum kinsan ynda nadauki Ya fahad tamkar wnda muka fito ciki daya,
tayaya zan tsane Ya fahad irin wan nan tsanar?,
Kursum ina son inga Ya fahad,
ina son ganin Yaya fahad
Dan Allah ki taimaka min ki kaini wurin shi kursum NAYI NADAMAR maganar da na fadawa yayana kursum
NAYI NADAMA,
Dan Allah ki kaini wurin Yaya fahad inroqe shi gafara,"
Idanuwa
Kursum tazuba mata tana hawaye,
"kursum me ki kewa kula?,
kada dai
kicemin Yaya fahad ya rasu,
tasake fashewa da wani matsanancin kuka
ita kanta kursum sai da taji tausayin ta duk da irin haushin ta da takeji  a kan abinda tayiwa yayanta.
Zuwa tayi ta rungumeta tana
fadin
" kiyi hakuri humaira har kisamu qarfin jikin ki "
Yaya fahad yana nan da ranshi kiyi hakuri zuwa gobe kije ki ganshi"
Bazan iya bari gobe ba kursum"
Ta fada cikin shashekar kuka
"pls muje kikaini wurin Yaya fahad Dan Allah" Kursum tarasa yanda zatayi da humaira dole tariqata hakanan suka doshi dakin da aka kwantar da fahad.
Tun da suka tura qofa gabanta
ke faduwa ganin yanda fahad
yake
kwance,
wata irin harara musty ya watso mata saida hanjinta suka
koka
San nan yafada cikin  tsawa
"me yakawo ki nan?, Zuwa ki kayi ne ki
ida  kar kare kashe shi, Wlh maza kifita daga dakin nan tun kafin ranki  ya baci,
Ya nuna  kursum da yatsa
"ki fita da ita kafin in bude idanuwana"
ganin irin bacin ran dake tattare da musty ne
yasan ya  kursum taja humaira suka bar dakin,
Nan fah humaira ta hau Sabon kuka tana fadin
" nashiga uku kowa yayi fushi dani,
kowa ya tsane ni wayyo ni humaira ina zansa kaina,"
itama kursum din kuka take ba mai lallashin wani,

House of novella📚📚
         For comment and correction
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: NAYI NADAMA😭
           Nah
     💞Ayshat💞
           75-80
Asibitin da musty ke aiki aka nufa da su don ceto rayuwar fahad,

Ko da humaira ta falka kawai taganta kwance kan gadon asibiti,
''innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ta fada a bayyane lkcn da ta ke tunano abunda
yafaru
"na shiga uku ni humaira yazanyi da rayuwa ta idan Yaya fahad yarasa rayuwar shi a kaina,
nan take duk taji ta tsane kanta,
ta kife kai a gwuiwa tanata rusar
kuka,
"kukan me kike bayan kin samu ynda kike
so?
Humaira kin kashe Dan uwanki hankln ki ya kwanta"
Inji Momy itama sai kukan take,
humaira tadago idanuwan ta da Suka rine  jawur,
cikin razana da tashin hankali
Ta ce,
"Momy me kike nufi ne?
Momy  Yaya fahad ya rasu?
Momy Ku kaini wurin Yaya fahad Dan Allah wayyo Momy na shiga uku!
Nan take ta sake zubewa qasa idanuwan ta suka birkice sai wasu kumfa ke fita bakin ta,
tuni Momy tayi tsale ta fita tana kiran
likita.
Dakyar aka samu kan humaira,
sai dai har ynx bata far fado ba,.     
Shi kuma fahad tun lokacin da a kazo
dashi likitoci
suke kanshi,
shima daqyar aka samu jinin ya daina zuba.
Musty ne yafito daga dakin da likitoci suke akan fahad,
yana fitowa su yakumbo sukayo kanshi cikin tashin hankali ya tsaidasu da hannun shi yana
ce wa,
" Alhmdlh Ku kwantar da hankalin Ku insha allahu zai samu sauqi saboda anyi sa'a abin gefen cikinshi ne ba tsakkiya ba,
  kuma bai yi zurfi ba zai farfado  zuwa safe insha Allah''
Abba ya ce,
alhamdulillah Allah abin godiya,
Yakumbo sai kuka take tana,
" Allah yabaka lafiya fahad"
Duk suka amsa da
"Ameen"
Dady
ya ce,
kursum ki tsaya wurin humaira shi kuma mustapha ya tsaya wurin fahad,
mukuma zamu wuce gida sai gobe da safe idan Allah ya kaimu Duk suka karba da toh dady.,

House of novella📚📚
08100376392
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
             Nah
     💞AYSHAT💞
           85-90
Haka su ka kasan ce har qarfe ukun dare ganin  zaman ba zai  yi ba ya sanya ta tashi taje ta dauro alwala tazo tafara slh, 
bayan taqare
tafara jero adduo'i
"ya ubangiji ina roqonka da sunayen ka kyawawa wadanda ka kira kanka dasu,
da wadanda annabawan ka suka kiraka dasu,
da wadanda ka barwa kanka sanin su ,
ya ubangija kai kasan abinda ke bayyane da boye,
ya Allah kabaiwa wannan bawa naka lfy ubangiji kayafe mishi kura kuranshi.
Ya ubangiji kai kasan abunda ke cikin zuciyar bayin ka,
Ya ubangiji zabin ka nake nema kai kasan abunda ke alkhairi a gare ni,
Ya sarkin sarauta kayimin zabi mafi alkhairi,
Ya ubangiji idan har ya fahad ne alkhari agare ni ya ubangiji ka sanya min son shi a zuciya
ta, ka kar kare min Lawal cikin zuciyata mutumin da ko kula Dani bayayi yadauka ka harakar shi akan tawa ubangiji kabani ikon yin biyayya ga iyayena kasanya son fahad azuciyata idan har shine alkhairi agareni."
Haka dai tayita adduo'i har akayi asuba,
Koda kursum ta tashi nan tasameta kan sallaya,
Ita ma taje tadoro alwala tayi slh
San nan suka Dan kishingida,
misalin karfe 6:30 am humaira ta miqe ta nufi dakin da fahad yake takoyi sa'a bata taradda musty ba.
Ta nufi inda yake ta gurfana qasa dai dai kanshi
har ynx dai bai farfado ba,
Ahankali tafara mgn tana
ce wa,
"Dan Allah Ya fahad ka tashi,
Yaya na dan allah ka
yafemin nayi nadamar abinda nayima,
ya fahad Dan Allah katashi kayimin mgn kozanji sanyi,
Ya idan narasaka
nima mutuwa zanyi,
ta sunne kanta dai dai fuskarshi tana kuka mai ban tausayi,

A hnkl hawayen humaira suka fara sauka qirjin shi yadan bude idanuwan shi kadan ya kuramata su cikin wani yanayi mai nuna alamun tausayawa,
yadan saita bakinshi dai dai kunnenta  da kyar yake mgn
ya ce,
cikin wani irin sauti
"ya isa haka humaira"   razane ta dago kanta idanuwan ta cike da hawaye,
suka hada ido ya sakar mata lallausan murmushi San nan yasake maida idanunwan shi ya  lumshe,

House of novella📚📚
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi Nadama😭
         Nah
     💞AYSHAT💞
            90-95
Jikin shi tafada tana hamdalah ,
      fahad yadan yunkura alamar yana so yamiqe,
tayi hanzarin kamashi ta jinginashi kan pillow.
Ya ce,
"Zanyi slh "
Ta mike cikin sauri taje ta hada mishi ruwan alwala,
Ta dan riqa shi ganin jkn na shi ba wani karfi toilet ta kaishi sannan tadawo ta shimfida mishi pray mat,
Bayan yajero sallolin da ake biyar shi ne ya Dan jingina bakin gado,
Ya lumshe idanuwan shi, humaira
Tadan sunkuyar da kanta qasa
Ta ce,
"Ya jikin ka"
"Da sauki"
yafada ba tare da ya bude idanuwa shi ba,
A hnkl tafara sheshekar kuka,

"humaira"!
ya kirata tare da bude idanuwan shi ya  kura mata su'
"na'am"
ta amsa murya daqushe,
ya ce,
"narasa meyake damuna humaira I hv been a little crazy, tadan dago kanta ta kalle shi,
yaci gaba da
ce wa ,
"i dn't knw wat to do about the strange feelings deep in to my hrt, "
humaira tun kina Yar mitsitsiya Allah yasanya  min kaunar ki  cikin rayuwata,
Nayi regrating nuna kauna ta
a gare ki  humaira na hakura dake kije ki aure duk Wanda kike so ki aura,
i wan to see u happy, ta dago ta dube shi cikin mamaki,
yadaga mata gira alamar dagske yake, zatayi mgn Kenan aka turo qofa aka shigo musty ne da kursum,
wani kallo must yake mata cikin tsana,
"me yakawo ki nan?
Banyi miki kashedi da dakin nan ba?"
Hawaye suka kwaranyo mata wai miyasa Yaya musty yatsaneta ne?
Ta fada cikin ranta,
fahad ne yadakatar da shi da cewa, haba malam bawurinka  fah tazo ba Dan Allah ka qyaleta mana,
itama kursum tasa baki sukayita bashi magana har yasauko, tamiqe jikinta ba kwari taje tahado tea tazo tazauna daf da fahad tana bashi a baki,
shiko gogan  sai kallon ta yake Duk mamakinta
yacikashi,
Sallamar su dady tadawo dashi cikin dogon tunanin dayake, sunyi murna sosai ganin fahad yasamu
sauki ,
sai dai wani irin kallo sukewa humaira cikin tsana da bacin rai bama kamar
yakumbo,
Da tafara soka mata mgn,

House of novella📚📚
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
              Nah
       💞AYSHAT💞
             95-100
  Momy ko sai wani kallo take mata tana hararar ta ganin hk yasa humaira takara tsanar kanta,
Umman fahad ce kadai tayi mata ya jiki,
Gainin tsanar ta a idon mahaifin ta ne yasa ta fashe da kuka,
Fahad ya runtse idanuwan shi sbd shi kadai yasan Abunda yake ji bazai iya jure kukan ta ba,
Sai a lkcn yakombo ta sake mgn,
Ta CE,
" toh alhmdlh godiya zamuyi wa Allah  da  yata da mana kai bata kai ga cinma burin ta ba na illata ka,
ynx duk wata mgn daza ayi qara ayita tun dawuri,
ynx dai kai fahad dole ne ka hakura da ita tunda kaga ynda al'amari yakasance yarinya na neman tarabaka da rayuwarka
A banza,
  kayi hakuri kaje ka nemi wata ka aura, dady
ya ce,
" hk shine dai dai don nan gaba sai dai muje musame gawarshi, qara kabar shi dawuri tun kafin  nadama da danasani tabiyo baya,"     Fahad ya dube iyayen shi
ya ce,
"Dady na hakura da ita amma dan allah ku daiba ganin laifin humaira dady bafa laifinta bane laifina ne nima kuma rudin shaidan ne,
musty ya katse shi da ce wa,
"gafara cen malam kai miyasa baka ganin laifin humaira ne akan komai?
Yarinya tana nema tarabaka da rayuwarka amma.....
Umma tayi karaf takarbe da cewa "jama'a bai fah dace adorawa humaira laifi ita kadai ba,
shima fahad din yanada laifi a nawa ma gani yafi ta laifi,"
momy ta ce
"haba Hajiya yazakice haka ai komai yafaru wlh ita taja don datayi mana biyayya tun farko da hk bata faru ba,
Humaira ta fashe da wani matsanan cin kuka ynx kowa ni yake xargi kowa yadauko laifi ya Dora min,
fahad yadan riqe hannun ta yana lallashin ta,
Allah sarki ta fada a cikin ranta
"ynxu duk halin da Yaya fahad yake ciki bai kula da ni nasa ka shi ciki ba gashi duk dangina sun bani baya hatta da mahaifiyata amma banda Yaya fahad take taji duk  tausnyi shi ya kamata nan take taji ta fara tsanar Lawal ace duk halin datake ciki ta sanadiyar shi tashiga amma ko sau daya bai kirata ba.
Maganar yakumbo tadawo da ita cikin tunanin da take tana cewa
"ban yarda ba ban a mince ba ko bayan raina ban aminta fahad ya aure humaira" inalillahi wa'ina ilaihi raji'un ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, bata sake katsewa ba saida taji dady nacewa
"toh kaji fahad tsakanin ka da humaira sai yan uwantaka mgnr aure ta kare bakai ba humaira, shima kanshi fahad baqaramin tshin hnkali yashiga ba,
Ya runtse ido cikin kuka yana
ce wa,
"shike nan dady na hakura da humaira na hakura da ita har abada,  dady kamun izini gobe inbar kasar nan,
gaba dai dakin sun shiga tashin hnkl jin abunda ya furta,
Dakin yayi tsit
kukansu humaira kawai  kakeji,
a hnkl humaira ta miqe taje tagurfana wurinsu dady tana fadin
"dady Dan Allah Ku gafarce ni dady kuyimini rai wlh dady ina son Yaya fahad zan aure shi,
kuyafemin dady nagane kuskure na NAYi NADAMA dady kuyi min rai kada ku bari ya fahad yabar kasar nan,

House of novella📚📚
[5/10, 3:42 PM] KAURA: Nayi nadama😭
              Nah
       💞AYSHAT💞
             95-100
  Momy ko sai wani kallo take mata tana hararar ta ganin hk yasa humaira takara tsanar kanta,
Umman fahad ce kadai tayi mata ya jiki,
Gainin tsanar ta a idon mahaifin ta ne yasa ta fashe da kuka,
Fahad ya runtse idanuwan shi sbd shi kadai yasan Abunda yake ji bazai iya jure kukan ta ba,
Sai a lkcn yakombo ta sake mgn,
Ta CE,
" toh alhmdlh godiya zamuyi wa Allah  da  yata da mana kai bata kai ga cinma burin ta ba na illata ka,
ynx duk wata mgn daza ayi qara ayita tun dawuri,
ynx dai kai fahad dole ne ka hakura da ita tunda kaga ynda al'amari yakasance yarinya na neman tarabaka da rayuwarka
A banza,
  kayi hakuri kaje ka nemi wata ka aura, dady
ya ce,
" hk shine dai dai don nan gaba sai dai muje musame gawarshi, qara kabar shi dawuri tun kafin  nadama da danasani tabiyo baya,"     Fahad ya dube iyayen shi
ya ce,
"Dady na hakura da ita amma dan allah ku daiba ganin laifin humaira dady bafa laifinta bane laifina ne nima kuma rudin shaidan ne,
musty ya katse shi da ce wa,
"gafara cen malam kai miyasa baka ganin laifin humaira ne akan komai?
Yarinya tana nema tarabaka da rayuwarka amma.....
Umma tayi karaf takarbe da cewa "jama'a bai fah dace adorawa humaira laifi ita kadai ba,
shima fahad din yanada laifi a nawa ma gani yafi ta laifi,"
momy ta ce
"haba Hajiya yazakice haka ai komai yafaru wlh ita taja don datayi mana biyayya tun farko da hk bata faru ba,
Humaira ta fashe da wani matsanan cin kuka ynx kowa ni yake xargi kowa yadauko laifi ya Dora min,
fahad yadan riqe hannun ta yana lallashin ta,
Allah sarki ta fada a cikin ranta
"ynxu duk halin da Yaya fahad yake ciki bai kula da ni nasa ka shi ciki ba gashi duk dangina sun bani baya hatta da mahaifiyata amma banda Yaya fahad take taji duk  tausnyi shi ya kamata nan take taji ta fara tsanar Lawal ace duk halin datake ciki ta sanadiyar shi tashiga amma ko sau daya bai kirata ba.
Maganar yakumbo tadawo da ita cikin tunanin da take tana cewa
"ban yarda ba ban a mince ba ko bayan raina ban aminta fahad ya aure humaira" inalillahi wa'ina ilaihi raji'un ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare, bata sake katsewa ba saida taji dady nacewa
"toh kaji fahad tsakanin ka da humaira sai yan uwantaka mgnr aure ta kare bakai ba humaira, shima kanshi fahad baqaramin tshin hnkali yashiga ba,
Ya runtse ido cikin kuka yana
ce wa,
"shike nan dady na hakura da humaira na hakura da ita har abada,  dady kamun izini gobe inbar kasar nan,
gaba dai dakin sun shiga tashin hnkl jin abunda ya furta,
Dakin yayi tsit
kukansu humaira kawai  kakeji,
a hnkl humaira ta miqe taje tagurfana wurinsu dady tana fadin
"dady Dan Allah Ku gafarce ni dady kuyimini rai wlh dady ina son Yaya fahad zan aure shi,
kuyafemin dady nagane kuskure na NAYi NADAMA dady kuyi min rai kada ku bari ya fahad yabar kasar nan,

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
               Nah
       💞AYSHAT💞
               102
Sannu sannu  wata irin shakuwa ta shiga tsakanin fahad da humaira  duk da ita har tym din bataji son fahad a cikin ranta ba,
Amma zata iya zama dashi ko sbd farin cikin iyayen ta,
Har ynx ganin ta ke kaman ta ci amanar Lawal,

Fahad da humaira zaune a Farfajiyar gdn suna ta firar su irin ta masoya,
Wayar da ke hannunta ta dauki ruri,
Ganin no ce ba suna yasa taki daukan wayar,
Fahad ya ce,
"Me yasa idan ana kiran ki bakya son dagawa ne,?
"No ce kawai ba suna"
"Toh kika Sani ko wani important call ne ai kara ki daga......."
Bai ida rufe bkn shi ba wayar rasake daukan ruri,
A hnkl ta dauka tare da yin slm,
Cikin sanyi jiki ta sauke wayar tana kallon fahad,
"Me yafaru ne " ya tmby,
Cikin rawar murya
ta ce,
"Lawal ne ya ce yana bakin gd"
Lkc daya fuskar fahad ta chanza yadaure fuska ya ce,
Ke kuma kika ce mishi me,?
A sanyaye ta CE
" ya fahad Dan Allah kamin uzuri inje inbawa Lawal hk kada yaga kaman na yaudare shi,"
    Ya ce,
"Duk hkrn da su Abba Suka bashi bai wadatar ba ne,
sai  yazo yaji naki,
Ganin ba ynda za ayi ya barta taje yasanya ta shiga yimasa magiya tana hada shi da Allah yabarta taje,
Ya tabe Baki
Ya ce,
Kin San Allah wlh minti 5 nabaki kuma kika wuce su sai kinga fishi na,
Ta karba da
"Insha allahu "
tare da mikewa.
 
Yau ma tsaye yake ya harde kafafuwan shi tare da jin ginawa kan motar shi kan shi a kasa,
Slmr humaira ce tasanya yadago kanshi,
Ya tsura mata idanunwan shi masu daukan hnkl da tafiya da nutsuwar Wanda aka duba dasu,
Ba tare da ya amsa slmr ta ba,
Yafara mgn,
" me yake damun ki humaira kika daina daga waya ta,?
Humaira iyayen ki sun zomun da wata mgn kan cewa za a hada ki da Dan uwan ki gsky ne ko dai don suna son su raba ni da ke ne?
Wasu hawaye masu zafi Suka riqa kwaran yowa idon ta,
Ta ce,
"Duk abunda iyaye na Suka fada maka gsky ne"
Cikin tashin hnkl
ya ce, " kin  daina so na ne?"
"Har ynx ina kaunar ka amma ba ynda zanyi dole inyiwa iyaye na biyayya,"
"Qarya kike humaira kin daina  kaunata, idan kuma har da gsk kike me zai hana kizo mugudu muje wani guri a Daura mana  aur..........."
Saukar marin da yajii ne ya katse mishi mgn,
Ta nuna shi da yatsa,
Ta ce,
"Ashe dama kai bakada hnkl,
Lawal nayi nadamar saninka arayuwa,
Ashe dama ba kaunata kake ba,? Lawal
Da kana kaunata da bakayi wannan FURUCI ba,
Cikin sarkakkiyar murya yace ni kika Mara humaira?
A hnkl tafara ja da baya ganin ynda idanuwan shi Suka chanza lkc daya,

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
               Nah
       💞AYSHAT💞
                103
Cikin zafin nama ya fizgota a fusace ya CE,
"Humaira ni kika gayawa wannan mgn?"
Da kinsan ko waye Lawal da Baki daga hannu kika mare ni ba ,
Da kinsan ko waye Lawal da Baki fadi munanan maganguna kaina ba,
Amma ina mai tabbatar miki da cewa duk lkcn da kikasan ko ni waye sai kinyi nadamar sanina a duniya,
Humaira wlh sai kinyi nadamar auren duk wani da namiji da ke fadin duniyar nan , sai na maida ki Abun tausayi a idon jama'a.
Kuma ki rubuta ki ajiye wlh wlh sai na aure ki matukar ina nunfashi a doron kasa, "
   " Nafi karfin ka Lawal,
Ni ga Allah na dogara kuma natabbatar da xai kare ni ga duk kan sharrin ka,
wlh ba abunda zaka mun face abunda Allah ya kaddara a gare ni,
Kaje kayi duk abunda zakayi ta Allah ba taka ba"
tana kare  fadar hk ta juya da gudu tayi gd tana kuka,
Fahad da ke zaune a hasale idanuwan shi cike da masifa da tsananin kishi,
Ganin ynda ta shigo gidan tana kuka ne ya kara kufular dashi, wato kuka ma take kukan rabuwa da masoyin ta kenan.
Cikin hanzari ya tare ta yafara balbala mata ruwan masifah,
"Humairah wannan kukan duk na rabuwa da masoyi ne meyasa kika bari yaje kije ki dawo dashi Ai yafi wannan kukan"
Ya juya da niyar ya wuce ta jawo hannun shi tana cewa,
"Wlh ya fahad ba hknan ba ne"
Jan shi tayi tamaida shi inda yk zaune sannan ta kwashe duk abunda sukayi da Lawal ta gaya mishi,
Ya tsorata matuka jin abunda tace amma bai nuna mata hkn ba kawai ya lallashe ta tare da kara bata hkr da kalamai masu kwantar da Hnkl..

📝House of novella 📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadamah😭
            Nah
     💞AYSHAT💞
            105
Fahad ya Karba da ameen tare da kara kwantar mata da hnkl ,

Kwance tashi asarar mai rai yau saura 2wks auren fahad da humaira,
Misalin karfe 4 na asuba humairah ta mike a razane sakamakon mummunan mafalkin da tayi,
Wai gatanan a cikin irin cage dinnan da ake sanya bayi a ciki lokcn dori,
Wasu katti janye da ita da wasu mata wadan da ga alama suma bayi ne amma sun saba da su,
Da wani mutum Wanda bataga fuskar shi ba ana dauke dashi cikin wata irin karagar mulki,
Ana tafe da ita tana kuka tana kiran ya fahad kazo ka taimake ni zasu tafi dani,
Da Gudu ta hango shi yana kiran sunan ta,
A wahalce ya karaso gurin su tare da zubewa yana kiran
"Dan Allah kada kuje mun da mata naroke Ku da Allah Ku barmun matata,"
Mutumen da Batasan ko waye ba yayi nuni da aka ma fahad a yanka shi,
Wani kato da ga cikin kartinnan ya zaro wata irin katuwar wuka da niyar ya yanka shi,
Wata irin guguwa ta taso mai karfi wadda tasanya lkc daya ta daina ganin kowa,
Sai dai wani kukan wasu halittu mai ban tsoro,
Inalillahi wa'inna ilaihirraji'un ta fada tare da mikewa duk ilahirin jikinta rawa yake ga wani gumie da ya jiketa kaman ba lkcn sanyi ba,
A hnkl ra riqa Kara to addu'ar da akeyi idan anyi mummunan mafalki sannan taje tadoro alwala tayi slh ba ita ta tashiba sai asuba.
Tun lkcn da tayi wannan mafalkin ta tsorata matuka kuma a kai2 tana yawaita mafalkan kusan iri daya takasa hkr sai da ta sanar da fahad,
Fahad ya CE,
"Wannan ba komai ba ne kinsan lkcn sanyi mutane sun cika irin wadannan miyagun mafalkan,
Kawai kici gaba da ardu'a tare da nemawa jikin ki tsari da azkar din Safiya da maraice,
Haka yayita yimata nasifa har taji nutsuwa a cikin zuciyar ta..........

HOUSE OF NOVELLA📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭 
             Nah
     💞AYSHAT💞
             104
Ynx humaira ta manta da zancen wani Lawal sbd yawaita addu'ar da take, ynx matsala daya yawan faduwar gaban da take yi duk sa'ilin da ta tuna dashi kuma faduwar gb mai tsanani,

Yau  an sanya ranar bikin su humaira murna gurin su fahad ba a ma mgn,
Dukan su suna dakin yakumbo anata fira cikin jin dadi,
Mgnr  da sukaji a tv ne ya sanya Suka maida hnkln su a tv Baki daya,
Wasu terrorist ne aka kama yayin da aka nuna wani mutum a photo Wanda shine babban su kuma ya Gudu,
Duk wnda ya kawo shi a Raye ko amace za'a yimishi kyauta mai tsoka,
Kuka humaira ta sanya ganin ba photon kowa ba ne face Lawal,
Dagudu ta bar dakin tayi dakin ta tana ta kuka kaman ranta zai fita,
A hnkl fahad ya tura dakin ya shiga,
Ganin irin kukan da humaira keyi ba karamin tada mishi hnkl yayi ba
Tsayawa yayi bakin kofar Dakin yakasa
shiga kuma yakasa fita abubuwa da yawa rayuwar shi take ayyana mishi game da kukan nata,
Jin motsin shi da tayi yasanya ta dago kanta idanuwan ta tab da hawaye,
Tayi mishi wani kyakkyawar duba ta sake maida kanta tana kuka,
Fahad yayi gyaran murya yace,
"Humaira kuka kike don kin gane sana'ar saurayin naki ko?,",
Yayi murmushi mai nuna takaici da damuwa sannan yaci gaba da cewa
"Humairah natabbatar da wlh har zuwa ynx kina kaunar wannan Dan ta'addan,
Wannan kukan da kike yana matukar bakanta mun rai da wannan kukan da kike da ma zuwa kikayi kika memo shi kuka Gudu kamar ynda ya bukata a baya,"
Yana qare fadar hk ya juya zai wuce,
Da Gudu humaira ta zo ta rungume shi ta baya ta Dora kanta kan bayanshi tare da fadin
"Hb ya fahad me yasa zakace hk me yasa baxaka fahimce ni ba,
Ya fahad kada kishi yarufe ma ido ka furta Kalmar da zakayi da nasani aciki, kaima kasan na fitar da Lawal a cikin zuciyata,
Kawai dai ina tausayin kaina ne," ta sake fashewa da kuka,
Duk jikin fahad yayi sanyi tausanyi humaira ya kamashi a hnkl ya juyo tare da kara matseta gam a kirjin shi, a hnkl ya rada mata" don't worry everything will be olryt"
Ta janye jikinta ta koma tazauna
Fahad yadawo kusa da ita ya zauna yana lallashin ta,
Ta ce,
"Ynx ya fahad dama Lawal Dan ta'adda ne ba navy ba ne,?
Fahad yayi murmushi yace
"Shiyasa aka so a rabaku tun farko, ynx hk ma su dady ne sukayi sanadiyar gane ko shi waye kuma ta dalilin Neman auren ki,
Humaira ta dafe kirji ta CE, "kaman ya Yaya?"
Yace,
Personal dinsu Suka zuba akata buncike Ashe ma Dan nijer ne ba Dan yola ba ne nan ma garin da yake zuwa yaxo kara tan tance gidajen da zasuyi sata ne,"
Cikin sanyi jiki race
"Allah nagode ma da ka bani ikon gane true colour nashi Allah ya kara tsare ni da dukkan sharrin shi'"

Masoya wannan littafin kuyi hkr kunjini kwana 2 shiru tafiya nayi inasha allahu zanyi kokari na kamnala shi cikin2 wks

Ayshart

HOUSE OFc  NOVELLA📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
     💞AYSHAT💞
           106
Yau ranar Asabar an Daura auren fahad da humaira, mustapha da kursum,
Anyi shagali Wanda yake shi ne,
Inda aka dauke amare aka kaisu muhallin su da ke Nasarawa g r a.
Gd ne plat mai kyau zaman mutum daya,
Lkcn da aka bar humaira ita kadai wani nishadi take ji yana ratsa zuciyar ta,
Pillow ta jawo ta kara bayanta ta dan kishingida,
Fahad yashigo da slmr shi tsayawa yayi kanta yana kallon kykkyawar fuskar ta,
Kunya takama humaira tajawo mayafi ta rufe fuskar ta,
Yayi murmushi yana godewa Allah a ranshi da yaba shi humairar shi .
Yakarasa gurinta ya zauna tare da yaye mayafin yana cewa,
" kada kimun rowar ganin wannan kyakkyawar fuskar taki humaira yau ina cikin farin ciki marar misaltuwa da Allah ya mallaka mun ke matsayin mata ta,
Humaira ki tashi kije ki doro arwala mugodewa ubangijin Mu da ya nuna mana wannan ranar,
Taje ta doro arwala Suka gabatar da slhr ma'aurata sannan yakama kanta yayi mata addu"a,
Shi yarika bata naman a baki tare da fresh milk har ta koshi,
Ta kwashe kayan ta kaisu kitchen,
Koda ta dawo bata sameshi dakin ba kwanciyar ta tayi har ta fara bacci,
Cen fahad ya shigo cikin shirin Bacci yadurkusa a hnkl ya sumbace Dan karamin bakinta mai kyau da tsantsi
Ta bude ido a hnkl tayi murmushi tare da fadin
"Ka barni bacci zanyi"
Ya haye gadon ya dagota ya rumgume ta a jikin shi,
Ya ce,
"Tsaya na rage miki kayan jikin ki ko maji dadin baccin ko ya kika ce?
Ta turo Baki "nifah bana so"
Ya shiga cire mata kayan ganin da gsk yakai yasanya tafara yi mishi magiya ,
Hnkln fahad baya kanshi ganin irin halittar fatimar shi,
Ya mannata kirjin shi ya shiga rada mata I luv u humaira i cnt leave wit out u, ke ce   rayuwata
Ya sumbace ta a kunne tsigar jikinta taji yana tashi kamshin turaren shi mai kamshi da dadin tsiya ya soma kashe mata jiki,
Ture shi ta shiga yi amma ko gizau sai ma yashiga yi mata wasu abubuwa masu rikitar wa,
Tun tana kuka tana magiya har ta gaji ta daina daren ranar fahad bai saurara mata ba har sai da ya maidata cikakkiyar macce,...........

HOUSE OF NOVELLA📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭       
           Nah
    💞AYSHAT💞
           107
Kiran slhr asuba  ne ya falkar da shi, humaira na manne a jikin shi,
Wani farin ciki yake ji da baisan iyakar sa ba,
Ya kunna shudiyar fitila ta ccita,
Ta haska humairah sai yaga takara yi masa kyau, tana ta baccin ta,
Nunfashin ta yana saula a hnkl,
Yasa hannu yana shafa tattausar fuskar ta,
Ta bude ido, a hnkl ya rada mata
"Humaira asuba tayi, tashi muje muyi wnk lkcn slh yayi"
Hannu tasa ta ture shi ta juya wani baren ya mirgino gaban ta
" haba babyn fahad tashi mana ko bazaki iya ba?"
Ta wasto mishi harara ta langabe masa ga sanyin asuba yana busata,
Ya yaye mata bargo ta kankame shi,
"Ka kyaleni bacci ya dame ni"
Daukanta yayi gaba dayan ta yayi toilet da ita ya rinka rarrashin ta yana gasa mata jikinta.
Sai da Suka kintsa sannan suka doro alwala
Shi yayi musu limanci sukayi sallar a gida don bazai iya fita yabarta ita kadai ba,
Yadaga hannuwa sama yana yiwa Allah godiya tare da kwararo ma humairan shi addu'a
Yana shafa addu'a ya juyo ya ganta kwance kan dadduma ta kanannade sanyi take ji
Dagota yayi Suka koma kan gado yayi mata runfa da jikin sa,
Yaja bargo ya rufesu ga ba daya,
Wata irin kauna da shakuwa mai tsanani ce ta shiga tsakanin su yana tsananin kaunar humairar shi ita ma tana tsananin kaunar fahad dinta tare da girma ma shi.

Watan su 2 da aure humaira tayi fari Tamara kyau fatar ta sai sheki take
Tana sanye da wani wando iya guiwa da wata Yar mitsitsiyr Riga ta raba kanta gida 2,
Fahad na zaune yana kallon news ta zo ta dale cinyar shi cikin shagwaba ta ce,
"Yaya ina goruba da nace ka siyomun?"
Yarike Baki
"Allah na manta kanwata,
Wai ma meye sirrin? Naga fari kawai kike karawa yafada
Yana taba cikin ta,
anya wannan cikin  ba ajiyar baby na a ciki?"
Ta sunne kai a kirjin shi
"Ni ba komai a cikina"
Ya ce,
Ban yadda ba humaira gayamin gsky"
"Nima ban sani ba amma tun last mnth bnga period dina ba"
Ta fada tare da rufe fuskar ta,
Ya jaye hannayen ta tare da kurawa kykkyawar fuskarta idanuwa zo muje in duba ki,
"Ni fah ba ynx ba kabari sai gobe"
"Toh naji banni nayi kallon news plz"
"Ni gsky Yaya kaje ka siyomun goruba ta"
Ganin bazata bar shi ba yasanya ya mike tare da daukan makullin motar shi,
Ya fita baifi 30 mnt da tafiya ba hadari yafara haduwa aka fara iska mai karfi hnkln humaira duk ya tashi gata da tsoron chida cen  kuma aka dauke wuta Jikinta sa kyarma ya ke hnkln ta yayi mummunan tashi,
Ta lalube fitilar wayarta ta haska ta shige daki jikinta sai kyarma take gashi anfara walkiya makurewa tayi cen karshen gado tana addu'a
Ana cikin HK taji tsayuwar mota ta Gudu ta fito har tana tuntube tana kawowa baking kofar dakin akayi wata irin tsawa tare da sakowa da ruwa masu karfi batasan sanda ta sake komawa ciki da Gudu ba tare da ihu mai karfi,..........

HOUSE OF NOVELLA📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadam😭
        Nah
   💞AYSHAT💞
           108
Da sauri fahad ya karaso dakin yana kiran sunan ta makure ya sameta duk ilahirin jikinta rawa yake a hnkl ya karasa gurinta yana jijjigata
"Humairah me yafaru bude idanuwan ki gani nadawo"
Fadawa tayi jikin shi ta saka kuka tana fadin "ya fahad tsoro nake ji "
Ya matseta gam a kirjin shi yana lallashin ta
"Yi shiru humairah ba abunda zai same ki ganinan tare da ke"
"Ya fahad gabana ke faduwa ganin nake kaman wani Abu zai same ni"
"Yi hkr humairah ba abunda zai same ki matukar ina tare
da ke",
Kankame shi tayi tana maida nunfashi,
Ganin yanda take ne yasanya fahad daukanta gaba daya ya dora kan gado yayi mata rumfa da jikin shi.
Tana manne Jikin shi har bacci yayi awon gb da su,
Bugun gidan da ake ne da karfi yasanya fahad ya mike,
Itama humairah mikewa tayi tare da fadin
"ya kada ka fita dare yayi fah"
"A'a humairah bugun gdn yayi yawa bari naje naga ko waye kila ma maigadi ne bamu Sani bah koh wani Abu ya same shi,
Tare Suka fita bakin palon sai dai kash! Kafin su bude gdn tuni an cire kofar an shigo,
Innalillahi wa'inna ilaihirraj'un su kafada lkc daya ganin mutanen da Suka shigo ko wane fuska rufe da mask dauke da miyagun makama,
Tun kan kofa aka fara ball da fahad har cikin daki, humairah sai kuka take tana cewa Dan Allah kuyi hkr Ku daina dukan shi komai kuke so kufada za'a baku,
Wani daga cikin su yayi mgn da kakkausar Maurya
"Kina da abunda zaki ba Mu be?'"
Rass!
Gabanta ya fadi domin tunano muryar mai maganar
Kafin tayi mgn ya nuna fahad da bindiga
"Rayuwar wannan nake so zaki bani",
Faduwa tayi kasa tare da riqe kafafuwan shi tana rokon shi
"Dan girman Allah kuyi hkr kada Ku kashe mun miji wayyo ni Allah Dan Allah kuyi hkr..........
Tas! tas !tas!
Kake ji lkcn da wani ya kai mishi bugu da wani irin katon kulki   sannan aka  dauke shi  da bullet ya fadi kasa jini na zuba,
Da Gudu takarasa gurinshi tana jijjiga shi "ya fahad ya fahad" ina ba ko alamar motsi a tare dashi,
Kafin tayi wani Abu tuni an shaka mata wata powder ta fadi kasa sumamma Suka dauketa sukayi gb akabar fahad kwance cikin jini

HOUSE OF NOVELLA📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
            Nah
     💞AYSHAT💞
              109
Koda humaira ta falka sai ganin ta tayi zagaye da mutane anata shewa innalillah wa inna"ilahirraju'un ta fada lkcn da ta tashi zaune take ta fara tunano abunda ya faru da ita,
Kuka ta sanya ta nuna Lawal da yatsa
"Ka cuce ni Lawal ka cuce rayuwa ka rabani da masoyi na Abun kaunata wayyo ni Allah Yaya na,
Yayi wata irin dariya sannan lkc daya kuma ya sha toka ya dube humairah a wulakance
"Dama ba nagaya miki ba?,
Ba'a ja da ni ,
humairah bari ingaya miki abunda Baki Sani ba ni Lawal ba a furta mun a na so na kuma daga baya a juyamun baya
Sai kuma gashi anyi rashin   sa'a da bantaba son wata macce ba kaman ynda nake son ki
Humairah kece rayuwata bazan iya rayuwa ba tare da ke ba,?
Zan iya aikata abunda yafi hk domin in mallake ki,
Cikin tsawa da rashin tsoro humairah ta cw
"
Karya kake Lawal ni Nafi karfin ka kuma kasani bazan taba zama mallakin ka ba har abada,
Naso ka a da kuma daga baya nayi nadamar saninka ma a rayuwata,
So daya ne tak,
Kuma fahad nakema shi,.......
Saukar mari taji a fuskarta cikin bacin ran da saida ta tsorata taga Lawal cikin tsawa yace,
Kujaye mun ita kuje kukaita daki ,
Take wani kato ya dauketa a kafada yayi daki da ita

Shi kuwa fahad tun lkcn da Abun yafaru akayi assibiti dashi ganin anceto rayuwar shi anyi Nasarar cire bullet din, don  a kafada ne aka harbe shi sai dai tun  lkcn ko yaushe cikin kuka yake ya rame yayi Baki  yazama kaman wani zararre bashida mgn saita humaira,
Su Abba sunyi iya bincike har sungaji ba lbrn humairah ba samatar ta,
Tun suna daukan Abun da sauki har sunfara tsorata,
ganin  kusan wata 2 ba lbrn ta..........

Dan Allah kuyi hkr yau bansamu yi dayawa ba sbd uzurin da ya gitta mun

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
            Nah
    💞AYSHAT💞
           110

Hnkln humairah yayi matukar tashi ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi,
tsawa lawal ya daka mata
"Ke ki saurarawa mutane kinaji ko, doctor fara aikin ka, duk wanan mgnr da yake yana yinta ne cikin turanci domin ga Alama mutumen baya jin Hausa,
Lktn yayi yan gwaje2 sannan yasake fada da turanci cewa,
"idan aka xubar da cikin zai iya zama risk ga rayuwar ta sai dai zai yi mata allura da magungunna dazasu taimaka wajjen zubar da shi batare da antaba ta ba"
Duk da ba hk Lawal yaso ba amma jin ance cikin zai zube yasa yaji sanyi,
Hk ya kwantar da ita tana kuka tana ihu aka mata allurar,
Tun lkcn bai fashin bata mgn har wuce ka'ida yake sbd cikin yayi sauri ya zube,

Wasa wasa cikin humaira yaki zubewa saima girma yk karawa yakira likitoci sunfi a kirga kusan duk d same tin suke gaya mishi,.......

Misalin karfe 3 na dare yayin da humairah ta tabbatar da Lawal da yaran shi basa gida ta mike  lkcn gari yayi tsit ba kajin motsin komai,
A hnkl take tafiya ta shiga cen ta fita nan bata taba sanin gdn katon gaske ba ne sai ranar  tayi Ku San 30 mnt snnan ta kai hanyar fita,
A hnkl ta murda kofar
Wani sanyi taji lkcn da kofar ta bude sai dai kash!
Tana budewa tayi 4eyes da Lawal
"Innalillahi wa'inna illaihirraji'un"
ta fada tare da sakin wata kara take ta durkushe wurin jikinta ya dauke mazari,
Ai ko Lawal yafara ball da ita yana zaginta har Suka kai bakin kofar dakinta
Cikin kakkausar murya yayi mgn
" humaira kina so ne ki rushe mun plan ko toh wlh Baki isa ba, kinyi yunkurin guduwa farko na kamaki kinyi na 2 hk to wlh dis tym ba zan kyale ki ba,
Zanyi miki illar da ko hnyr guduwa kika gani bazaki Gudu ba,"
Wani Abu yafitar ya watsa mata a ido
Wata kara ta yi lkcn da taji tamkar kwayar idanuwan ta ta tsiyaye sbd tsananin zafi lkc daya kuma taga dakin yayi duhu bata iya ganin komai,
Dariya yayi tare da cewa,
Wannan kadan daga cikin aikin Lawal,
Idan kin natsu kika haihu aka daura mana aure zansa agyara miki idanuwan ki,
Yafice dakin yanata kwsar dariya
Ita kuwa humaira tun tana kuka da hawaye ynz har sun daina zuba sbd tsananin bakin ciki..........
Wannan kenan!,

Fahad yazama tamkar mutum mutume ganin kusan 9 month babu lbrn humaira yasanya ya yanke shawarar barin kasar  Baki daya,
Iyayen shi basuyi yunkurin hanashi ba ganin irin halin da yake ciki,
Dady yace,
"Fahad nasanka mutum mai tsananin hkr da tawakkali fahad bana so ka sauya irin rayuwar da nasan ka da ita akan wata musiba da ta
same Ka"
Fahad ya ce,
"Insha allahu dady ba abunda zai sauya nagode kwarai da irin tarbiyar da kabani Allah ya kara girma"
Hk yayi bnkwana dasu ya bar kasar sai Egypt yakumbo da kursum sunyi kuka har sun godewa ubangiji hk su Momy take batar humaira ya dawo musu sabo dakyar su dady Suka lallashe su,......


House of novella📚📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
     💞AYSHA💞
          112
Humairah ta dafe kirji ta ce,
"Innalilahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga 3 ni humaira yazanyi da rayuwata ynx shikenan bani ba iyaye na har abada,
Ta fashe da wani irin matsanancin kuka,
Tausayin humairah ya kama Hauwa tadafa kafadar ta ta ce,
"Humairah ki kwantar da hnkln ki namiki alkawari insha allahu sai kinbar gdn nan humairah zan taimaka miki kibar gdn nan nima zan bar gidannan domin kuwa idan Lawal yakamani na tabbatar da sai dai wata Hauwa amma dai ba ni ba,
Bata san lkcn da ta rungume Hauwa ba sbd farin ciki,
Ta ce,
"Hauwa yaushe zamubar gdn nan,"
  Da kin haihu zamu bar gdn nan"
Ta ce,
"A"a Hauwa bana son na haihu gdn nan idan nahaihu gdn nan Lawal bazai barmun yaro na ba yace,
Da nahaihu zai dauke yaron don baxai bari nabashi nono ba,"
Hauwa ta ce,
"Humairah zaki iya Gudu da wannan cikin?,
Cikin ki fah yana cikin 10 month,"
Humairah tace,
"Zan iya hauwa muradi dai mubar gdn nan banajin ciyo komai a cikina sai dai nauyin da yake mun,"
Ta ce,
"To tunda hk ne gobe zamubar gdan nan idan su Lawal Suka fita operation matsala daya kuma wannan idanun naki,"
  "Ba matsala ba ce Hauwa tunda zaki zamo mun YARJAGORA",

Lolz zamuga gudun makauniy da tsohon ciki a sunkur min daji,
Hk kuwa zai yiwu?
Ku biyo ni anjima domin jin ynda zata kasance
Taku har kullun
Aisha faruk

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
               Nah
        💞AYSHAT💞
              111
Ynx cikin humairah ya tsufa har ya wuce wata tara, ga matsalar idanuwa,
Abun duniya duk ya dameta,
Sallamar Hauwa taji da ke kula da ita,
Hauwa ta ce,
"Humairah meyasa bakya jin mgn ne meyasa bazaki cirewa kanki wannan damuwar ba?
Kisani duk abunda yafaru da bawa mukaddari ne nima nan daki ka ganni kusan abunda yafaru dake nima shi yafaru dani,"
Humaira ta goge kwallar da ta zubo mata ta ce,
"Dole indamu Hauwa kiduba kiga cikina kusan 10 mnth ba alamar haihuwa,
Ki duba idanuwa na ki gani hauwa Lawal ya maidani makauniyar karfi da yaji,
Ya rabani da masoyina ya rabani da dangina Hauwa nayi nadamar sanin Lawal a rayuwata,
Takarasa mgnr cikin matsanancin kuka,
Itama Hauwa kukan ta fashe da shi sannan ta ce ,
"Humairah na tausaya miki kuma na tausayawa kaina, humairah ina mai tabbata miki cewa matan da Lawal ya aikatawa hk sunfi a kirga,
Humairah zan gaya miki ko wane ne Lawal,

Lawal mutumen kasar nijar ne shi yakashe iyayen shi da kanshi sanadiyar rayuwar da yajefah kanshi ciki ta ta sanfarin  da miyagun makamai in takaice miki dai ynx Lawal ya shahara gurin sata da fashi da makami   Lawal Nada daurin gindi fiye da ynda kike tsammani kuma Lawal mutum ne mai shige shige gurin malamma idan ya bude idanuwa yaga maccen da yake so toh addu'a kadai zata rabashi da ita domin kuwa sai ya mallaketa ko ta halin kaka,
Nima nan da kika ganni Lawal ya kashemun mahaifi yarabani da dangina yakuma rabani da masoyi na
Humairah ranar da za a dauramun aure ranar Lawal ya dauko ni yakawo ni tun ina kuka har na gaji na daina ynx hk ina dai daga cikin manyan matayen Lawal da yake holewa dasu na zubar da ciki yafi sau 5,
humairah bana fatan HK ta hau kanki humairah,
Lawal ya aure macce tafi a kirga,
Amma ina tabbata miki ke kadai yake so yayi tsalkakakken aure da ke sbd irin kaunar da yk miki
Humairah wlh na tabbatar da da ace Lawal baya sonki da tune ya kashe ki ba ma kaman lkcn da ya fuskanci kinada ciki  domin shi a tunanin shi lkcn da ya dauko ki lkcn a ka kai ki,
Yakashe yaron shi daya wnda yasanya domin yasanya ido ga lalurar ki,
Humairah ta CE,
Kaman ya kenan"
Hauwa tayi murmushi ta ce,
Tun lkcn da akaba shi hkr akanki tun lkcn yasanya wani yarika lura da al'amuran ki daga baya yaron yarika yimishi karya har kikayi aure bai gaya mishi ba sai bayan kinyi 2 mnth sannan Lawal yasan kinyi aure shiyasa yadauko ki a lkcn ,"
Humairah ta nisa cikin damuwa ta ce,
"Ynx kenan ina Nijar ko ina nigeria?"
Hauwa tayi murmushi ta ce,
"Humairah Baki nijer kuma Baki Nigeria"
Cikin tashin hnkl ta ce,
"Ina wace kasa,"
Hauwa ta ce,
"Kina Egypt "..

Chargy na yakare kuyi hkr

House of novella📚📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
    💞AYSHAT💞
            112
Misalin karfe 10 na dare humairah na kwance ita kadai tasan abunda take ji Lawal ya shigo dakin cikin shirin shi nafita,
yadube ta a wulalance ya ce,
"Wannan cikin fah naki ya wuce watan shi na haihuwa so ki shirya gobe za ayi miki aiki acire yaron,
Kuma kisa aranki
cewa  yaron matacce ne,
Bayan ancire yaron da 2 wks za a daura mana aure da ke kizama mallakina,
Idan na malakke ki zan sa a gyara miki idanuwan ki domun nasan bazaki taba guduwa da aure na akan ki ba,
Ya duka ya Dan shafe fuskar ta tare da kissing dinta a forehead yayi Murmushi ya  lumshe idanuwan shi,
shikadai yasan abunda yake ji game da yarinyar
Ita kuma humaira wasu hawaye ne Suka kwaranyo mata masu zafi,
"Ta Allah ba taka ba Lawal insha allahu Allah ba zai barka ba" ta fada tare da fashewa da kuka,
Ya tabe baki tare da mikewa yana duban agogon hannun shi,
Ya ce,
"Kada kidamu everything will be olright nasan sooner or letter za kidawo as humairar da na sanki a da I wil teach u how to luv me a gain,
na tafi sai nadawo"
Ya juya ya tafi abinshi yabarta nan tana kuka,
Hauwa ta shigo tana tmbyr ta me yafaru,?
takwashe duk abunda Lawal ya gayamata ta fadawa Hauwa,
Hauwa tayi ajiyar zuciya ta ce ,
"Kada ki damu humairah insha allahu yau zamubar gdan nan awa 2 masu
zuwa"
Batasan lkcn da ta rungume Hauwa ba tana murna,

Misalin 12 na daren ranar Hauwa ta kama hannun  humairah a hnkl take janye da
ita,
wata barauniyar hnya ta bi da ke cikin gdan sunyi 30 mnt suna cikin gdn kafin su
fita,
lkcn da Suka fita gdn wani sanyi ne yaratsa zuciyar humairah,
Lkc daya Suka fara ketar daji Gudu Gudu sauri sauri iya gajiya humairah ta gaji matuka amma bazata iya tsayawa ta huta ba ganin take idan ta tsaya kaman za a iya kamasu
Sunci 2 klometers amma ba alamar motsin mutane kukan tsuntsaye kawai kakeji da wasu halittu na ubangiji cen Suka fara jiyo kukan motoci innalillahi wa'inna ilahirraji'un Hauwa ta fada tare da kiran sun dawo wlh,
Lkc daya fitillun motocin Suka haska su,.............

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
             Nah
     💞AYSHAT💞
              113
Lkc daya Hauwa ta fizge hannu humaira Suka sake kutsawa ckin jejin da
gudu,
Ganin hnyar da sukabi ba ynda za ayi mota tabi yasanya su Lawal suka ajiye mutocin su suka bi bayan su da gudu,
Gudu suke tmkr ransu zai fita bama kamar humairah da tafara sadaukarwa ganin bazasu cimmusu ba yasanya suka fara harbin bindiga kafin kace  me Hauwa ta zube kasa lkcn da aka harbeta cikin shahsheka ta ce,
"Humairah tawa ta kare ki mike kici gb da Gudu  zan bari sai sunyi dab inbi cen inraba musu hnkl ynda bazasu iya cimmiki ba Allah yana tare da ke humairah jeki "
A wahalce humairah  ta sake rankayawa ckn jejin da Gudu,
(Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un makauniya da tsohun ciki a cikin dokar  daji batare da YAR JAGORA ba.
ni kaina marubuciyar kuka nake ganin irin hln da humairah ta ke
ciki )

Tun tana Gudu tana kuka tana fadin sunan Allah har takai ga ta ma kasa mgn Baki daya  karfin ta
yakare ,
Lkcn da takawo kan wani godabe yayi dai dai da faduwarta qasa
Ta  sanadiyar wani birki da aka ja,
Wasu mutane 2 ne macce da namiji  suka fito a rude.
Suka ciccebeta suka sa ta a mota  ba alamar nunfashi a tattare da ita...!
Da Gudu suka  ja motar sai asibiti domin ceto rayuwar ta,

A uzurce likitan ya fito yana cewa namijin cikin harshen turanci domin ga alama yasan shi,
"  Aliyu me yasa kabar wannan yarinyar har takai wannan condition din kamar ba docter ba?
Yaro har ya fara rubewa a cikin ta,"
Aliyu ya dube Matar shi da tunda Suka shigo take kuka ganin hlin da humairah ta ke ciki
Ya ce,
"Kiyi hkr Zainab zamu taimake ta insha Allah"
Ya dube doctor
ya ce,
"Kaje kabata duk irin taimakon da take  ne ma plz "............

Dan Allah kuyi hkr nadaina typing da yawa sbd wani uzuri da ya tare gaba na,

Nagode kwarai masoyana Allah yabar zumunci......

House of novella📚📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
          Nah
    💞AYSHAT💞
            114
An samu nasarar cero da Yara biyu a ckn humaira mace da namiji sai dai maccen tariga ta mutu tun a cikin ciki,
namijin ne kawai ya rayu,
A Lkcn da humairah ta dawo hayyacin ta
Kuka ta rika yi tare da godiyar Allah da Allah ya kubutar da ita hannun Lawal ynx matsala daya batasan ko hannun wa zata fada ba.
Aliyu yashigo dakin yayi tsaye bakin kofar dakin ya zubawa humaira idanuwa kamar yana nazarin wani abu  cen kuma yakarasa kusa da matarshi ya
zauna.
Zainab ta  dube mijinta a raunane ta
ce,
" tun dazun taki
tadaina kuka "
Aliyu ya ce, 
"Je ki karbo mata yaronta tabashi
abinci"
Ba tafi 2 mnt ba tadawo dauke da yaron idan kaga yaron ba zaka ce yasha wahala a cikin ciki  ba,
A hnkali ta
dungunawa humaira  yaron ta na
ce wa,
"Rike yaron ki boyar Allah kibashi nono yunwa yake ji"
Cikin murna da farin ciki humairah ta rike jaririn ta,
kankame shi tayi kaman wani zai kwace mata shi ta sake wani irin kuka mai ban tausayi,
Ta ce,
"Wannan shine ake kira da ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CHARA to ko ana muzuho ana shaho sai yayi Allah na godema da ka nunawa Lawal kai ne babban sarki kai ke rayawa kuma kake kashewa kai ke fitar da rayayye a cikin matacce ka kuma fitar da matacce a cikin rayayye,
lallai kai kakeda MULKI DA SARAUTA hkika
RANAR NADAMA tana nan zuwa ga
Lawal,
Zainab da Aliyu kallon humairah kawai suke Sunyi matukar tausaya mata duk da basu San matsalar ta ba amma NUNI YA ISHE MAIHANKALI sun tabbatar da humairah na cikin damuwa kuma sun kudiri niyar taimaka mata a matsayin ta na Yar uwar su musulma kuma Yar Nigeria
Sai da Suka bar ta  tadan samu  nutsuwa ta shayar da yaron ta nono sannan Aliyu yayi mgn ya ce,
"Boyar Allah muna so ki nutsu ki bamu Aron hnkln ki ki kuma karba mana dukkan Irin tmbayoyin da zamuyi miki domin Mu masu so su taimake ki ne,
ni sunana Aliyu tare da mata ta zainab mu nada yara 2 ameeer da ameeera mu yan asalin Nigeria ne aiki ne yakawo ni nan Egypt  amma insha  allahu nan da six month zamu koma
gd Nigeria muyi Hutu,
Ynx ina so ki fada muna sunan ki da kuma lbrn ki"
Humairah tayi shiru na Dan lkc sannan ta fara da cewa,
"Sunana Fateema kuma ni Yar Nigeria ce  a Kaduna"
A hnkl ta kwashe duk lbrn ta ta gaya
musu.
Sun tausayawa humairah matukar tausayawa Zainab ta rungume humairah tana ta kuka da kyar Aliyu ya lallashe su sukayi shiru

Ranar suna yaro yaci sunan Baban shi wato fahad kaman ynda humairah ta bukata a sanya mishi,

Satin ta 3 aka salllameta suka koma gd.

Humairah na zaune falo tare da Zainab suna fira  Aliyu ya shigo rungume da fahad ameer da ameerah suna bayan shi
Aliyu ya mikawa Zainab fahad   sannan ya zauna ya fuskance humairah ya ce,
"Fateemah ina so muyi  wata mgn da ke"
Humairah takarba da cewa,
"Ina jinka Yaya"
Ya ce
"Dama kan idanuwan ki ne
munyi mgn da Zainab kan cewa  tana so a gyara miki idanuwan ki Aidan zai yiwu,
Ynx abunda nake so dake shine kin tabbatar da abunda ya zuba miki gari ne ba ruwa
ba ?"
Humairah ta share hawayen da Suka zubu mata ta ce,
"Eh gari ne ynx hk ina jinshi a idanuwa nah"
Ya CE,
" toh ki kwantar da hnklin nayi mgn da wani aboki na Ahmad shima Dan Nigeria ne zai zo anjima ya duba ki,
Domin shi zaiyi miki aikin idanuwan
ki............

Ayshart farouq

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
            Nah
    💞AYSHAT💞
            116

Humairah tarasa bakin dazatayi musu gdy kawai ta fashe musu da kuka,
Zainab ta ce,
"Ba kuka zakiyi ba gdy zakiyiwa Allah "
"Hk ne kam "
Aliyu ya fada tare da mikewa,
itama Zainab mikewa tayi tabi mijin ta Suka shiga daki,

Bayan slh azahar humaira na toilet tana wanka fahad ya tashi yanata tsala kuka,
Aliyu ya shigo dakin yadauke shi tare da cewa
"Fateema idan kin kare ki same mu Palo ga docter Ahmad nan yazo,
Yafita tare da fahad da keta kuka,
Docter Ahmad na zaune hnkln shi nagun Aliyu da ke karasowa
Ya dube Aliyu yayi murmushi yace,
"Ina kuma kasamu yaro ko madam ta sake haihuwa ne?"
Aliyu ya ce,
"Dan kanwata ne da za ayiwa aiki"
Kukan da fahad keyi har cikin zuciyar shi yake jin shi ya mika hannu ya karbe shi daga hannun Aliyu tare da kuraw yaron idanuwa kaman ance yi shiru fahad yayi tsit ya ware idanuw yana kalllon Ahmad ,
Aliyu ya ce,
"Ikon Allah Ahmad kaga ynda yaron nan yayi shiru kana karbar shi,"
Ahmad yayi murmushi ya ce,
" may be ina kama da Baban shi"
Aliyu yayi dariya yace,
"Wan nan jariri ina ya isa sanin Baban shi Ai ko uwarshi don tana bashi nono ne,
Baban shi ma yarasu kafun a haife shi, sunan Baban shi aka sanya mishi,
Ahmad yace,
Allah sarki ya sunan shi,
Aliyu ya ce,
Sunan Ku daya amma fahad muke kiran shi kasan sunan dady na ne"

Ras gaban Ahmad ya fadi,
Ya kurawa fahad idanuwa yana nazarin wani Abu cen ya ce,
"Ina mamar shi?,"
Aliyu ya ce,
Wnka take ammma bari naje naga ko ta kare,

Ahmad ya tsurawa fahad ido shima yaron kalllo shi kawai yake yana dariya,
 
Lkcn da Aliyu ya dawo wayar Ahmad ta dauki ruri ya dauka
"Hello OK ganinan zuwa"
Yadube Aliyu ya CE,
Ina take,?,
Aliyu ya ce,
"Ta fara slh "
"Ba damuwa ynx ankira ni ana nemana urgently sai dai na sake dawowa"
Ya fada tare da mikewa yana mikawa aliyu fahad
Ya ce,
Takwarana sai nadawo yayiwa yaron kiss a goshi ya wuce Aliyu ya bishi suna tattaunawa kan issue din,
Ko can ma kafin ya shiga motar shi sai da ya sake kissing din yaron
Aliyu yayi dariya
ya ce,
Naga yaron yashiga ranka "
Ahmad ya ce,
"Sosai kuwa"
Sukayi dariya Baki daya Ahmad yayi gb abunshi .

Lkcn da humairah ta tunkaro palon sai ta tsinci kanta da faduwar gb
A hnkl ta karaso tana cewa
"Ya  na bata muku lkc ko?"
Aliyu yayi murmushi ya ce,
"Ba komai  docter ya ma wuce sbd ana Neman shi"
   Ita kanta humairah bataji dadin Abun ba ammma ta basar kawai ta karbi fahad ta wuce daki,

Lkcn da Ahmad ya koma gd gabaki daya yakasa sukuni fuskar fahad kawai yake gni
Take tunanin humairah yasake dawo mishi sabo
Ya dauki waya ya kira musty ringing daya musty ya dauka bayan sun gaisa
Yake ce mishi wai ya lbrn humairah
Musty ya ce,
"Fahad me yasa baxaka hkr da humaira ba iya bincike da mukayi ya tabbatar mana humairah bata Raye
Meyasa bazaka hkr ba?,
ya ce,
"Musty bazaka gane ba ne ni rayuwata har ynx bata aminta humairah ta mutu ba kwanakkin nan. Ina yawaita mafalkin ta  ni dai zan dawo kwanan nan na ci gb da Neman ta da kaina,"
Musty yayi murmushi ya ce,
"Sai kazo"
Domin yariga yasan halin fahad ba yaddda zaiyi da humairah ta mutu ba ammma kuma dole ya hkr tunda HK Allah ya kaddara...
Hk sukayi slm batare da Ahmad ya same karfin guiwa ba...
Ranar kuka yayini yi tmkar wani karamin yaro,.

Bayan kwana biyu Aliyu da Zainab suna Palo suna fira yayin da humaira ke daki tana ta sharar bacci Ahmad ya shigo gidan da sallamar shi aliyu ya karba tare da mika mishi hannu Suka gaisa Suka gaisa da Zainab ,
Aliyu ya dube Zainab ya ce,
"Kije kijawo humaira docter naso ayimata aikin dis wk
sbd yana so ya koma Nigeria "
Zainab ta karba tare da mikawa Ahmad fahad tana cewa,
Ga Dan gidan ka naji ko yaushe sai ka kira   ka tmby shi "
Ahmad ya karbe shi yana murmushi tare da dorashi a kan kafadar shi,
shi kadai yasan ynda yke ji game da yaron......

Qaraqaqa qaqa ga akuya ga kura,😂

Ku biyo ni Ku dai

Ayshart farouq

House of novella📚📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
          Nah
  💞AYSHAT💞
          107
Koda Zainab ta shiga dakin sai tasamu humaira nata sharar bacci harda su minshari ji tayi nazata iya tada ta ba kawai ta fito dakin,
Aliyu ya dubeta ya ce
"Ina take ne?"
Ta ce,
"Baccci takeyi sosai wlh harda minshari kuma ga alama  taji dadin baccin ko naje na tadata?"
Aliyu ya ce,
"Je ki tado ta mana"
Ahmad ya dakatar da ita da cewa,
" hb barta Dan Allah ba kyaun tado da mai nacci,
Ni wucewa ma zanyi abunda za ayi ynx Mu hadu asibiti cen tare da ita amma fah a kwai wani hnzari ba Gudu ba,
Aliyu ya dubeshi ya ce,
" kaman ya kenan"
Ahmad ya ce,
"Kaman ynda kuka ce powder aka watsa mata a idanuwa toh idan hk ne kafin ayi mata aiki sai an tabbatar powder ta hadu guri daya sannan za a iya cire ta don hk duk lkcn da tayi kuka powder zata watse, don hk ynx xuwa jibi muhadu a asibiti"
Aliyu yayi godiya yaraka Ahmad har bakin motar shi ya tada ya wuce.
Bai Dade da wucewa ba humairah ta tashi daga bacci,
Zainab ta ce,
"Kai fateema ko tsoron wannan doctor kike yi ne naga ko yaushe yazo kina bacci ko kina slh"
Humairah tayi murmushi ta ce,
" kila banida rabon ingan shi ne gashi kuwa ina son ganin shi ko don kaunar da yakewa fahad"
"Zaki ganshi jibi ko tunda shi zaiyi aikin ynx dai ki kiyaye abunda aka gaya miki Dan Allah wannan ZUBAR HAWYEN da kike ki hkr ki bari hr kiga kin same lfy "
Humairah tayi yake tare da kokarin maida hawayen da suke so su zubo ta ce,
"Insha Allah zanyi kokari naga nadaina"
Hk sukayit firarrakin su

Misalin karfe 10 na safiyar yau ne akaje da humairah asibiti kaman yadda Ahmad ya buqata

Batare da bata lkc ba aka mata wasu allurori da Ahmad ya  umurci wani docter ya mata kafin ya iso cikin kankanen lkc ta fita hayyacin ta, 
Lkcn da ya iso ne ya buqace a sanyata dakin da za ayi mata operation din
Cikin shirin shi na shiga tiyatar ya iso
Tun da docter Ahmad ya tunkari dakin da humairah take ciki yake jin wani irin faduwar gaba da bai taba samun kansa a ciki ba,
Da sallamar shi ya tura kofar dakin ya shiga,
Kwance ta ke kanta na kallon sillin idanuwan ta a bude wnda idan kagani zaka dauka ba bacci take ba,
A hnkl ya isa gurinta tare dakai Duban shi gare ta,
Inannalillahi wa'inna ilaihirraji'un ya fada lkcn da yayi Arba da fuskar da baxai taba mantawa da ita ba  har abada ya gani a razane ya fada HUMaIRa  murza idanuwan shi yayi tare da Dan Marin kanshi yaji ko mafalki yakeyi amma still ita yake gani lkc daya jikin shi ya dauke rawa hnkln shi yayi matukar tashi a hnkli ya riqa ja da baya yana fadin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tare da fashewa da kuka mai tsanani.....


Ayshart farouq

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭    
             Nah
      💞AYSHAT💞
              118
Kuka yake tare da yiwa Allah tasbihi yana kuma qara gode mishi ganin kukan bashida wani amfani yasan ya yaje yadoro alwala yafara jero
nafilfili,
yadade yana addu'ar Neman nasara a ckn aikin da zaiyiwa Matar shi,
Yana cikin hk ne wadan nurse 2 Suka shigo ga alama tare dasu za'ayi aikin su Kansu sunji tsoron ganin fahad ckn yanayin da yake ciki,
Batare da bata lkc ba aka soma yi mata aikin
Cikin iyawa ta ubangiji fahad yayiwa humairah aikin idanuwan ta
lkcn da yaqare ne yasanya cotton da bandage ya laulaye idanunn dasu sannan yayiwa nurse din umurni da su fita,
Konan ma saida sukayi mamaki domin sun san duk lkcn da yayi aiki da yaqare shi yake fara fita amma ynx gashi harda jawo kujera ya xauna,

Kujera yajawo yazauna gbn ta yakura mata idanuwa yana kallon ta a hnkl wasu kwallla masu zafi Suka shiga zubo mishi hannun ta Yakama yariqe  tare da Dora kanshi a kan cikinta,
Ganin nurse sunfita da 20 mnt Ahmad bai fito ba yasan ya Aliyu turo kofar dakin yashiga.
Tsaye yayi tare  da zubawa Ahmad ido yafi minti goma tsaye Ahmad bai Masanya shigo ba ,
A hnkl ya qarasa gurin shi ya dafa kafadar shi, fahad ya jiyo idanuwan shi jawur kaman wuta
Hnkl Aliyu ya tashi  ganin irin halin da fahad yake ciki,
Cikin mamaki ya ce,
" Ahmad me yafaru ne?,
Me yasaka cikin wannan Halin,?"
Fahad ya riqe shi tare da cewa,
Aliyu ina kasamu wannan yarinya,?
Meye dangantakar ka da ita,?"
Aliyu ya ce,
Kasan ta ne?,
Fahad ya ce,
"Answer me first pls"
Aliyu ya ce,
" I will tell u buh sai ka dai daita kan ka"
Fahad yafashe da kuka ya ce,
"How can I control mah salf matata tana ckin wannan halin,
Aliyu ka gayamun waya maida mun mata hk,?
A ina kasame ta?
Aliyu da tune jikin shi yayi sanyi cikin sanyi murya ya ce,
"Ahmad kai ne fahad din Fateemah?,"
"Ovcrse nine fahad din ta"
Aliyu yadaga hannuwa sama yanaw Allah godiya sannan daga bisani ya kwashe lbrn ynda Suka tsince  humairah ya gayawa faha.

Ayshart  farouq

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi nadama😭
           Nah
    💞AYSHAT💞
            119

Ya kwashe lbrn ynx Suka tsinci humairah ya gayawa fahad,
Fahad xaune yayi tare da dafe Kai domin har wani jujjuyawa yk Jin kanshi nayi,
Ita kuwa humairah har zuwa lkcn bata San inda kanta yake ba,
Aliyu ya dube fahad ya ce,
" yau ban san iyakar farin cikin da Fateemah zatayi ba idan taji fahad dinta yana raye kuma yana tare da ita,"
Fahad yayi shiru nadan lkc kadan sannan ya ce,
" bayanxu humairah zata Sani ba"
Aliiyu ya ce,
"Kaman ya kedan"
Fahad ya ce,
" idan har humairah ta san cewa ina raye toh aikin da akayi mata zai zama na banza sbd d moment tayi kuka toh aikin zai lalace"
Aliyu ya ce,
" lallai kuwa idan ta sani zatayi kukan farin
ciki ".
Fahad ya ce,
" Shiyasa nace kada a fada mata saboda nasan halin humairah da Saigon kuka "
Aliyu ya fitaya kira Zainab  suka shigo tare,
Fahad ya karbe fahad karami tare da kura mishi idanuwa
Yana cewa,
"Ashe dama kai  jini na ne shiyasa nake matukar kaunar ka "
ya qanqame yaron tare da skin ajiyar zuciya,
Zainab kallon shi kawai take cikin mamaki,
Aliyu ya kwashe komai ya gaya mata tayi matukar murna da jin dadi .

Ba fahad yabar dakin ba sai la'asar koshima dakyar Aliyu ya lallabashi sukaje masallaci

Koda suka dawa har humairah ta farfado Zainab tariqe hannun ta tana yi mata sannu,
Aliyu yaqara sa gurinta shima yana mata sannu,
A hnkl ta ke mgn
" Anty zainab da gske Yaya na yazo?,"
Ras gaban su ya fadi,
Aliyu ya ce,
"Wane yayan ki Kuma?,"
Ta ce,
"Yaya na fahad kaddai kuce mun baku gan shi ba"
Zainab ta ce,
"A'a humairah kar muyi hk da ke ina kika taba ganin matacce ya taso qila dai mafalki ki kayi"

"Ba mafalki nayi ba naji muryar shi kuma har ynx ina jin kamshin turare shi"

Aliyu ya ce,
"Haba Fatemah kina so ki sake sanya kanki cikin damuwa ne ina hnklin ki yake me yasa Bazakiyi tawakkali ba?,
Me yasa kike so kiyi ruin lyf dinki kinsan kuwa docter yace idan kikayi kuka aiki zai lalace,?"

A hnkl tafara gunjin kuka tana cewa,
" Ban so na farka daga baccin da nakeyi ba Ina ma zan sake kwantawa inyi irinshi da ban yi fatar falkawa ba har abada"
Zainab ta rungumeta tanata lallashin ta,

Fahad dake tsaye bakin kofar dakin kasa jumirin ganinta yayi cikin wannan hali dole ya fita yabar asibitin yana kuka,

Dakyar Aliyu da Zainab Suka ciyo kan humairah amma duk da hknan tayi hawayen sai dai ba suyi affecting aikin da aka mata ba,..

Tun lkcn da aka koma da humairah gd kullun fahad na gidan Aliyu sai dai idan humairah na falon baya cewa komai
Sai dai ko yaushe yana manne da yaron shi wani lkc ma idan humairah na bacci hk zai mannata jikin shi ya rungume ita kuwa humairah ta dauke abun matsayin mafalki
Sai dai ko yaushe tana so taga wannan doctor ahmad din da aka ce yana matukar kaunar fahad din ta,

Yau ne humairah ta cika wata 1 kuma yau ne za a cire bandage din da ke fuskar ta,
  Zainab ta same humairah zaune tayi tagumi ta ce,
" humairah miye Abun tagume yau fah ranar farin ciki ce,"
Humairah tayi murmushi ta ce,
"Wlh Anty hk kawai naji gaba na yana faduwa gani nake kaman idanuwa na bazasu bude ba"
Zainab ta ce,
Insha allahu idanuwan ki zasu bude qila wani Abun alkhairi ne zai same ki tashi muje ga doctor Ahmad cen yazo,
Humairah ta karba da "uhum"

Zainab ta jawota Suka doso palon da fahad da aliyu suke zaune,.......

Ayshart farouq c

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi Nadam😭
            Nah
     💞AYSHAT💞
             121
Har wuraren karfe 10pm fahad na gdn Aliyu
Aliyu ya dube shi ya ce,
Sabbenin mgnr zuwa gd fah ko nan zaka kwana?"
Fahad ya ce,
" idan kun bani matata tafiya zanyi amma idan kuka hanani toh fah kafata kafar ta"
Aliyu ya ce,
" lallai Ahmad Abun ka azimun ne toh ga matarka nan Allah raka raki gona kuma dadin Abun kowa ynada mata"
Duk aka sanya dariya
Zainab ta ce,
" toh Ai nagama kaman Fateemah bacci take ji bazaka bari zuwa gobe ba?,
Humairah ta zaro ido ta ce,
" kai Anty yaushe nagaya miki ni ko safe zan iya kaiwa a hk"
Fahad ya mike tare da daukar fahad qarami yana cewa,
Kara Ai muje ki hutu u need
to rest "
HK suka kama hny Suka wuce su Zainab na musu dariya,

Fahad zaune  kan gado ya jingina kan pillow yayin da humairah ke kwance kan cinyar shi ya lalubo waya ya kira no musty ringn daya aka dauka bayan sun gama gaisawa fahad ya ce,
" albishirin ka bro"
Musyt ya karba da goro
Fahad ya ce,
" nasamu wata wadda zan aura"
Humairah da ke cinyar shi bata San lkcn da ta mike ba tana kallon shi
Ya kashe mata ido
Yaci gb da cewa ,
Kamar su daya da humairah ta idan kaga ni zaka ce twins ne har da irin tsiwar humairah wlh bros babyn ta shiga raina"
Musty yaji dadi sosai ganin hnkln fahad ya kwanta har ya neme mata ya ce,
" Ashe kuwa yau har goron albishir sai yakumbo ta bani idan taji duk suka sanya dariya yasake cewa toh yaushe zaka dawo ynx tunda ka hkr da humairar fahad yayi murmushi ya ce,
" har abada bazan manta humaira ba kuma baxan taba son wata ba kamar ynda naso humaira,  humairah ita ce rayuwata "
Humairah da ke zaune tana mitsi mitsin ta kwace wayar tayi mgn a hnkl ta lumshe idanuwa sbd jin kalaman shi ,
Fahad ya ce,
"Insha allahu zan dawo nan da 3mnth,
Sukayi sallama ya ajiye wayar tare da jawo humairah jikin shi yana cewa so nake muyi surprising dinsu kaman ynda kikayi surprising dina ko ya kika ce,?"
Gyada mishi kai kawai tayi sbd ynda ya matseta a kirjin shi yashiga sunbatar ta ta ko ina,
nan fah wasa ta chanja,
lolz!
Ni dai bazan iya gani ba na kwashe inawa da nawa nayi gb amma na tabbatad da sunyi missing junan su a wannan rana.
Rayuwa kenan.

Su fahad sun zama tamkar yan uwa juna da su Aliyu ko yaushe suna tare alaqa mai karfi Suka kulla  har sun yanke shawara tare zasu koma gida Nigeria,

Ranar yau ne asabar da tayi dai dai da dawowar su humairah Nigeria sunyi shigar su ta alfarma yayin da humairah ta ke sanye da jallabiya baqa da mayafinta takuma rufe fuskar ta da nikaf da kaganta zaka dauka irin larabawan na ne batare da bata lkc ba suka isa airport  cen Suka taradda Aliyu da Zainab,
cikin yan minto ta kadan jirgin su ya tashi sai Nigeria,

Cen kuwa gd Nigeria su yakumbo ana ta shirye shiryen tarbon fahad da Amaryar shi su kursum da ke da Yar qaramar diyar ta mai suna humairh duk an halarta a airport saukar jirgin su fahad kawai ake jira,

  Cikin iyawa ta ubangiji jirgin su fahad ya sauka a international airport dake Kaduna.

House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi Nadama😭
             Nah
    💞 AYSHAT💞
             120

Tunda suka doso falon  gaban humaira ke dukan 3 3 sbd wani irin kamshin turaren fahad datake ji a hnkl Suka qarasa falon Zainab ta zaunar da ita tare da cewa docter Ahmad gata nan,

A hnkl fahad ya qaraso gbn humairah ya gurfana tare da tsura mata idnuwa na Dan wani lkc kadan
Hnkln humairah yayi matukar tashi jin kamshin turaren fahad dinta,
Ta qagu a kwance mata idanuwan ta taga wannan doctor Ahmad din da ke irin kamshin fahad dinta bata kai ga qare tunanin ta ba taji anfara warware bandage din,
Lkcn da aka warware bandage din idanuwan ta rufe cen qasan makoshin sa yayi mgn da cewa,
"Bude idanuwan ki "
Bata gasgan ta abund taji ba sai da ya sake cewa ,
"Idanuwan basa buduwa ne?,"
Da sauri humairah ta bude idanuwan ta tas akan fuskar fahad a hnkl ta sake maidasu ta rufe ta kuma sake budewa domin ta dauka ko har ynx idanuwan basu gyaru ba domin ganin abunda ko yaushe shi take gani,
Wasu hawaye masu zafi Suka shiga kwaranyowa a fuskar ta take ta dauke kanta da wani irin mari ta sake daga hannu da niyar qara marin kanta ko zata falka daga baccin da take,
Fahad yariqe hannun ta yana cewa,
"Haba humairah miye hk ? meyasa kike so ki qara jimun ciyo
ne?"
Subuhanallah!
wani kuka humairah tasaki mai tsuma zuciya tare da fadawa jikin fahad tana cewa,
"Yaya na Ashe ba mafalki nake yi ba dama inaji a jikina kana raye Yaya nah kaga ynda Lawal ya maida ni ya........
Bata qarasa mgnr ba ta sulale a kasa sumamma
Hnkln fahad ya matuqar tashi yarasa ko wane irin taimako zai bata  batare da yasan abunda yake ba ya jawo coke din da ke gaban shi yashiga zuba mata yana shafa mata a fuska yana kiran sunan ta
"humairah humairah"
A  hnkl  ta bude idanuwan ta tare da fashewa da kuka bakinta sai motsi ya ke da alama mgn take yi,
cikin kuka fahad  ya manna  ta a kirjin shi  ya rungume ta gam  kamar wani zai kwace mishi ita  yana shafa kanta tare  da cewa,
" Ya Isa humairah daina yin mgn riqa yin tasbihi"
Zainab da Aliyu da sukayi rigan gan gurin kawo ruwa  tsaye sukayi  ko wanen su kwalla ta cikawa idanuwa saboda tsanani tausayawa fahad da humaira nima kaina marubuciyar kwalla nake yi ganin irin halin da wadannan bayin Allah suke ciki,
Palon yayi tsit bakajin komai banda gunjin kukan humairah da fahad cen Aliyu yayi karfin halin zuwa kusa dasu ya dafa kafadar fahad yana cewa,
" hb Ahmad bai dace ka riqa biyewa Fateemah kuna irin wannan kukan ba kuka Ai bai kamace Ku ba godiya ya kamata kuyiwa Allah "
Hk itama Zainab tazo  ta ce,
" Gsky ne kam gashi tun dazu fahad  keta tsala kuka ko Neman abunci yake ko kuma yana taya iyayen shi kuka ne allahu wa'alamu "
Sai lkcn ma Suka tuna da wani fahad qarami,
Fahad yayi murmushi tare da miqa hannu ya karbi yaron ya dube humairah ya ce,
" Ashe zanga jinina humairah ban yi tunani cikin ki zai zauna ba kwata kwata ban kawo wa raina zaki haife cikin ba,
Humairah tayi murmushi tare da karbar yaron ta ce,
" Yayanah nima Banyi tunanin zanga yaron ba,  ta qarashe mgnr tare da shafe kwalla
Ta ce,
Allah nagodema idanuwana sun rufe tare da babban maqiyi na yayin da Suka bude da babban masoyi nah lallai wannan ita  CE kYUTA ta ubangiji"
HK sukayi ta lbrn  yaushe gamo har maraice,
Fahad da humaira ko sunanan manne da junan su....




House of novella📚📚
[5/10, 3:43 PM] KAURA: Nayi Nadama😭
            Nah
      💞AYSHAT💞
              122
Lkcn da jirgin ya sauka wani sanyi humairah taji a hnkl ta dube fahad ta ce,
" ya faha ji nake tamkar mafalki nake "
Yayi murmushi tare da kama hannun ta ya riqe
" ba mafalki kike ba kanwata hk din ne yau insha allahu zakiga Abba da Momy "
HK suka fito ckn jirgin Aliyu na riqe da Ameer fahad riqe da hannun humairah da Ameerah yayin da zainab ta ke rungume da fahad karami,
Ckn murna musty ya tare Dan uwan shi kursum kuwa da gudu tazo tarungume humairah tana fadin ko ban fada ba wannan ita ce amaryar Mu,
Wani sanyi humairah taji lkcn da taga iyayenta da yan uwan ta Allah sarki ta fada a ckn ranta,
Fahad ya nuna Aliyu da Zainab ya ce,
Dady wadannan sune dangin mata ta sun biyo ni ne domun suga muhallina da iyali na dady ya ce,
" masha Allah sannun Ku da zuwa"
suka karba da
"yauwa"
Musty ya ce,
" shine amaryar ta rufe fuska don kar mugan ta"
Fahad yayi murmushi ya ce,
" za kuganta amma sai yakumboo tafara ganin ta"
Duk aka sanya dariya
Yau ma kaman ynda aka saba duk part din yakumbo aka halarta kowa yazo domin ganin amaryar fahad,
Yakumbo ta washe Baki tana fadin toh
"a bude mana amaryar mugani domun kuwa na qagu Inga balarabiyar idan ta fini kyau"
A hnkl fahad ya durqusa gbn humairah ya sanya hannu ya yaye nikab din da ke fuskar ta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
Kowa yayi tsit dakin da alama sunyi mutuwar zaune,
Yakumbo ta fashe da kuka tana fadin nashiga uku ni fatsima aljannu sun shige ne fahad Humairah na ke gani,
Ita ma kursum ckn kuka ta ke fadin wlh yakumbo nima sun shafe ni domin nima humairah nake gani
Momy kuwa fadowa tayi daga kan kujera nunfashin ta na neman daukewa,
Da Gudu humairah ta isa gurin momyn ta ta rungume ta tana kuka tana fadin Momy kinga ikon Allah ko Momy humairarn ki ta dawo bazan sake barin ki ba har abada Momy kiyafe ni nasanya ki ckn damuwa
Mom..........."
Momy ta katse ta da
"Fadin ya isa humairah ya isa hk yi shiru daina kuka kinji"
Hnkln kowa ya koma kan fahad domin jin ynda al'amari ya faru,
Fahad ya zayyane musu duk abunda yafaru
Dakin ba Wanda baiyi kuka ba sbd tausayin humairah da kyar dady ya lallashe su ba kamar yakumbo mai aljannu lolx.
Sai da sukaci abinci suka Dan huta sannan aka gaggaisa su dady sunyiwa su Aliyu gdiya maiyawa da goma ta arziqi sannan sukayi bankwana dasu suka wuce kano,
Wannan kenan.

Tun lkcn da Suka dawo yakumbo ta hana su koma gdn su a cewar ta wai Lawal zai sake zuwa gdn da kyar dai aka shawo kanta ta hkr Suka koma gdn su.

Rayuwar su humairah gwanin ban sha'awa
Idan kagansu bazaka taba cewa sun taba shiga wani tashin hnkl ba ga junior yayi bulbul abinshi fahad yana tsananin kaunar Matar shi da dan shi baya kaunar abunda ya taba su.

Fahad zaune yana kallon news yayin da humairah ke gefen shi da Dan yaron ckinta Dan wata 3 tana ta shagwaba cen hnklnta ya karkata da news din da ake lkcn da aka yankewa wasu mutane 3 hukuncin kisa an umurce su da su fadi last word ga wadan da suke so suji humairah mikewa tayi tsayi jin mgnr da mutumin keyi lallai da ba domin muryar shi ba da ba ynda za 'ayi ta gane shi
Sbd qafar shi daya ta cire yayin da idon shi daya ya tsiyaye har wata qasunba yayi wadda idan ka Ganshi bazaka taba rabashi da mahaukaci ba cikin kuka da nuna tsantsar NADAMA ya ke mgn,
" ina rukon Allah yasa wannan sakon nawa zai Isa kunne wannan boyar Allah humaira hkika humairah kinyi gskiyar RANAR NADAMA tazo tabbas NAYI NADAMAR abunda na aikata miki domin ni nasan alhakin ki ne ya kamani humairah Dan girman Allah ki yafe min ko zan samu dan wani sasauci,
ina fatar wannan sakon zai Isa gare ki da yan uwan ki kuma ki Sani cewa tsananin kaunar ki da tsantsar nadamar abunda na aikata miki yafi mun radadi akan halin da nake ciki ynx" ya qarashe mgnr tare da fashewa da wani irin kuka,
Itama humairah kuka ta saki tare da fadawa jkn fahad tana fadin
" Yayana kaga qarshen wannan azzalumin ko dama na gaya maka qrshen shi bazaiyi kyau ba Allah nagodema da ka nunamin ranar nadamar Lawal,
Yaya nah nayi nadamar sanin shi a rayuwa ta,"
Fahad ya rungume ta tsam a qirjin shi tare da lallashin ta ganin batada niyar daina kukan ne yasan ya ya rada mata wata mgn a kunne ai kuwa take ta miqe ta ruga daki tana dariya shima biyarta yayi yana dariya tare da banko kofar dakin.
Wata rayuwa sukayi mai ban sha'awa da kauanar juna.

ALHAMDULILLAH

Nan nakawo karshen wannan littafi NAYI NADMA sai mun hadu insha allahu  a littafina nagaba KYUTAR ALLAH
 
Godiya da jinjina ga
Khadijah Ahmad (khady) nagode kwarai da kulawar ki Allah yabar zumunci.

Godiya a gareku kuma
Ummienice and Zainab Nasir Danmaranyo domin kunfi kowa kaunar littafin  😉😂

Ban manta Ku ba members of
House of novella
Excellent writers
Mata rahama
Housa novels
Best Hausa novels
Hasken mata
Da duk masoyan wannan littafin nagode kwarai da kulawar Ku Allah yabar zumunci
Ameen.

Ayshart farouq
For comment and correction 08100376392

House of novella